Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai

عَنْ سَلْمَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ رَبَّكُمْ حَيِيٌّ كَرِيمٌ، يَسْتَحْيِي مِنْ عَبْدِهِ إِذَا رَفَعَ يَدَيْهِ إِلَيْهِ أَنْ يَرُدَّهُمَا صِفْرًا».
Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa akan ɗaga hannaye a lokacin addu'a, kuma ya bada labarin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa (Mai kunya ne) Mai yawan kunya ne, ba Ya barin kyauta, Yana yi wa bawa abinda yake faranta masa, kuma Yana barin abinda yake cutar da shi, (Mai yawan kyauta ne) Yana bayarwa ba tare da tambaya ba to yaya kuma bayan tambaya! Yana jin kunyar bawanSa mumini ya dawo da hannayensa bayan ɗagasu dan yin addu'a babu komai suna babu komai cikinsu a taɓe daga amsawa.

Fa’idoji
  1. A duk lokacin da mutum ya bayyanar da buƙatuwa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da bauta, ya kasance ya fi ƙauna gare shi kuma ya fi kusanci ga amsawa.
  2. Kwaɗaitarwa a kan addu'a, da son ɗaga hannaye a cikinta, kuma cewa shi yana daga sabubban amsawa.
  3. Bayanin yalwar karamcin Allah da rahamarSa ga bayinSa.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 609) (1488). سنن الترمذي (5/ 521) (3556). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 552). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 423). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 483).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBAN ADDU'A

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com