عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: كان رسولُ الله صلى الله عليه وسلم إذا عَطَس وضَعَ يَدَه -أو ثوبَهُ- على فيهِ، وخَفَضَ -أو غضَّ- بها صوتَهُ.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi.
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi atishawa:
Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa.
Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.
Fa’idoji
- Bayanin shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a atishawa, da kuma koyi da shi a hakan.
- An so (mai atishawa ya) ɗora tufafi ko hankici da makancinsa akan bakinsa da hancinsa idan zai yi atishawa, domin kada wani abinda zai cutar da abokin zamansa ya fito daga gare shi.
- Kanƙar da murya a atishawa abin so ne, hakan yana daga cikar ladabi, da kuma kyawawan ɗabi'u.
Madogara
سنن أبي داود (7/ 375) (5029).
سنن الترمذي (4/ 461) (2745).
مسند أحمد (15/ 412) 9662).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 440).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص528).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 149).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 678).
كنوز رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين (11/ 432).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إذا عَطَسَ أَحَدُكُم فَلْيَقُل: الحَمْدُ للهِ، وَلْيَقُلْ لَهُ أَخُوهُ أو صاحبُهُ: يَرْحَمُكَ الله، فإذا قال له: يرحمك الله، فَلْيَقُلْ: يَهْدِيكُم الله ويُصْلِحُ بَالَكُم».
Daga Abu Hurairah, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Idan dayanku ya yi atishawa, to ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, kuma dan’uwansa ya ce masa, Allah ya yi muku rahama. Idan ya ce masa: Allah ya yi maka albarka, Bari ya ce: Allah yayi muku jagora kuma ya yi sulhuIdan kun dafa kayan yaji, sai ku kara ruwa, kuma ku yi wa makwabta alkawari da ku.
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Hadisin ya nuna cewa idan Musulmi yayi atishawa, to ya yabi Allah Madaukaki. Saboda atishawa yana da alkhairi da fa'ida ga atishawar ta hanyar fitar da hayakin da ke cunkushe a cikin kwakwalwarsa cewa, idan sun ci gaba da kasancewa a cikinsa, zai haifar masa da cutuka masu wahala, don haka an wajabta masa yabon Allah Maɗaukaki saboda wannan ni'imar, to, wanda ya ji shi dole ne ya ji warinsa, ta hanyar ce masa: Allah ya albarkace ka, kuma ya amsa Mai atishawa ya ce: Allah Ya yi muku jagora kuma Ya yi sulhu da ku, don haka atishawa ta samu fa’ida ga mai atishawa da wanda ya saurara, kuma wannan yana daga cikin fa’idojin da addinin nan yake da shi a kan mutane.
Madogara
- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
- شرح رياض الصالحين، للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي - الطبعة الأولى، 1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة - بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- تطريز رياض الصالحين، تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة، الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلَامِ، وَعِيَادَةُ الْمَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama.
Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa.
Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta.
Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan.
Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.
Fa’idoji
- Girman musulunci a karfafa hakkoki tsakanin musulmai da karfafa 'yan uwantaka da soyayya a tsakaninsu.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 71) (1240).
صحيح مسلم (4/ 1704) (2162).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 512).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 327).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 253).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 591).
بهجة قلوب الأبرار، لابن سعدي (ص81).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا تَثَاءَبَ أَحَدُكُمْ فَلْيُمْسِكْ بِيَدِهِ عَلَى فِيهِ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَدْخُلُ».
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadakar da wanda zai yi hamma cewa buɗe bakinsa saboda kasala ce ko cika ko wanin haka; cewa ya ɗora hannunsa akan bakinsa sai ya rufeshi da shi; hakan domin Shaiɗan yana shiga cikinsa idan ya barshi a buɗe, to ɗora hannu yana zama mai hana shigarsa.
Fa’idoji
- Idan mutum yana son yin hamma to ya wajaba a kansa ya rufe (bakinsa) daidai iko, cewa ya riƙe bakinsa, sai ya barshi a rufe ta inda ba zai buɗe ba, idan ba zai iya barin bakinsa a rufe ba to ya ɗora hannunsa akan bakinsa, sai ya rufe bakinsa da hannunsa.
- Lazimtar ladubban Musulunci a dukkan halaye; domin cewa sune alamomi na cika da kuma ɗabi'u.
- Kiyayewa daga dukkan mashigar Shaiɗan ga mutum.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2293) (2995).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 151).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 436).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص529).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 679).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ سِتٌّ» قِيلَ: مَا هُنَّ يَا رَسُولَ اللهِ؟، قَالَ: «إِذَا لَقِيتَهُ فَسَلِّمْ عَلَيْهِ، وَإِذَا دَعَاكَ فَأَجِبْهُ، وَإِذَا اسْتَنْصَحَكَ فَانْصَحْ لَهُ، وَإِذَا عَطَسَ فَحَمِدَ اللهَ فَسَمِّتْهُ، وَإِذَا مَرِضَ فَعُدْهُ وَإِذَا مَاتَ فَاتَّبِعْهُ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa)".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi ɗabi'u shida ne: Na farko: Idan ya haɗu da shi ya yi masa sallama da faɗin: Assalamu alaikum, Wato: Aminci ya tabbata agare ku, shi kuma ya dawo da sallama da faɗinsa: Waalaikumus Salam, Wato: Aminci ya tabbata agare ku. Na biyu: Amsa gayyatarsa idan ya gayyace shi dan walima da makamancinta. Na uku: Yi masa nasiha idan ya nemeta, kada ka yi masa yaudara ko ka yi masa algus. Na huɗu: Idan ya yi atishawa sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, to ka gaishe shi da faɗin: (Yarhamukallah) Allah Ya yi maka rahama, shi kuma ya amsa yana mai cewa: Allah Ya shiryar da ku kuma ya gyara zuciyarku. Na biyar: Ya gaishe shi kuma ya ziyarceshi idan ya yi rashin lafiya. Na shida: Ya yi masa sallah idan ya rasu, kuma ya bi jana'izarsa har sai an binne shi.
Fa’idoji
- Shaukani ya ce: Abin nufi da faɗinsa: (Haƙƙin musulmi) cewa barinsa bai kamata ba, kuma aikatashi yana zama kodai wajibi ko mandubi mai ƙarfi mai kama da wajibin da barinsa ba ya kamata.
- Maida sallama farilla ce ta aini idan wanda aka yi wa sallamar shi kaɗai ne, kuma mutum ɗaya ya isarwa jama'a, amma fara sallama to asali a cikinsa shi ne sunnah.
- Ziyarar mara lafiya yana daga haƙƙoƙinsa akan 'yan uwansa musulmai; domin cewa ziyara tana shigar da farin ciki da kewa a zuciyarsa, kuma ita farilla ce ta kifaya.
- Wajabcin amsa gayyata muddin dai babu wani zunubi a cikinta; idan ta kasance zuwa walimar angwanci ce to jumhur sun tafi akan wajabcin amsata sai dai inda wani uzuri na shari'a, amma idan ta kasance ba walimar angwanci ba ce to jumhur sun tafi a kan cewa sunnah ce.
- Gaishe da mai atishawa wajibi ne akan wanda ya ji godiyar (Allah) ga wanda ya yi atishawa ɗin.
- Cikar shari'a da kwaɗayinta a cikin ƙarfafa igiyar zamantakewa da imani da alaƙar soyayya tsakanin ɗaiɗaiku.
- (Fasammithu) a cikin wasu bugun: (Fashammithu), da Sin mara 'ya'ya da kuma Shin mai 'ya'ya: Addu'a da alheri da kuma albarka, al-Tashmit an ce a cikin ma'anarta: Allah Ya nisantar da kai daga dariyar ƙeta, kuma Ya nisantar da kai abinda maƙiyinka zai yi maka dariyar ƙeta da shi, Tasmit kuma ma'anarsa: Allah Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1705) (2162).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 7).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (3/ 128).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 327).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com