Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلَامِ، وَعِيَادَةُ الْمَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza, da amsa gayyata, da gaida mai atishawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama. Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa. Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta. Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan. Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.

Fa’idoji
  1. Girman musulunci a karfafa hakkoki tsakanin musulmai da karfafa 'yan uwantaka da soyayya a tsakaninsu.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 71) (1240). صحيح مسلم (4/ 1704) (2162). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 512). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 327). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 253). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 591). بهجة قلوب الأبرار، لابن سعدي (ص81).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN SALLAMA DA NEMAN IZINI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com