Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

LADUBBAN KARATUN ALƘUR'ANI MAI GIRMA

Hadisai 3

Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّمَا مَثَلُ صَاحِبِ القُرْآنِ كَمَثَلِ صَاحِبِ الإِبِلِ المُعَقَّلَةِ، إِنْ عَاهَدَ عَلَيْهَا أَمْسَكَهَا، وَإِنْ أَطْلَقَهَا ذَهَبَتْ».
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa kwatankwacin ma’abocin Alƙur'ani kamar kwatankwacin ma'abocin dabaibayayyun raƙuma ne, idan ya kula da su sai ya riƙesu, idan kuma ya sakesu sai su tafi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta wanda ya karanta Alƙur'ani kuma ya saba da karanta shi - daidai ne yana dubawa daga Mushafi ne ko da ka yake yi - da ma'abocin dabaibayayyun raƙuma da igiyar da ake ɗaure gwiwowin raƙuma da su, idan ya kula sai ya ci gaba da riƙesu, idan kuma ya saki ɗaurinsu sai su tafi su suɓuce, idan ma'abocin Alƙur'ani ya tsaya sai ya karanta shi zai tuna shi, idan kuma bai tsayu da shi ba to zai manta shi; lazimta ba zata gushe tana samammiya ba sai hadda itama ta zama tana nan.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan lazimtara Alƙur'ani da kuma karanta shi, da kiyayewa daga bijirar da shi ga mantuwa.
  2. Dawwama akan karatun Alƙur'ani harshensa zai horu da shi kuma karanta shi zai yi masa sauƙi, idan ya ƙaurace masa sai karatun ya yi masa nauyi kuma ya wahalar da shi.
  3. Alƙali ya ce: Ma'anar "Ma'abocin Alƙur'ani" wato: Wanda ya saba da shi, al-Musahaba: Sabo da abu, daga haka ne: Wane abokin wane ne, da 'yan aljanna da kuma 'yan wuta.
  4. Daga cikin hanyoyin Da'awah akwai buga misalai.
  5. Ibnu Hajar ya ce: An keɓanci raƙuma da ambato; domin cewa sune mafi tsananin gujewa cikin dabbobin gida, kuma kama su bayan sun gudu akwai wahala.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 193) (5031). صحيح مسلم (1/ 543) (789). شرح صحيح مسلم، للنووي (6/ 77). فيض القدير شرح الجامع الصغير، لعبدالرؤوف المناوي (3/ 3). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (13/ 12).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne

عن عُقبة بن عامر الجُهني رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم: «الجاهِرُ بالقرآن كالجاهِرِ بالصَّدَقَةِ، والمُسِرُّ بالقرآن كالمُسِرِّ بالصَّدَقَة».
Daga Uqubah Dan Amir Al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai bayyanar da karatun Alkur’ani kamar mai bayyanar da bayar da sadaka ne, mai boye karatun Alkur’ani kamar mai boye bayar da sadaka ne.

Fa’idoji
  1. Boye karatun Alkur’ani shi ya fi , kamar yadda boye sadaka shi yafi, dan abinda yake cikinsa na tsarkake niyya da nisanta daga riya da jiji da kai, sai dai idan bukata da maslaha sun bukaci bayyanarwar kamar koyar da Alkur’ani .
Madogara

سنن أبي داود (2/ 494) (1333)، سنن الترمذي (5/ 40) (2919)، سنن النسائي (5/ 80) (2561)، الكاشف عن حقائق السُّنن (5/1688)، شرح أبي داود للعيني (5/238)، تحفة الأحوذي (8/ 191)، التنوير في شرح الجامع الصغير (5/286).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: اعْتَكَفَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي المَسْجِدِ، فَسَمِعَهُمْ يَجْهَرُونَ بِالقِرَاءَةِ، فَكَشَفَ السِّتْرَ، فَقَالَ: «أَلَا إِنَّ كُلَّكُمْ مُنَاجٍ رَبَّهُ، فَلَا يُؤْذِيَنَّ بَعْضُكُمْ بَعْضًا، وَلَا يَرْفَعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَعْضٍ فِي القِرَاءَةِ»، أَوْ قَالَ: «فِي الصَّلَاةِ».
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi i'itikafi a cikin Masallaci, sai ya ji su suna bayyanar da karatu, sai ya yaye mayafi, sai ya ce: «Ku saurara, lallai kowannenku yana ganawa ne da Ubangijinsa, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kada kuma sashinku ya ɗaga muryarsa ga sashi a cikin karatu», ko cewa ya yi: «A cikin sallah».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune yana i'itikafi a cikin wata ƙubba a cikin Masallacinsa dan neman kusanci ga Allah, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sahabbansa suna bayyanar da karatun Alƙur'ani a bayyane mai tsanani sashinsu yana cutar da sashi. Sai ya yaye mayafi daga ƙubbar, ya zargi wanda ya aikata haka ya zarge shi, sai ya ce: Dukkaninku kuna ganawa ne da Ubangijinku ta hanyar karatun Alƙur'ani, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kuma kada sashinku ya ɗaga muryarsa akan sashi a cikin karatu, ko a cikin sallah.

Fa’idoji
  1. Hani akan ɗaga murya a karatun Alƙur'ani, idan ya kasance a akwai cutarwa ga wani a cikinsa.
  2. Koyarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa ladubann karartun Alƙur'ani.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 494) (1332). شرح سنن أبي داود للعباد (162/ 18). شرح أبي داود للعيني (5/238). شرح سنن ابي داود لابن رسلان (6/515). ذخيرة العقبى (11/669).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com