Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune yana i'itikafi a cikin wata ƙubba a cikin Masallacinsa dan neman kusanci ga Allah, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji sahabbansa suna bayyanar da karatun Alƙur'ani a bayyane mai tsanani sashinsu yana cutar da sashi. Sai ya yaye mayafi daga ƙubbar, ya zargi wanda ya aikata haka ya zarge shi, sai ya ce: Dukkaninku kuna ganawa ne da Ubangijinku ta hanyar karatun Alƙur'ani, dan haka kada sashinku ya cutar da sashi, kuma kada sashinku ya ɗaga muryarsa akan sashi a cikin karatu, ko a cikin sallah.
- Hani akan ɗaga murya a karatun Alƙur'ani, idan ya kasance a akwai cutarwa ga wani a cikinsa.
- Koyarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa ladubann karartun Alƙur'ani.
سنن أبي داود (2/ 494) (1332). شرح سنن أبي داود للعباد (162/ 18). شرح أبي داود للعيني (5/238). شرح سنن ابي داود لابن رسلان (6/515). ذخيرة العقبى (11/669).