عن أبي واقد الحارث بن عوف رضي الله عنه أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم بينما هو جالس في المسجد، والناس معه، إذ أقبل ثلاثَةُ نَفَرٍ، فأقبل اثنان إلى رسول الله، صلى الله عليه وسلم وذهب واحد، فوقفا على رسول الله صلى الله عليه وسلم ، فأما أحدهما فرأى فُرْجَةً في الْحَلْقَةِ فجلس فيها، وأما الآخر فجلس خلفهم، وأما الثالث فأدْبَر ذاهبٍا، فلما فرغ رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ألا أُخْبِرُكُم عن النَّفَرِ الثلاثة: أما أحدهم فأَوَى إلى الله فآوَاهُ الله إليه، وأما الآخر فاسْتَحْيا فاسْتَحْيَا الله منه، وأما الآخر، فأعْرَضَ، فأعرضَ اللهُ عنه».
Daga Abu Waqid al-Harith bin Auf - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake zaune a cikin masallaci, kuma mutane suna tare da shi, kamar yadda mutane uku suka zo, sai biyu suka zo wajan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai daya ya tafi, ya tashi tsaye A kan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Amma dayansu, sai ya ga wani rata a cikin zobe ya zauna a ciki, dayan kuma ya zauna a bayansu. Na uku, ya yi nasarar tafiya. Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gama ya ce: "Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsa
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، دار طوق النجاة، ط: الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي – بيروت.
رياض الصالحين، للنووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق -بيروت، ط: الأولى 1428هـ.
نزهة المتقين، لمجموعة من المؤلفين، مؤسسة الرسالة، ط: الرابعة عشر،1407هـ.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، بإشراف مؤسسة الشيخ، دار الوطن للنشر، الرياض، ط: 1426هـ.
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي، دار ابن الجوزي، السعودية، ط: الثالثة 1418هـ.
تطريز رياض الصالحين، تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة -الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
صفات الله عز وجل الواردة في الكتاب والسنة: علوي بن عبد القادر السَّقَّاف، دار الهجرة الطبعة: الثالثة ، 1426هـ - 2006م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سمرة بن جندب رضي الله عنه قال: لقد كنت على عَهْدِ رسولِ الله صلى الله عليه وسلم غُلاما، فكنت أحفظ عنه، فما يمنعني من القول إلا أن هاهنا رِجَالًا هم أَسَنُّ مِنِّي.
Daga Samra bin Jundub - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Na kasance a lokacin Manzon Allah -SAW- yaro ne, kuma na kasance ina kiyaye shi daga gare shi, don haka me ya hana ni fada sai dai a nan maza sun girme ni.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Samra bin Jundub - yardar Allah ta tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa shi saurayi ne a lokacin Manzon Allah -SAW- kuma ya kasance yana haddace wasu maganganun nasa - Allah ya kara masa yarda - kuma abin da ke hana shi sabunta su sai dai akwai wani wanda ya girme shi.
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى 1418هـ.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، محمد علي بن البكري بن علان، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، الطبعة: الرابعة 1425هـ.
رياض الصالحين، للنووي، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى 1428هـ.
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، كنوز إشبيليا، الرياض، الطبعة: الأولى 1430هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ أَعْرَابِيًّا أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ دَخَلْتُ الجَنَّةَ، قَالَ: «تَعْبُدُ اللَّهَ لاَ تُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلاَةَ المَكْتُوبَةَ، وَتُؤَدِّي الزَّكَاةَ المَفْرُوضَةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ» قَالَ: وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لاَ أَزِيدُ عَلَى هَذَا، فَلَمَّا وَلَّى قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَنْظُرَ إِلَى رَجُلٍ مِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ، فَلْيَنْظُرْ إِلَى هَذَا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Cewa wani balaraben kauye ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan" Ya ce: Na rantse da Wanda raina yake a hannunSa, ba zan yi kari akan wannan ba, lokacin da ya juya ya tafi sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda yake son ya kalli wani mutum daga 'yan aljanna, to ya yi duba zuwa ga wannan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.
Fa’idoji
- Kadaita Allah - Madaukakin sarki - da ibada shi ne farkon abinda ake farawa da shi a kira zuwa ga Allah.
- Takaituwa da koyar da wajibai ga wanda ya zama farkon shiga Musulunci.
- Kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - babu makawa daga bi a sannu a sannu.
- Kwadayin mutumin akan neman sanin al'amarin Addininsa
- Idan musulmi ya takaita akan wajibai to cewa shi ya tsira, saidai anan ba ya nufin sakaci ga nafilifili; domin nafila ana cike tawayar farilla da ita.
- Kebance wasu daga ibadu da ambato dalili ne akan muhimmancinsu da kwadaitarwa akan su, (hakan) ba ya nufin rashin wajabcin waninta.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 105) (1397).
صحيح مسلم (1/ 44) (14).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 588).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 349).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 861).
منار القاري، لحمزة قاسم (3/ 5).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (1/ 82).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ أَبِي لَيْلَى قَالَ: لَقِيَنِي كَعْبُ بْنُ عُجْرَةَ، فَقَالَ: أَلاَ أُهْدِي لَكَ هَدِيَّةً؟ إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَيْنَا، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَدْ عَلِمْنَا كَيْفَ نُسَلِّمُ عَلَيْكَ، فَكَيْفَ نُصَلِّي عَلَيْكَ؟ قَالَ: «فَقُولُوا: اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ».
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.
Fa’idoji
- Magabata sun kasance suna musayar kyautar mas'alolin ilimi.
- Wajabcin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Tahiyar karshe a sallah.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa sahabbansa sallama da salati gare shi.
- Wannan sigar ita ce mafi cikar sigogi a salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 77) (6357).
صحيح مسلم (1/ 305) (406).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص208).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 270).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 170).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ تَعَلَّمَ عِلْمًا مِمَّا يُبْتَغَى بِهِ وَجْهُ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ لَا يَتَعَلَّمُهُ إِلَّا لِيُصِيبَ بِهِ عَرَضًا مِنَ الدُّنْيَا لَمْ يَجِدْ عَرْفَ الْجَنَّةِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ» يَعْنِي رِيحَهَا.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima» wato ƙanshinta.
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya nemi sanin ilimin shari'a wanda asali a cikinsa shi ne a nufi yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi ba ya nemansa ba ne kawai sai dan ya samu wani rabo da wani jin daɗi na duniya da shi na dukiya ko alfarma to ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙiyama.
Fa’idoji
- Wajabcin ikhlasi a cikin neman ilimi, da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
- Gargaɗarwa mai tsanani daga riƙo da ilimin shari'a saboda riya ko abin neman duniya, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
- Cewa wanda ya nemi ilimi saboda Allah - Maɗaukakin sarki - sai duniya ta zo masa dan bi to ya halatta ya karɓeta, hakan ba zai cutar da shi ba.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (ƙanshin aljanna): ƙanshi, kai matuƙa ne a cikin haramta aljanna; domin cewa duk wanda ba zai ji ƙanshin abu ba to ba zai same shi ba.
- Wanda ya koyi wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah da shi saboda neman aiki, ko saboda wasu buƙatu na duniya daban; to wajibi ne ya tuba zuwa ga Allah daga hakan, Allah zai goge masa abinda ya faru na gurɓatacciyar niyya kuma Shi Ma'abocin falala ne Mai girma - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
- Wannan gargaɗarwar ga mai neman ilimin shari'a ne, amma wanda ya nemi wani ilimi daga cikin ilimummukan duniya saboda jin daɗin duniya kamar Injiniyarin ko Kimiyya da wasunsu saboda duniya to shi niyyarsa ta tabbata gare shi.
Madogara
سنن أبي داود (5/ 504) (3664).
سنن ابن ماجه (1/ 169) (252).
مسند أحمد (14/ 169) (8457).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 477).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 507).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 957).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 447).
عون المعبود شرح سنن أبي داود، العظيم آبادي (10/ 70).
حاشية السندي على سنن ابن ماجه، لمحمد التتوي (1/ 110).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ سُئِلَ عن عِلْمٍ فَكَتَمَهُ، أُلْجِمَ يوم القيامةِ بِلِجَامٍ مِنْ نارٍ».
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya ce:"Duk wanda aka yambaye shi wani ilimi sai ya boye shi to za'a yi masa linzami da shi na wuta a Ranar Alkiyama"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- الجامع الصحيح –وهو سنن الترمذي-؛ للإمام محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق أحمد شاكر وآخرين، مكتبة الحلبي-مصر، الطبعة الثانية، 1388هـ.
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح؛ تأليف ملا علي القاري، تحقيق صدقي العطار، دار الفكر-بيروت، الطبعة الأولى، 1412هـ.
- مشكاة المصابيح؛ تأليف محمد بن عبدالله التبريزي، تحقيق محمد ناصر الدين الألباني، المكتب الإسلامي-بيروت، الطبعة الثانية، 1399هـ.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- سنن أبي داود, أبو داود سليمان بن الأشعث بن إسحاق بن بشير بن شداد بن عمرو الأزدي السِّجِسْتاني, المحقق: محمد محيي الدين عبد الحميد, المكتبة العصرية، صيدا – بيروت.
- مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
- مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
- بهجة الناظرين, سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م.
- سنن ابن ماجه, ابن ماجه أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي, الناشر: دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي.
- مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، أبو الحسن عبيد الله بن محمد الرحماني المباركفوري, الناشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء - الجامعة السلفية، بنارس الهند, الطبعة: الثالثة - 1404 هـ، 1984 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «نَضَّرَ اللَّهُ امْرَأً سَمِعَ مِنَّا شَيْئًا فَبَلَّغَهُ كَمَا سَمِعَ، فَرُبَّ مُبَلِّغٍ أَوْعَى مِنْ سَامِعٍ».
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan haddace sunnar Annabi, da isar da ita ga mutane.
- Bayanin falalar ma'abota hadisi, da ɗaukakar nemansa.
- Falalar malamai waɗanda sune ma'abota istinbaɗi da fahimta.
- Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su -, su ne waɗanda suka ji hadisin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma suka isar da shi garemu.
- AlManawi ya ce: Ya bayyana anan cewa maruwaicin hadisi Fiƙihu ba sharaɗinsa ba ne, sharaɗinsa kawai shi ne hadda, kuma ya wajaba ga masanin fiƙihu fahimta da jujjuya ma'ana.
- Ibnu Uyaina ya ce: Babu wani da zai nemi hadisi sai a fuskarsa akwai ni'ima ga wannan hadisin.
- Hadda a wajen malaman hadisi nau'i biyu ce: Hadda ta zuciya da ƙirji, da hadda ta rubutu da zanawa, su biyun addu'ar a cikin hadisin ta ƙunshe su.
- Fahimace-fahimcen mutane mabanbanta ne, wataƙila wanda aka isarwa ya zama ya fi kiyayewa daga wanda ya ji, da yawa wanda ya dakko fiƙihu ya zama ba faƙihi ba.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 394) (2657).
سنن ابن ماجه (1/ 157) (232).
مسند أحمد (7/ 221) (4157).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 476).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 446).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، لعبدالرؤوف المناوي (3/ 206).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 496).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 956).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن مسروق، قال: دخَلْنَا على عبد الله بن مسعود رضي الله عنه فقال: يا أيها الناس، من عَلِم شيئا فَلْيَقُلْ به، ومن لم يَعْلَم، فَلْيَقُلْ: الله أعلم، فإن من العلم أن يقول لما لا يَعْلَم: الله أعلم. قال الله تعالى لنبيه صلى الله عليه وسلم : (قل ما أسألكم عليه من أجر وما أنا من المتكلفين).
Daga Masruq ya ce Mun shiga wajen Ibn Mas'ud -Allah ya yarda da shi- sai ya ce:Ya Ku Mutane, duk wanda yasan Wani abu daga cikin kuto ya faxe shi kuma duk wanda bai sani ba to ya ce: Allah ne mafi sani, saboda yana daga cikin Ilimi ya ce a abunda bai sani ba Allah shi ne mafi sani, Allah SWT ya ce da Annabinsa SAW: "Kace ban tambayeku lada ba kan abnda nazo muku da shi, kuma ni ban zamanto cikin masu shishigi ba"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ
رياض الصالحين، تأليف : محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ
مطالع الأنوار على صحاح الآثار، تأليف: إبراهيم بن يوسف بن أدهم ابن قرقول، تحقيق: دار الفلاح للبحث العلمي وتحقيق التراث، الناشر: وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية - دولة قطر، الطبعة: الأولى، 1433 هـ - 2012 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com