عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «السَّاعِي عَلَى الأَرْمَلَةِ وَالمِسْكِينِ، كَالْمُجَاهِدِ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، أَوِ القَائِمِ اللَّيْلَ الصَّائِمِ النَّهَارَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.
Fa’idoji
- Kwadaitarwa akan taimamkekeniya da toshe bukatun masu rauni.
- Ibada ta kunshi kowane aiki na gari, daga ibada akwai kaikawo ga wacce mijinta ya rasu da kuma miskini.
- Dan Hubaira ya ce: Abin nufi cewa Allah - Madaukakin sarki - Zai tattaro masa ladan mai azimi da mai tsayuwar (dare) alokaci daya; saboda shi ya tsaya ga matar da mijinta ya rasu a matsayin mijinta..., ya kuma tsaya ga miskinin da ya gajiya daga tsayuwa akan kansa, sai ya ciyar da wannan ragowar abincinsa, ya kuma yi sadaka da karfinsa, sai amfaninsa ya zama ya yi daidai da azimi da tsayuwar dare da kuma yaki.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 62) (5353).
صحيح مسلم (4/ 2286) (2982).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم بن عيد الهلالي (1/ 351).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل بن عبد العزيز المبارك (ص198).
رياض الصالحين (ص107) (265).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 99).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (275).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ ثَوْبَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْضَلُ دِينَارٍ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ، دِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى عِيَالِهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ الرَّجُلُ عَلَى دَابَّتِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ، وَدِينَارٌ يُنْفِقُهُ عَلَى أَصْحَابِهِ فِي سَبِيلِ اللهِ» قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَبَدَأَ بِالْعِيَالِ، ثُمَّ قَالَ أَبُو قِلَابَةَ: وَأَيُّ رَجُلٍ أَعْظَمُ أَجْرًا مِنْ رَجُلٍ يُنْفِقُ عَلَى عِيَالٍ صِغَارٍ، يُعِفُّهُمْ أَوْ يَنْفَعُهُمُ اللهُ بِهِ وَيُغْنِيهِمْ.
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
(Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana wasu Nau’uka a cikin ciyarwa, ya kuma jerantasu idan fuskokin ciyarwar sun gagara gwargwadan mafi wajabci akanka, sai ya fara da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci; sai ya sanar da cewa mafi yawan dukiya a lada ita ce wadda musulmi yake ciyar da ita ga wanda ciyarwarsa ta wajaba akan shi; kamar mata da ɗa, sannan ciyarwa ga abin hawa wanda aka tanada dan yaƙi a tafarkin Allah, sannan ciyarwa ga abokansa da ayarinsa a halin kasancewarsu mayaƙa a tafarkin Allah.
Fa’idoji
- Jeranta ciyarwa a falala ta fuskar da aka ambata, sai a lura da hakan a lokacin da suka taru.
- Bayanin cancantar ciyarwa ga iyali a falala akan wasunsu.
- Ciyarwa a yaƙi saboda Allah tana daga mafi girman ciyarwa, kamar tanadar kaya da mayaka a Jihadi.
- An ce: Abin nufi da tafarkin Allah dukkanin aikin ɗa'a kamar aikin hajji a misali.
Madogara
صحيح مسلم (2/ 691) (994).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 315).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 156).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 291).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 374).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا تَوَضَّأَ الْعَبْدُ الْمُسْلِمُ -أَوِ الْمُؤْمِنُ- فَغَسَلَ وَجْهَهُ خَرَجَ مِنْ وَجْهِهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ نَظَرَ إِلَيْهَا بِعَيْنَيْهِ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ-، فَإِذَا غَسَلَ يَدَيْهِ خَرَجَ مِنْ يَدَيْهِ كُلُّ خَطِيئَةٍ كَانَ بَطَشَتْهَا يَدَاهُ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ-، فَإِذَا غَسَلَ رِجْلَيْهِ خَرَجَتْ كُلُّ خَطِيئَةٍ مَشَتْهَا رِجْلَاهُ مَعَ الْمَاءِ -أَوْ مَعَ آخِرِ قَطْرِ الْمَاءِ- حَتَّى يَخْرُجَ نَقِيًّا مِنَ الذُّنُوبِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ko mumini ya yi alwala sai ya wanke fuskarsa a cikin alwalar duk ƙaramin kuskuren da ya kalla da idanuwansa zai fita daga fuskarsa tare da ruwan da ya zuba bayan wankewar ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke hannayensa kowane ƙaramin kuskuren da hannayensa suka aikata shi zai fita daga hannayensa tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke ƙafafuwansa kowane ƙaramin kuskuren da ƙafafuwansa suka taka (zuwa gare shi) zai fita tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan har sai ya fita tsarkakke daga ƙananan zunubai idan ya gama alwalar.
Fa’idoji
- Falalar kiyayewa akan alwala, kuma cewa ita tana kankare zunubai.
- Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana kwaɗaitar da mutane a cikin ayyukan ɗa'a da kuma ibadu ta hanyar ambatan lada da sakamako akan su.
- Kowace gaɓa daga gaɓɓan mutum tana faɗawa cikin wani abu daga saɓo, saboda haka zunubai suke bin kowace gaɓar da ta aikatasu, kuma suna fita daga kowace gaɓar da ya tuba daga gareta.
- Alwala, a cikinta akwai tsarkaka ta gani ɓaro-ɓaro, kuma tana kasancewa ne a lokacin da kake wanke gaɓɓan alwala, da kuma tsarkakewa ta ma'ana tana kasancewa ne daga zunuban da suka faru daga gaɓɓan.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 215) (244).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 108).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 181).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 208).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 157).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا، أَوَلَا أَدُلُّكُمْ عَلَى شَيْءٍ إِذَا فَعَلْتُمُوهُ تَحَابَبْتُمْ؟ أَفْشُوا السَّلَامَ بَيْنَكُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, Ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, , shin ba na shiryar daku akan abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a tsakaninku".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bayyana cewa ba masu shiga aljanna sai muminai, kuma imani ba ya cika, sannan halin jama'ar musulmai ba ya gyaruwa har sai sashinsu yaso sa shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya shiryar zuwa mafificin al'amuran da su ne soyayya take gamewa, ita ce yada sallama tsakanin musulmai, wacce Allah Ya sanyata gaisuwa ga bayinSa.
Fa’idoji
- Shiga aljanna ba ya kasancewa saida imani.
- Daga cikar imani musulmi ya so wa dan uwansa abinda yake sowa kansa.
- An so yada sallama da shinfidata ga musulmai; dan abinda ke cikinta na yada soyayya da aminci tsakanin mutane.
- Ba'ayin sallama sai ga musulmi; saboda fadinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi -: "A tsakaninku".
- Yada sallam Akwai dauke damuwa da kauracewa da gaba ta hanyar yin sallama.
- Muhimmancin soyayya tsakanin musulmai, kuma cewa ita tana daga cikar imani.
- Ya zo a cikin wani hadisin daban cewa sigar sallama cikakkiya: "Assalamu alaiku warahmatullahi wa barakatuh ", ya isa a ce: "Assalamu alaikum".
Madogara
صحيح مسلم (1/ 74) (54).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 129).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص515).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 394).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 661).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سعيد الخُدْرِي رضي الله عنه قال: جاءت امرأة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، ذهب الرجال بِحَدِيثِكَ، فاجْعَل لنَا من نَفْسِك يومًا نَأتِيكَ فيه تُعَلِّمُنَا مما عَلَّمَكَ الله، قال: «اجْتَمِعْنَ يَوَم كَذَا وكَذَا» فَاجْتَمَعْنَ، فأتَاهُنَّ النبي صلى الله عليه وسلم فَعَلَّمَهُنَّ مما عَلَّمَهُ الله، ثم قال: «ما مِنْكُنَّ من امرأة تُقَدِّمُ ثَلاَثَة من الولد إلا كانوا حِجَابًا من النَّارِ» فقالت امرأة: واثنين؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «واثنين».
Daga Abu Sa`id al-Khudri - yardar Allah ta tabbata a gare shi - wanda ya ce: Wata mata ta zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta ce: Ya Manzon Allah, mutanen ya tafi tare da maganarka, don haka ka sanya mana wata Rana daga gareka da za mu koya daga gareka kamar yadda ka koya daga abin da Allah ya sanar da kai Sai ya ce: kum haxu Ranar Kaza da Kaza sai suka tarun sai Manzon Allah SAW ya zo musu sai ya koyar da su abunda Allah ya sanar da shi, sannan ya ce: “Babu wata Mace daga cikinku da zata rasa 'Ya'yanta Uku sai sun kasance Mata Katanga daga Wuta" "Da biyu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wata mata ta ce wa Annabi - SAW -: Maza sun shagaltar da kai ga barin mu a kowane lokaci, don haka ba za mu iya sake samun lokacin da za mu sadu da kai ba har mu tambaye ka game da addininmu, saboda sun kasance tare da kair tsawon rana. Don haka ka sanyawa mata ranar da za mu hadu da kai don karantar da mu game da addininmu, don haka Annabi - SAW- ya ware musu rana don su hadu, don haka matan suka hadu a ranar kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kebe su, don haka ya zo wurinsu ya koyar da su abin da Allah ya sanar da shi na abin da suke bukata na ilmi.Sai ya ce musu babu wata mace a cikinsu da 'ya'ya uku sun mutu, mace ko namiji, don haka ta kawo su lahira, cikin haƙuri da tausayi, sai dai idan sun same ta don kare ta daga wuta kuma idan ta neme ta da zunubanta, to wata mace ta ce: Kuma idan biyu daga gare ta yara sun mutu, shin za a ba ta lada ga duk wanda ‘ya’yanta uku suka mutu? Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Haka nan kuma idan ‘ya’yanta biyu suka mutu, ladanta shi ne ladar wanda ya mutu a kan‘ ya’yanta uku.
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407هـ.
بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م.
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428هـ.
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ.
دليل الفالحين، تأليف: محمد بن علان، الناشر: دار الكتاب العربي، نسخة الكترونية، لا يوجد بها بيانات نشر.
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426هـ.
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، تأليف: علي بن سلطان القاري، الناشر: دار الفكر، الطبعة: الأولى، 1422هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «لا يَمُوتُ لأحَدٍ من المسلمين ثلاثة من الوَلَد فتَمسُّه النَّار إلا تَحِلَّة القَسَم».
Daga Abu Huraira =Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wani Mutum daga cikin Musulmai da 'Ya'yansa uku zasu Mutu sannan kuma wuta ta tava shi sai karayar rantsuwa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Idan mutum yaransa maza guda uku ko kuma mata biyu Suka Mutu kadai, ko kuma maza da mata, to, Allah - Madaukaki - ya haramta jikinsa cin wuta, idan ya yi hakuri, kuma ya nemi ladan Allah, kuma ya gamsu da hukuncin Allah Madaukakin Sarki ya Hukunta, da da Kaddararsa wacce take kubutar da Rantsuwa, ga wanda yake ketare Siraxi. Domin Allah Madaukaki yana cewa: (Kuma babu wani daga cikinku face sai ya ketare ta)
Madogara
- صحيح البخاري، للإمام محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق محمد الناصر، دار طوق النجاة.
- صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- سنن أبي داود، لأبي داود السجستاني، تحقيق محمد محيي الدين، المكتبة العصرية.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان بن إبراهيم البكري الصديقي الشافعي اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ خُرَيْمِ بْنِ فَاتِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْأَعْمَالُ سِتَّةٌ، وَالنَّاسُ أَرْبَعَةٌ، فَمُوجِبَتَانِ، وَمِثْلٌ بِمِثْلٍ، وَحَسَنَةٌ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، وَحَسَنَةٌ بِسَبْعِ مِائَةٍ، فَأَمَّا الْمُوجِبَتَانِ: فَمَنْ مَاتَ لَا يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ مَاتَ يُشْرِكُ بِاللهِ شَيْئًا دَخَلَ النَّارَ، وَأَمَّا مِثْلٌ بِمِثْلٍ: فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ حَتَّى يَشْعُرَهَا قَلْبُهُ، وَيَعْلَمَهَا اللهُ مِنْهُ كُتِبَتْ لَهُ حَسَنَةً، وَمَنْ عَمِلَ سَيِّئَةً، كُتِبَتْ عَلَيْهِ سَيِّئَةً، وَمَنْ عَمِلَ حَسَنَةً فَبِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، وَمَنْ أَنْفَقَ نَفَقَةً فِي سَبِيلِ اللهِ فَحَسَنَةٌ بِسَبْعِ مِائَةٍ، وَأَمَّا النَّاسُ، فَمُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا مَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الْآخِرَةِ، وَمَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا مُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الْآخِرَةِ، وَمَقْتُورٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمُوَسَّعٌ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ».
Daga Khuraim Dan Fatik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu.
Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai.
Amma masu tabbatattu biyu: Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta.
Amma tamka da tamka: Wanda ya himmantu da kyakkyawa har ya jiyar da zuciyarsa ita, kuma Allah Ya santa daga gareshi za'a rubuta masa kyakkyawa, wanda ya aikata mummuna, za'a rubuta mummuna akansa. Wanda ya aikata kyakkyawa da tamkarta goma, wanda ya ciyar da wani abu a tafarkin Allah to kyakkyawa da dari bakwai.
Amma mutane akwai wanda aka yalwatawa a duniya aka kuntata masa a lahira, da kuma wanda aka kuntatawa a duniya kuma aka yalwata masa a lahira, da wanda aka kuntatawa a duniya da lahira, da wanda aka yalwatawa a duniya da lahira".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ayyuka nau'uka shida ne, kuma mutane sinfi hudu ne. Ayyuka shidan su ne:
Na farko: Wanda ya mutu alhali shi ba ya tarayya da wani abu ga Allah to Aljanna ta tabbata a gare shi.
Na biyu: Wanda ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah wuta ta tabbata a gare shi yana madawwami a cikinta.
Su ne tabbatattu guda biyu.
Na uku: Kyakkyawa da aka niyyata, wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa kuma ya kasance mai gaskiya a cikin niyyarsa har sai ya jiyar da zuciyarsa hakan, kuma Allah Yana sanin wannan niyyar daga gare shi, sannan wani al'amari ya bijiro gareshi ba zai iya aikata wannan kyakkyawan ba za'a rubuta masa kyakkyawa cikakkiya.
Na hudu: Mummuna da aka aikata. wanda ya aikata wata mummuna za'a rubuta masa mummuna daya.
Su biyun: Tamka da tamka ne ba tare da ribanyawa ba.
Na biyar: Kyakkyawar da take da goma irinta, ita ce wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa ya kuma aikatata; za'a rubuta masa kyakkyawa goma.
Na shida: Kyakkyawar da take kasancewa da kaykkyawa dari bakwai, ita ce wanda ya ciyar da wata ciyarwa daya a tafarkin Allah sai a rubuta masa wannan kyakkyawar da kyakkyawa dari bakwai, wannan daga falalarSa ne - tsarki ya tabbara maSa Ya daukaka - da karamcinSa ga bayinSa.
Amma sinfin mutane hudu, su ne:
Na farko: Wanda aka yalwatawa a duniya daga arziki, aka ni'imtar da shi a cikinta yana samun abinda yake so a cikinta, saidai cewa shi abin kuntatawa ne a lahira kuma makomarsa ita ce wuta, shi ne kafiri mawadaci.
Na biyu: Wanda aka kuntatawa a duniya daga arziki, saidai cewa abin yalwatawa ne a lahira, kuma makomarsa ita ce Aljanna, wannan shi ne mmumini talaka.
Na uku: Wanda aka kuntatatawa a duniya da lahira, shi ne kafiri talaka.
Na hudu: Wanda aka yalwatawa a duniya da lahira, shi ne mumini mawadaci.
Fa’idoji
- Girman falalar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa da kuma ribanyawarSa ga kyawawan ayyuka.
- Adalcin Allah da karamcinSa, dan Ya mu'amalance mu a mummuna da adalci, sakamakon mummuna da daya ne.
- Girman shirka da Allah, domin a cikin shirka akwai haramta Aljanna ga wanda ya yi ta.
- Bayanin falalar ciyarwa a tafarkin Allah.
- Ribanya ladan ciyarwa a tafarkin Allah, yana farawa ne daga dari bakwai; domin hakan yana taimakawa akan daukaka kalmar Allah ne.
- Bayanin sinfofin mutane da kuma sabaninsu.
- Ana yalwatawa mumini a duniya da wanda ba mumini ba, amma ba a yalwatawa wani a lahira sai mumini kadai.
Madogara
مسند أحمد (31/ 196) (18900)، (31/ 384)، الفتح الرباني لترتيب مسند أحمد بن حنبل الشيباني (19/198).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com