عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَبَا ذَرٍّ إِذَا طَبَخْتَ مَرَقَةً فَأَكْثِرْ مَاءَهَا، وَتَعَاهَدْ جِيرَانَكَ».
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitarwa Abu Zarr al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - cewa idan zai dafa romo to ya yawaita ruwansa, ya bibiyi maƙotansa da shi.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan kyakkyawar mu'amala tare da maƙota.
- An so yin kyauta tsakanin maƙota; domin hakan yana gadar da soyayya kuma yana ƙara ƙauna, wannan kyautar tana ƙarfafuwa idan abincin yana da ƙanshi, kuma an san buƙatuwar maƙoci (gare shi).
- Kwaɗaitarwa akan bada abin alheri da abinda ya sawwaƙa daga gare shi koda kaɗan ne, da shigar da farin ciki ga musulmai.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2025) (2625). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 386). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 175). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 301).