Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَا زَالَ يُوصِينِي جِبْرِيلُ بِالْجَارِ، حَتَّى ظَنَنْتُ أَنَّهُ سَيُوَرِّثُهُ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.

Fa’idoji
  1. Girman haƙƙin maƙoci da wajabcin kula da hakan.
  2. Ƙarfafawa a kan haƙƙin maƙoci da wasiyyarr da take hukunta larurar girmamashi da nuna soyayya da kyautatawa zuwa gareshi, da tunkuɗe cutarwa daga gareshi, da dubo shi a yayin rashin lafiya, da tayashi murna a yayin farin ciki, da yi masa ta'aziyya a yayin musiba.
  3. A duk lokacin da ƙofar maƙoci ta zama mafi kusa, to, haƙƙinsa ya zama mafi ƙarfi.
  4. Cikar shari'a a cikin abin da ta zo da shi na gyaran zamatakewa wajen kyautatawa maƙota da tunkuɗe cuta daga garesu.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 10) (6014)، (8/ 10) (6015). صحيح مسلم (4/ 2025) (2624)، (4/ 2025) (2625). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (1/ 300). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 175).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SULHU DA HUKUNCE-HUKUNCEN MAƘOTAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com