عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَا زَالَ يُوصِينِي جِبْرِيلُ بِالْجَارِ، حَتَّى ظَنَنْتُ أَنَّهُ سَيُوَرِّثُهُ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.
Fa’idoji
Girman haƙƙin maƙoci da wajabcin kula da hakan.
Ƙarfafawa a kan haƙƙin maƙoci da wasiyyarr da take hukunta larurar girmamashi da nuna soyayya da kyautatawa zuwa gareshi, da tunkuɗe cutarwa daga gareshi, da dubo shi a yayin rashin lafiya, da tayashi murna a yayin farin ciki, da yi masa ta'aziyya a yayin musiba.
A duk lokacin da ƙofar maƙoci ta zama mafi kusa, to, haƙƙinsa ya zama mafi ƙarfi.
Cikar shari'a a cikin abin da ta zo da shi na gyaran zamatakewa wajen kyautatawa maƙota da tunkuɗe cuta daga garesu.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 10) (6014)، (8/ 10) (6015).
صحيح مسلم (4/ 2025) (2624)، (4/ 2025) (2625).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (1/ 300).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 175).
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ya Abu Zarr idan zaka dafa romo to ka yawaita ruwansa, ka bibiyi maƙotanka da shi".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitarwa Abu Zarr al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - cewa idan zai dafa romo to ya yawaita ruwansa, ya bibiyi maƙotansa da shi.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa akan kyakkyawar mu'amala tare da maƙota.
An so yin kyauta tsakanin maƙota; domin hakan yana gadar da soyayya kuma yana ƙara ƙauna, wannan kyautar tana ƙarfafuwa idan abincin yana da ƙanshi, kuma an san buƙatuwar maƙoci (gare shi).
Kwaɗaitarwa akan bada abin alheri da abinda ya sawwaƙa daga gare shi koda kaɗan ne, da shigar da farin ciki ga musulmai.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2025) (2625).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 386).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 175).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 301).
Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.
Fa’idoji
Kore imani ga wanda maƙocinsa ba ya aminta daga zalincinsa da sharrinsa yana nuni akan cewa shi yana daga manyan zunubai, kuma cewa mai aikata shi mai tauyayyen imani ne.
Kwaɗaitarwa mai ƙarfi akan kyautatawa maƙoci da barin cutar da shi da magana ne ko da aiki.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 10) (6016).
التوضيح لشرح الجامع الصحيح (28/ 321).
النهاية في غريب الحديث والأثر (93).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com