Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa

عَنْ أَبِي شُرَيْحٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ»، قِيلَ: وَمَنْ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «الَّذِي لاَ يَأْمَنُ جَارُهُ بَوَايِقَهُ».
Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.

Fa’idoji
  1. Kore imani ga wanda maƙocinsa ba ya aminta daga zalincinsa da sharrinsa yana nuni akan cewa shi yana daga manyan zunubai, kuma cewa mai aikata shi mai tauyayyen imani ne.
  2. Kwaɗaitarwa mai ƙarfi akan kyautatawa maƙoci da barin cutar da shi da magana ne ko da aiki.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 10) (6016). التوضيح لشرح الجامع الصحيح (28/ 321). النهاية في غريب الحديث والأثر (93).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SULHU DA HUKUNCE-HUKUNCEN MAƘOTAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com