Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 49

At-Tawba 9:49

التوبة

وَمِنْهُم مَّن يَقُولُ ٱئْذَن لِّى وَلَا تَفْتِنِّىٓ ۚ أَلَا فِى ٱلْفِتْنَةِ سَقَطُوا۟ ۗ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌۢ بِٱلْكَـٰفِرِينَ

Ma’ana

Kuma daga cikinsu[1] akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.

[1] Kuma a yanzu ga yãƙin Tabũka (munafukai) sun bayyana da irin uzurran da suke kãwowa dõmin kada su fita kamar mai cewa" To, Allah Ya hana zina, idan na fita nã gã mãtan Rũmãwa, bã zan iya yin haƙuri daga barinsu ba' sabõdahaka inã son a karbi uzurina kada a jefa ni a cikin fitina." Bai sani ba. da wannan rashin fitar ya jefa kansa a cikin fitinar. Dõmin zã a bar shi tãre da mãtã, sũ da shi kawai.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net