At-Tawba 9:48
التوبةلَقَدِ ٱبْتَغَوُا۟ ٱلْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُوا۟ لَكَ ٱلْأُمُورَ حَتَّىٰ جَآءَ ٱلْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ ٱللَّهِ وَهُمْ كَـٰرِهُونَ
Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo,[1] kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,
[1] Tun farkon zuwan Annabi a Madĩna mũnafukai sun yi ta yin kaidi dõmin su ɓãta al'amarin Annabi da Musulunci, suka kãsa, har gaskiya ta bayyana, suka kãma bakinsu dõmin rashin abin da zã su iya faɗã a yarda da shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net