Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 117

At-Tawba 9:117

التوبة

لَّقَد تَّابَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلنَّبِىِّ وَٱلْمُهَـٰجِرِينَ وَٱلْأَنصَارِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ فِى سَاعَةِ ٱلْعُسْرَةِ مِنۢ بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ مِّنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّهُۥ بِهِمْ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ

Ma’ana

Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da[1] Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su.

[1] Yã fãra gabãtar da cewa, "Allah Yã karɓi tũbar Annabi da waɗanda Ya ambata tãre da shi," dõmin ya biyar ãyar da ke zuwa ta tũbar waɗanda suka yi zamansu, bã da wani uzuri ba, kuma sũ bã munãfuƙai ba, aka jinkirtar da maganar tũbarsu har a bãyan hõron kwãna hamsin bãbu mai yi musu magana, bisa hanin Allah. Kuma dã an ambaci karɓar tũbarsu kawai bã da an gabãtar da tũbar waɗanda suka fita ba, dã sai a ce sun fi waɗanda suka fita, dõmin an yi nassi a kan tũbarsu. Wanda aka yi nassi akan tũbarsa, yã fi wanda. aka bari a cikin duhu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net