At-Tawba 9:116
التوبةإِنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ يُحْىِۦ وَيُمِيتُ ۚ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا نَصِيرٍ
Lalle ne Allah Yanã[1] da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
[1] Wannan ãyã tanã nũna cewa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alheri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net