Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 118

At-Tawba 9:118

التوبة

وَعَلَى ٱلثَّلَـٰثَةِ ٱلَّذِينَ خُلِّفُوا۟ حَتَّىٰٓ إِذَا ضَاقَتْ عَلَيْهِمُ ٱلْأَرْضُ بِمَا رَحُبَتْ وَضَاقَتْ عَلَيْهِمْ أَنفُسُهُمْ وَظَنُّوٓا۟ أَن لَّا مَلْجَأَ مِنَ ٱللَّهِ إِلَّآ إِلَيْهِ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ لِيَتُوبُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Ma’ana

Kuma (Allah) Yã karɓi tũba a kan ukun[1] nan waɗanda aka jinkirtar har ƙasa da yalwarta ta yi ƙunci a kansu, kuma rãyukansu suka yi ƙunci a kansu, kuma suka yi zaton bãbu wata mafakã daga Allah fãce (kõmãwa) zuwa gare Shi. Sa'an nan Allah Ya karɓi tũbarsu, dõmin su tabbata a kan tũba. Lalle Allah ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

[1] Sũ mutãne uku waɗan da aka jinkintar da al'amarinsu, a ãyã ta l06, sũ ne Ka'abu bn Mãliki da Marãratu bn Rabĩ'a el Umary, da Hilãlu bn Umaiya el Wãƙify. Sun ƙi fita, bã da wani uzuri ba, kuma a lõkacin da Annabi ya kõmo daga Tabũka, waɗanda ba su fita ba suka tafi suka faɗi uzurõrinsu na rashin fitã. Annabi ya karɓa musu Kuma ya nema musu gãfara. Amma su ukun, suka faɗi gaskiya cewa sun zauna ne bã dõmin munãfunci ba, sai dai abin yã kasance haka kawai bã da wani uzuri ba. To, Annabi ya ce su dãkata, sai abin da Allah Ya ce a kansu. Aka hana kõwa ya yi musu magana a cikin Madĩna, har mãtansu na aure. Suka yi kwãna hamsin a cikin matsuwa, sa'an nan Allah Ya sauko da tũbarsu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net