Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 107

At-Tawba 9:107

التوبة

وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ مَسْجِدًا ضِرَارًا وَكُفْرًا وَتَفْرِيقًۢا بَيْنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَإِرْصَادًا لِّمَنْ حَارَبَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ مِن قَبْلُ ۚ وَلَيَحْلِفُنَّ إِنْ أَرَدْنَآ إِلَّا ٱلْحُسْنَىٰ ۖ وَٱللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ

Ma’ana

Kuma waɗanda[1] suka riƙi wani masallãci dõmin cũta da kãfirci da nẽman rarrabẽwa a tsakãnin muminai da fakẽwã ga taimakon wanda ya yãƙi Allah da ManzonSa daga gabãni, kuma haƙĩƙa sunã yin rantsuwa cẽwa, "Ba mu yi nufin kõmai ba fãce alhẽri", alhãli kuwa Allah Yanã yin shaida cẽwa, su, haƙĩƙa, maƙaryata ne.

[1] Wata ƙungiyã ta munãfukai mãsu aiki dõmin tumɓuke ƙarfin Musulmi ta hanyar da bã a iya gãnewa da sauri. Kamarsu gina masallaci kusa da wani tsõhon masallãci da sũnan taimakon addĩni amma da nufin su raba jama'ar Musulmi,kuma sun sãmi wurin da zã su riƙa tãro da ɓõye kãyan yãƙi da shirin sharri ga Musulmi. Kamar ma'abũta Masjidil Darãr, wanda aka yi kusa da masallacin Kuba a Madĩna. Aikinsu bai tsaya ga lõkacin yãƙin Tabũka ba, sabõda haka aka ce: da bagewa ga wanda ya yãƙi Allah a gabãni, watau a gabãnin bayyanar fallasar munãfukai da yãƙin Tabũka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net