Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 106

At-Tawba 9:106

التوبة

وَءَاخَرُونَ مُرْجَوْنَ لِأَمْرِ ٱللَّهِ إِمَّا يُعَذِّبُهُمْ وَإِمَّا يَتُوبُ عَلَيْهِمْ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Ma’ana

Kuma da waɗansu waɗanda[1] aka jinkirtar ga umurnin Allah, kõ dai Ya yi musu azãba kõ kuma Ya karɓi tũba a kansu. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.

[1] Wata ƙungiya wadda ita ba munãfuka ba ce, amma kuma ba su fita zuwa yãƙin ba, kuma bã su da wani dalĩli sai kasãla kawai da taushewar Shaiɗan. Waɗannan an jinkirtar da al'amarinsu har Allah Ya yi hukunci a kansu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net