Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 9 · Aya ta 108

At-Tawba 9:108

التوبة

لَا تَقُمْ فِيهِ أَبَدًا ۚ لَّمَسْجِدٌ أُسِّسَ عَلَى ٱلتَّقْوَىٰ مِنْ أَوَّلِ يَوْمٍ أَحَقُّ أَن تَقُومَ فِيهِ ۚ فِيهِ رِجَالٌ يُحِبُّونَ أَن يَتَطَهَّرُوا۟ ۚ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلْمُطَّهِّرِينَ

Ma’ana

Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne, Masallaci wanda aka yi harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini, shĩ ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai waɗansu maza sunã son su tsarkaka[1]. Kuma Allah Yanã son mãsu nẽman tsarkakuwa.

[1] Sunã son tsarkaka ta ɓõye da ta bayyane. Ta ɓõye sananniya ce: ita ce rashin munãfunci, kuma ta bayyane ita ce sunã kãma rũwa a bãyan sun karce kãshinsu da dũtse, kamar yadda ya zo a cikin Hadĩsi. Allah ne Mafi sani.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tawba

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net