Al-A'raaf 7:161
الأعرافوَإِذْ قِيلَ لَهُمُ ٱسْكُنُوا۟ هَـٰذِهِ ٱلْقَرْيَةَ وَكُلُوا۟ مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ وَقُولُوا۟ حِطَّةٌ وَٱدْخُلُوا۟ ٱلْبَابَ سُجَّدًا نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطِيٓـَٔـٰتِكُمْ ۚ سَنَزِيدُ ٱلْمُحْسِنِينَ
Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya[1], kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa."
[1] Alƙaryar ita ce Baitil Maƙdis, bisa shugabancin Yũsha'u. 'Saryarwa,' watau a saryar mana da zunubinmu, yã Allah!, 'Shiga ƙõfa da sujada,' watau da tawãli'u.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net