Al-A'raaf 7:162
الأعراففَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْهُمْ قَوْلًا غَيْرَ ٱلَّذِى قِيلَ لَهُمْ فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِجْزًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُوا۟ يَظْلِمُونَ
Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana[1] watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.
[1] Suka musanya hiɗɗa da hinɗa: watau alkama. (Aya ta 161) Sai aka saukar da azãba a kansu, sabõda haka wannan yã nũna cewa Allah ba ya son a musanya addininSa da kõme, sai dai mutum ya yi shi kamar yadda ya zo masa. Musanyawar umarnin, yãƙi ne a tsakãnin gaskiya da ƙarya. Ma'anar hiɗɗa ita ce kãyar da zunubi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net