Al-A'raaf 7:160
الأعرافوَقَطَّعْنَـٰهُمُ ٱثْنَتَىْ عَشْرَةَ أَسْبَاطًا أُمَمًا ۚ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ إِذِ ٱسْتَسْقَىٰهُ قَوْمُهُۥٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْحَجَرَ ۖ فَٱنۢبَجَسَتْ مِنْهُ ٱثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ ۚ وَظَلَّلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلْغَمَـٰمَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلْمَنَّ وَٱلسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا رَزَقْنَـٰكُمْ ۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen[1] da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.
[1] Watau dũtsen da ya gudu da tufafinsa ne a lõkacin da yake yin wanka dõmin a nũna wa Banĩ Isra'ila, waɗanda suka sõke shi da gwaiwa, cewa lãfiya lau yake. Kuma aka umurce shi da ɗaukar dũtsen, kuma yanzu aka umurce shi da ya dõke shi dõmin ruwa ya fito sabõda shansu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net