Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 34

An-Nisaa 4:34

النساء

ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ وَبِمَآ أَنفَقُوا۟ مِنْ أَمْوَٰلِهِمْ ۚ فَٱلصَّـٰلِحَـٰتُ قَـٰنِتَـٰتٌ حَـٰفِظَـٰتٌ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُ ۚ وَٱلَّـٰتِى تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهْجُرُوهُنَّ فِى ٱلْمَضَاجِعِ وَٱضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا۟ عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيرًا

Ma’ana

Maza mãsu tsayuwa ne[1] a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. To, sãlihanmãtã mãsu ɗã'a ne, mãsu tsarẽwa ga gaibi sabõda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsõron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wurãren kwanciya, kuma ku dõke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nẽmiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Yã kasance Maɗaukaki, Mai girma.

[1] Allah Ya sanya shugabancin gida da gudanar da tasarrufinsa a hannuwan maza domin ginar jikinsu, da hankalinsu da kuma dukiyarsu da suke ciyarwa ga sadãki da kuma nafaƙar (ciyarwar) gidan. Kuma Allah Ya aza wa mãta ɗa'a ga maza da kuma tsare farjojinsu domin kada su kawo wani baƙon da ba ɗan gida ba, a cikin gidan.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net