Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 35

An-Nisaa 4:35

النساء

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَٱبْعَثُوا۟ حَكَمًا مِّنْ أَهْلِهِۦ وَحَكَمًا مِّنْ أَهْلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصْلَـٰحًا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيْنَهُمَآ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا

Ma’ana

Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta[1]. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.

[1] Hakamãni, ko masu sulhu biyu, su tafi su yi binciken abin da ya hana auren kyau, su tsawaci maras gaskiya daga cikin ma'auran, ko kuma su hukunta rabuwa da hul'i, ko ba da hul'i ba. Abin da suka hukunta alƙãlĩ ya zartar da shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net