Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 33

An-Nisaa 4:33

النساء

وَلِكُلٍّ جَعَلْنَا مَوَٰلِىَ مِمَّا تَرَكَ ٱلْوَٰلِدَانِ وَٱلْأَقْرَبُونَ ۚ وَٱلَّذِينَ عَقَدَتْ أَيْمَـٰنُكُمْ فَـَٔاتُوهُمْ نَصِيبَهُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدًا

Ma’ana

Kuma ga kõwa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwõyinku suka ƙulla[1] ku bã su rabonsu. Lalle ne, Allah Yã kasance, a kan dukkan kõme, Mahalarci.

[1] A zãmanin Jahiliyya ana ƙullin amana a tsakanin ƙabilu ko a tsakanin mutum da wani mutum. Wannan ƙullin amãnar yakan haɗa har da sudusin dukiyar wanda ya mutu daga cikinsu. Wasu Musulmi sun shiga Musulunci a bãyan sun ƙulla irin wannan amãnar sabõda haka Allah Ya yi umurni da cika wannan alkawarin, kuma Ya kashe al'adar, Ya musanya ta da hukunce-hukuncen Musulunci. Kuma ana fassara masu ƙullin rantsuwa da masu gudãnar da aikin rabon dũkiyar gãdo. Ana biyan su ijãrar wahalarsu daga kãwunan magãda kamar yadda ya kamata.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net