Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 186

Aal-i-Imraan 3:186

آل عمران

لَتُبْلَوُنَّ فِىٓ أَمْوَٰلِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ وَلَتَسْمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِكُمْ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوٓا۟ أَذًى كَثِيرًا ۚ وَإِن تَصْبِرُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنْ عَزْمِ ٱلْأُمُورِ

Ma’ana

Lalle ne zã a jarraba[1] ku a cikin dũkiyarku da rãyukanku, kuma lalle ne kuna jin cũtarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra.

[1] Duk wanda ya tsayu da gaskiya ko umurni da alheri, ko hani daga abin da ba a so, to lalle ne sai an cũtar dashi, kuma ba shi da mãgani sai haƙuri, dõmin Allah, da neman taimako daga Allah, da kõmãwa zuwa ga Allah.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net