Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 187

Aal-i-Imraan 3:187

آل عمران

وَإِذْ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَـٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكْتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمْ وَٱشْتَرَوْا۟ بِهِۦ ثَمَنًا قَلِيلًا ۖ فَبِئْسَ مَا يَشْتَرُونَ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa[1] Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!

[1] A cikin wannan akwai gargaɗi ga mãlaman Musulmi, kada su shiga hanyar Yahũdu ta ɓõye ilmin gaskiya, ko kuwa abin da ya sãme su, sũ ma ya sãme su, kuma ya shiga da su mashigarsu. Wãjibi ne akan mãlamai su bãyar da abin da ke hannuwansu na ilmi mai amfãni, mai nũni a kan aikin ƙwarai, kada su ɓõye kõme daga gare shi. Idan sun ɓõye, to, la'anar Allah da malã'iku da ta mutãne zã ta tabbata a kansu, kamar yadda ta tabbata a kan mãlaman Yahũdu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net