Al-Anbiyaa 21:87
الأنبياءوَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَـٰضِبًا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَىٰ فِى ٱلظُّلُمَـٰتِ أَن لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبْحَـٰنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma mai kifi[1] a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."
[1] Shĩ ne Yũnus bn Matta. Yãyi hushi da mutãnensa dõmin ba su karɓi addini ba, sai ya bar su tun a gabãnin a yi masa iznin barinsu. Sai Allah Ya jarrabe shi da fãɗãwã cikin ruwa har wani kĩfi ya haɗiye Shi, sa'an nan kuma ya amãyo Shi a bãyan wahala, ya kõma wa mutãnensa. Suka yĩ ĩmãni.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net