Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

MAS'ALOLIN HUKUNCIN ALLAH NA ƘADDARA

Hadisai 7

Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُصِبْ مِنْهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan Allah Ya yi nufin wani alheri ga bayinsa muminai sai ya jarrabesu a kawunansu da dukiyoyinsu, don abin da zai faru ga mumini na komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da addu'a, da kankare munanan ayyuka, da ɗaukaka darajoji.

Fa’idoji
  1. Lallai mumini abin bijirarwa ne ga nau'o'in bala'i.
  2. Jarrabawa za ta iya kasancewa alama ce ta son Allah ga bawansa, har sai ya daukaka darajarsa, ya ɗaga martabarsa, ya kuma kankare laifinsa.
  3. Kwaɗaitarwa a kan haƙuri a lokacin masifu da rashin ƙorafi.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 115) (5645). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 509). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 98). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص45). نزهة المتقين، مجموعة من المشايخ (1/ 71). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 244). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (3/ 1127).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga mai ɗaga murya da mai aske kanta da mai tsaga kayanta

عَن أَبِي بُرْدَةَ بْنِ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: وَجِعَ أَبُو مُوسَى وَجَعًا شَدِيدًا، فَغُشِيَ عَلَيْهِ وَرَأْسُهُ فِي حَجْرِ امْرَأَةٍ مِنْ أَهْلِهِ، فَلَمْ يَسْتَطِعْ أَنْ يَرُدَّ عَلَيْهَا شَيْئًا، فَلَمَّا أَفَاقَ، قَالَ: أَنَا بَرِيءٌ مِمَّنْ بَرِئَ مِنْهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَرِئَ مِنَ الصَّالِقَةِ وَالحَالِقَةِ وَالشَّاقَّةِ.
Daga Abu Burdah ɗan Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Abu Musa ya yi ciwo ciwo mai tsanani, sai ya suma alhali kansa yana cikin ɗakin wata mata daga iyalansa, bai samu damar da zai dawo mata da komai ba, lokacin da ya farka, ya ce: Ni na kuɓuta (na barranta) daga wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta da shi, Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga mai ɗaga murya da mai aske kanta da mai tsaga kayanta.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Burda - Allah Ya yarda da shi - ya hakaito cewa babansa Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya yi rashin lafiya, rashin lafiya mai tsanani har ya suma, kuma kansa ya zama a ɗakin wata mata daga cikin iyalansa, sai ta yi ihu ta yi masa kukan mutuwa, bai samu damar da zai mayar mata da komai ba saboda sumansa. Lokacin da ya farka ya ce: Lallai cewa shi ya kuɓuta (ya barranta) daga wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga gare shi, lallai cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - haƙiƙa ya kuɓuta daga: Al-Saliƙah: Ita ce mai ɗaga muryarta a lokacin musiba. AlHaliƙah: Ita ce wacce take aske gashin kanta a lokacin musiba. Asshaƙƙah: Ita ce wacce take tsaga tufafinta a lokacin musiba. Domin cewa su suna daga al'amuran Jahiliyya, kai an yi umarni da yin haƙuri a lokacin musiba, da neman ladanta ga Allah.

Fa’idoji
  1. Hani daga tsaga tufa, da aske gashi, da ɗaga murya a lokacin afkuwar musibu, kuma cewa hakan yana daga manyan zunubai.
  2. Baƙin ciki da kuka banda kururuwa da ɗaga murya ba haramun ba ne, hakan ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah, kawai shi tausayi ne.
  3. Haramcin fushi daga ƙaddarorin Allah masu sa raɗaɗi da faɗa ko aikatawa.
  4. Wajabcin haƙuri a lokacin afkuwar musibu.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 81) (1296). صحيح مسلم (1/ 100) (104). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص287). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 371).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne,

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْمُؤْمِنُ الْقَوِيُّ، خَيْرٌ وَأَحَبُّ إِلَى اللهِ مِنَ الْمُؤْمِنِ الضَّعِيفِ، وَفِي كُلٍّ خَيْرٌ، احْرِصْ عَلَى مَا يَنْفَعُكَ، وَاسْتَعِنْ بِاللهِ وَلَا تَعْجَزْ، وَإِنْ أَصَابَكَ شَيْءٌ، فَلَا تَقُلْ لَوْ أَنِّي فَعَلْتُ كَانَ كَذَا وَكَذَا، وَلَكِنْ قُلْ قَدَرُ اللهِ وَمَا شَاءَ فَعَلَ، فَإِنَّ (لَوْ) تَفْتَحُ عَمَلَ الشَّيْطَانِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa mumini gaba dayansa alheri ne , sai dai mumini kakkarfa a imaninsa da kudirin niyyarsa da dukiyarsa da wasunsu daga fuskokin karfi shi ne mafi alheri kuma mafi soyuwa ga Allah - Mai girma da daukaka - daga mumini rarrauna. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mumini wasicci da yin riko da sabubba a cikin abinda zai anfane shi na al'amuran duniya da lahira, tare da dogaro ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, da neman taimakonSa, da dogaro gareShi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga gajiyawa da kasala da nauyayawa game da aikata abinda zai yi amfani a duniya da lahira. Idan mumini ya yi kokari a aiki, ya yi riko da sabubba, yana mai neman taimakon Allah, da neman alheri daga Allah, to babu komai akansa sai ya fawwala al'amarinsa gaba dayansa ga Allah, kuma ya sani cewa zabin Allah - Mai girma da daukaka - shi ne alheri. Idan wata musiba ta same shi bayan hakan , to kada ya ce: "Da a ce, ni na aikata da kaza da kaza ya kasance"; "Domin cewa (Da a ce) tana bude aikin Shaidan" A bujirewa kaddara, da dana sani akan abinda ya wuce, sai dai ya ce yana mai mika wuya kuma yana mai yarda: "Kaddarar Allah, abinda Ya so zai aikata", abinda ya afku , kawai shi da hukuncin abinda Allah ya so ne, domin cewa Shi mai aikata abinda Ya yi nufi ne, kuma babu mai juyar da hukuncinSa, kuma babu mai bibiyar HukuncinSa.

Fa’idoji
  1. Banbance banbance mutane a matakan a imani.
  2. An so karfi a ayyuka; Domin yana faruwa ne daga fa'idar abinda ba ya faruwa da rauni.
  3. Mutum ya kamata ya yi kwadayi akan abinda zai anfane shi, kuma ya bar abinda ba zai anfane shi ba.
  4. Yana wajaba akan mumini ya nemi taimakon Allah a dukkanin al'amuransa, kuma kada ya dogara da kansa.
  5. Tabbatar da hukunci da kaddara, kuma shi ba ya kore kokari a sabubba da kokari a neman alkairai.
  6. Hani game da fadin "Da a ce" ta fuskar fushi a lokacin saukar musibu, da haramcin bijirewa hukunci da kaddara ga Allah - Madaukakin sarki -.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2052) (2664). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 492). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 338). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 430).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Idan kuka ji faruwar Annoba a wani gari, to kada ku shige shi, kuma idan ta faru a gari kuna cikinsa, to kada ku futa daga cikinsa"

عن أسامة بن زيد رضي الله عنهما مرفوعاً: «إذا سمعتم الطاعونَ بأرض فلا تدخلوها وإذا وقع بأرض وأنتم فيها فلا تخرجوا منها».
An rawaito daga Usama Bn Zaid -Allah ya yarda da shi daga Annabi: "Idan kuka ji faruwar Annoba a wani gari, to kada ku shige shi, kuma idan ta faru a gari kuna cikinsa, to kada ku futa daga cikinsa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

"Idan Annoba ta faru a wata Kasa kada wani Mutum ya shige ta, Saboda haka bai halatta a shige shi ba, saboda kare lafiyarsa da lafiyar waninsa, kuma idan rashin lafiyar ta shiga gari kuma yana ciki bai halatta gare shi ya futa ba kuma ya wajaba yayi hakuri kan abunda Allah ya kaddara masa don a rubuta masa lada.

Madogara

- صحيح البخاري ،للإمام محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - كنوز رياض الصالحين»،لحمد بن ناصر العمار،دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه. - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. - منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري تأليف- حمزة محمد قاسم مكتبة دار البيان، دمشق - الجمهورية العربية السورية، مكتبة المؤيد، الطائف - المملكة العربية السعودية-1410 هـ - 1990 م. -دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين/محمد علي بن محمد بن علان البكري -اعتنى بها: خليل مأمون شيحا- دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت – لبنان- الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya dauke mu zuwa ga falala, sai ya dauke mu kada mu saba masa a ciki: cewa ba mu fiskar fuska, ba kiran makoki, ba mu raba aljihu, kuma ba mu shimfida gashi.

عن أسيد بن أبي أسيد التابعي، عن امرأة من المبايعات، قالت: كان فيما أخذ علينا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم في المعروف الذي أخذ علينا أن لا نعصيه فيه: أن لا نَخْمِشَ وجهًا، ولا نَدْعُوَ وَيْلًا، ولا نَشُقَّ جَيْبًا، وأن لا نَنْشُرَ شَعْرًا.
Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya dauke mu zuwa ga falala, sai ya dauke mu kada mu saba masa a ciki: cewa ba mu fiskar fuska, ba kiran makoki, ba mu raba aljihu, kuma ba mu shimfida gashi.
Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah SAW "ya kasance yana karban alkawari daga sahabbai kan yi masa mubaya'a cewa ba zai saba masa ba, gami da: kar ta goge fuskarta, ta bugi fuskarta, ko bugun kuncinta, kuma ba ta daga muryarta da makokin da aka hana, ko kuma yayyage tufafinta, kuma ba ya yage gashinta kuma ya tsaga idan yana saukowa. Masifa".

Madogara

نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407هـ. كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430هـ. بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي، سنة النشر: 1418هـ- 1997م. سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا. صحيح الترغيب والترهيب، تأليف: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف، الطبعة: الخامسة. رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل، الطبعة: الأولى، 1428هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can

عن أبي عزة الهذلي رضي الله عنه قال قال رسول الله صلى الله وسلم: «إذا أراد اللهُ قَبْضَ عبد بأرض جعلَ له بها حاجة».
An karvo daga Abi Izza Al-huzali -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Al-Tayalisi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Idan Allah yayi nufin Mutuwar Bawa daga cikin Bayinsa a Wata Qasa ta Musamman baya cikin ta, sai Allah ya sanya masa Buqata a wannan Qasar, kuma idan ya tafi buqatar tasa a wannan Qasa sai Allah ya karvi ransa, da kuma abunda Allah ya Qaddara kuma ya rubuta Masa babu makawa sai ya faru gare shi kamar yadda ya Qaddara shi, kuma wannan yana daga cikin Imani da Hukuncin Allah da Qaddara

Madogara

سنن الترمذي، محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر، ومحمد فؤاد عبد الباقي، وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ، 1975م. مسند الإمام أحمد بن حنبل، أحمد بن حنبل أبو عبدالله الشيباني، تحقيق: شعيب الأرنؤوط و عادل مرشد، وآخرون، تحت إشراف: عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى1421هـ. مسند أبي داود الطيالسي، أبو داود سليمان بن داود الطيالسي، تحقيق: محمد بن عبد المحسن التركي، الناشر: دار هجر، مصر، الطبعة: الأولى، 1419هـ، 1999م. سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، محمد ناصر الدين الألباني، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة الأولى لمكتبة المعارف، 1422هـ. الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية، إسماعيل بن حماد الجوهري الفارابي، تحقيق: أحمد عبد الغفور عطار، دار العلم للملايين، بيروت، الطبعة: الرابعة 1407هـ، 1987م. فيض القدير شرح الجامع الصغير، زين الدين محمد عبد الرؤوف المناوي، المكتبة التجارية الكبرى، مصر، الطبعة: الأولى 1356هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan Allah yana son Al-kairi ga Bawa sai yayi anfani da shi kafin Mutuwarsa

عن عمر الجمعي رضي الله عنه : أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إذا أراد اللهُ بعبدٍ خيرًا استعملَه قبل موتِه» فسأله رجلٌ من القوم: ما استعملَه؟ قال: «يهديه اللهُ عزَّ وجلَّ إلى العمل الصالح قبل موتِه، ثم يقبضه على ذلك».
An karvo daga Umar Al-juma'i -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon ALlah SAW ya ce: "Idan Allah yana son Al-kairi ga Bawa sai yayi anfani da shi kafin Mutuwarsa" sai wani daga cikin Mutane ya tambaye shi, ta yaya zai yi aiki da shi? sai ya ce: "Allah sai ya shirye shi zuwa aiki na gari kafin Mutuwarsa, sannan ya kavi rayuwarsa a kansa"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lallai Allah idan yana nufin Al-kairi ga wani Bawa daga cikin Bayinsa sai ya datar da shi da aiki nagari kafin Mutuwarsa har ya samu ya Mutu kan wannan aikin, sai ya samu kyakkyawan Qarshe, sai ya shiga Al-janna

Madogara

مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م. الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية, أبو نصر إسماعيل بن حماد الجوهري الفارابي, تحقيق: أحمد عبد الغفور عطار, دار العلم للملايين – بيروت, الطبعة: الرابعة 1407 هـ‍ - 1987 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com