Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُصِبْ مِنْهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan Allah Ya yi nufin wani alheri ga bayinsa muminai sai ya jarrabesu a kawunansu da dukiyoyinsu, don abin da zai faru ga mumini na komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da addu'a, da kankare munanan ayyuka, da ɗaukaka darajoji.
Fa’idoji
Lallai mumini abin bijirarwa ne ga nau'o'in bala'i.
Jarrabawa za ta iya kasancewa alama ce ta son Allah ga bawansa, har sai ya daukaka darajarsa, ya ɗaga martabarsa, ya kuma kankare laifinsa.
Kwaɗaitarwa a kan haƙuri a lokacin masifu da rashin ƙorafi.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 115) (5645).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 509).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 98).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص45).
نزهة المتقين، مجموعة من المشايخ (1/ 71).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 244).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (3/ 1127).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com