عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا يَزَالُ البَلاَءُ بِالمُؤْمِنِ وَالمُؤْمِنَةِ فِي نَفْسِهِ وَوَلَدِهِ وَمَالِهِ حَتَّى يَلْقَى اللَّهَ وَمَا عَلَيْهِ خَطِيئَةٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.
Fa’idoji
- Daga cikin rahamar Allah ga bayinSa muminai shi ne ya kankare musu zunubansu a duniyarsu ta hanyar wasu masibu na duniya da aibobinta.
- Bala'i shi akarankansa yana kankare zunubai da sharaɗin imani, idan bawa ya yi hakuri bai yi fushi ba za'a ba shi lada.
- Kwaɗaitarwa akan hakuri a dukkan al'amura, cikin abinda yake so da abinda yake ki, ya yi hakuri har ya bada abinda Allah Ya wajabta masa, kuma ya yi hakuri har ya nisanci abinda Allah Ya haramta, yana kwaɗayin ladan Allah, kuma yana tsoron ukubarSa.
- FaɗinSa: "Da mumini da mumina", karin lafazin mumina a cikinsa akwai dalili akan karin karfafawa ga mace; in ba haka ba da ya ce: "Da mumini" da mace ta shiga cikinsa; domin hakan ba ya kebantar namiji, idan bala'i ya afkawa mace to haka itama an yi mata alkawari da kwatankwacin wannan sakamakon na kankare zunubai da kurakurai.
- Falalar da ta jerantu akan bala'i tana daga abinda zai sawwakawa bawa abinda yake gamuwa da shi na raɗaɗi akai akai.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 204) (2399).
مسند أحمد (13/ 248) (7859).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 113).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص51).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 273).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 80).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضيَ اللهُ عنهما: أنَّهُ قَالَ لعَطَاءِ بْنِ أَبِي رَبَاحٍ: أَلَا أُرِيكَ امْرَأَةً مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَ: هَذِهِ الْمَرْأَةُ السَّوْدَاءُ، أَتَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: إِنِّي أُصْرَعُ وَإِنِّي أَتَكَشَّفُ، فَادْعُ اللهَ لِي، قَالَ: «إِنْ شِئْتِ صَبَرْتِ وَلَكِ الْجَنَّةُ، وَإِنْ شِئْتِ دَعَوْتُ اللهَ أَنْ يُعَافِيَكِ» قَالَتْ: أَصْبِرُ، قَالَتْ: فَإِنِّي أَتَكَشَّفُ فَادْعُ اللهَ أَنْ لَا أَتَكَشَّفَ، فَدَعَا لَهَا.
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.
Fa’idoji
- Haƙuri akan bala'i a duniya yana gadar da aljanna.
- Nawawi ya ce: A cikin sa akwai dalili akan cewa farfaɗiya ana bada lada a kanta mafi cikar lada.
- Kamewa da kunyar matan sahabbai, da kuma kwaɗayinsu akan suturta - Allah Ya yarda da su -, wannan matar ta kasance mafi yawan abinda take jin tsoro shi ne wani abu ya yaye daga jikinta.
- Ibnu Hajar ya ce: Lallai yin riƙo da tsanani shi yafi daga yin riƙo da rangwami ga wanda ya san cewa akan kansa zai iya, kuma ba zai yi rauni ba saboda lazimtar tsanani.
- Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa cewa maganin cututtuka gaba ɗayansu shi ne addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah ya fi tasiri kuma ya fi amfani daga magani da ƙwayoyi, kuma cewa tasirin hakan da kuma tasirin jiki daga gare shi ya fi girma daga tasirin magungunan jiki, sai dai kaɗai yana tasiri ne da al'amura biyu: Na farkonsu ta ɓangaren wanda illar ta sama shi ne gaskiyar nufi, ɗayan kuma ta ɓangaren mai yin maganin, shi ne ƙarfin niyya da kuma ƙarfin zuciyarsa da tsoron Allah da kuma dogara, Allah ne Mafi sani.
- Ibnu Hajar ya ce; A cikinsa akwai dalili akan halaccin barin yin magani.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 116) (5652).
صحيح مسلم (4/ 1994) (2576).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 95).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 235).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال: "إن عِظَمَ الجزاءِ مع عِظَمِ البلاءِ، وإن الله تعالى إذا أحب قوما ابتلاهم، فمن رَضِيَ فله الرِضا، ومن سَخِطَ فله السُّخْطُ".
Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi ya ce: "Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana bamu labari acikin wannan Hadisi cewa Mumini wani lokaci wani abu na masibu yakan same shi akansa ko Dukiyarsa ko waninsa, kuma cewa Allah zai bashi lada akan kowace Musiba ce ta Sameshi, Sannan ya bayyana cewa Musibu koyaushe suka zamo Manya kuma hadarin su ya girmama to ladansu yakan girmama a wajen Allah Sannan Annabi yayi bayanin cewa cewa afkuwar Musibu yana daga cikin Alamomin Son Allah ga Mumini, Kuma Hukunin Allah da Kaddararsa babu Makawa sai sun afku, sai dai kuma wanda yayi Hakuri kuma ya yarda da Kaddarar , to Allah zai saka masa kan hakan da Yardarsa kuma babu ladan da yafi wannan, kuma duk wanda ya yayi fushi kuma yaki yarda da Kaddarar Allah to Allah zai fushi da shi , kuma babu ukubar da tafi wannan.
Madogara
كتاب التوحيد للإمام محمد بن عبد الوهاب، ت: د. دغش العجمي، مكتبة أهل الأثر, الطبعة الخامسة, 1435ه.
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي, ت: محمد بن أحمد سيد, مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424ه.
الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة، الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ - 2001م.
جامع الترمذي، ت: أحمد شاكر, شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي, الطبعة: الثانية، 1395هـ.
صحيح الجامع الصغير , للألباني , المكتب الإسلامي.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ طَاوُسٍ أَنَّهُ قَالَ: أَدْرَكْتُ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُونَ كُلُّ شَيْءٍ بِقَدَرٍ، قَالَ: وَسَمِعْتُ عَبْدَ اللهِ بْنَ عُمَرَ رضي الله عنهما يَقُولُ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «كُلُّ شَيْءٍ بِقَدَرٍ، حَتَّى الْعَجْزِ وَالْكَيْسِ، أَوِ الْكَيْسِ وَالْعَجْزِ».
Daga Dawus cewa shi ya ce: Na riski wasu mutane daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna cewa kowane abu (yana kasancewa) da kaddara ne, ya ce: Na ji Abdullahi Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su, yana cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya ".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kowanne abu da kaddara ne; Har kasawa: ita ce: Barin abinda yake wajibi ne aikata shi, da cewa zai yi ta jinkirta shi daga lokacinsa, da al'amuran duniya da lahira. Har dabara ita ce: Nishadi da kwarewa da al'amuran duniya da lahira. Kuma cewa Allah - Mai girma da daukaka - hakika Ya kaddara gajiyawa da wayo da kowane abu, ba zai afku a kasantacce ba sai hakika sanin Allah Ya rigaya da shi da mashi'arSa.
Fa’idoji
- Bayanin kudircewar sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kaddara.
- Kowanne abu yana faruwa ne da kaddarawar Allah har gajiyawa da kuma nishadi.
- Ya tabbata kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su, sun tsoratar - a cikin riwayar hadisan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Yin imani da kaddara dukkaninsa alherinSa da kuma sharrinSa.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2045) (2655)، إكمال المعلم (8/143)، شرح النووي على مسلم (16/205)، الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني (1/ 122).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ مَطَرِ بْنِ عُكَامِسٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا قَضَى اللَّهُ لِعَبْدٍ أَنْ يَمُوتَ بِأَرْضٍ جَعَلَ لَهُ إِلَيْهَا حَاجَةً».
Daga Madar Dan Ukamis - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta".
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah idan Ya hukunta Ya kuma kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa alhali shi ba ya cikin kasar; sai a sanya masa wata bukata gareta sai ya tafi kasar, sai a karbi ransa a cikinta.
Fa’idoji
- Hadisin gasgatawa ne ga fadin Allah - Mai girma da daukaka -: {Kuma wata rai ba ta sanin a wacce kasa zata mutu}.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 23) (2146)، تحفة الأحوذي (6/ 299).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِعَمِّهِ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، أَشْهَدُ لَكَ بِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ»، قَالَ: لَوْلَا أَنْ تُعَيِّرَنِي قُرَيْشٌ، يَقُولُونَ: إِنَّمَا حَمَلَهُ عَلَى ذَلِكَ الْجَزَعُ لَأَقْرَرْتُ بِهَا عَيْنَكَ. فَأَنْزَلَ اللهُ: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ } [القصص: 56].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya cewa Baffansa; "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama", ya ce: Da badan Kuraishawa zasu aibatani ba, zasu ce: Razani da tsoron mutuwa ne suka kai shi haka ba da na faranta ranka da ita. Sai Allah Ya saukar: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda ka so ba saidai Allah Yana shiryar da wanda yake so} [Al-Kasas; 56].
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi:
Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.
Fa’idoji
- Ba'a barin gaskiya dan tsoro daga zancen mutane.
- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kadai yana mallakar shiriyar nuni ne da fadakarwa kawai ba shiriyar dacewa ba.
- Halaccin ziyarar kafiri mara lafiya dan kiransa zuwa ga Musulunci.
- Kwadayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - a kowane hali.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 55) (25)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (1/ 539)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 742).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: حَدَّثَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ الصَّادِقُ المَصْدُوقُ: «إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ إلَيْهِ المَلَكُ فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ، وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٍّ أَوْ سَعِيدٍ؛ فَوَالَّذِي لَا إلَهَ غَيْرُهُ إنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ فَيَدْخُلُهَا، وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ فَيَدْخُلُهَا».
Daga Abu Abdurrahman Abdullahi ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya karantar da mu alhali shi mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa: «Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana maniyyi, sannan ya zama gudan jini misalin haka, sannan ya zama gudan tsoka misalin haka, sannan a aiko masa da mala’ika sai ya busa masa rai, kuma a umarce shi da kalmomi guda huɗu: Da rubuta arziƙinsa, da ajalinsa, da aikinsa, kuma shi ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne, na rantse da wanda babu wani abin bautawa da cancanta in ba shi ba, lallai ɗayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai zira’i, sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan wuta sai ya shige ta, kuma cewa ɗayanku zai yi aiki aiki irin na 'yan wuta har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai dai zira’i sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan aljannah sai ya shige ta».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Dan Mas'ud ya ce:: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiyane a zancensa, kuma abin gasgatawa yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya gasgata shi. Ya ce: Lallai cewa dayanku ana taro halittarsa, cewa mutum idan ya zo wa iyalansa to tarwatsettsen maniyyinsa ana taroshi a cikin mace kwana arba'in yana maniyyi. Sannan ya zama gudan jini ita ce gudan jini mai kauri sandararre, wannan a arba'in ta biyu ne, Sannan ya zama gudan tsoka ita ce yanki na nama gwargwadan abinda ake taunawa, wannan a arba'in ta uku ce, Sannan sai Allah Ya aiko masa da Mala'ika, sai ya busa rai a cikinsa bayan karewar arba'in ta uku, Sai a umarci Mala'ikan da ya rubuta kalmomi hudu su ne: Arzikinsa, shi ne gwargwadan abin da zai samu daga ni'imomi a rayuwarsa, Da ajalinsa, shi ne gwargwadan wanzuwarsa a duniya, Da aikinsa, menene shi? dan wutan ne ko dan Aljanna ne. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa cewa; mutum zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna kuma aikinsa zai zama na gari, wato a abinda yake bayyana ga mutane, kuma ba zai gushe a haka ba har ya kasance tsakaninsa da ita bai zama ba sai zira'i daya, wato: Babu abinda zai wanzu tsakaninsa da tsakanin saduwa da ita aljannar sai kamar wanda zai zama tsakaninsa da tsakanin wani wuri na kasa zira'i daya ne, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa to a wannan lokacin zai yi aiki da aikin 'yan wuta sai a cika masa da shi sai ya shiga wutar; Domin cewa sharadin karbar aikinsa shi ne ya tabbata akansa ta yadda ba zai canjaba, wani dayan kuma daga mutane zai yi ayyukan 'yan wuta har sai ya kusanci shigarta, kuma gwargwadan zira'i ne na kasa zai kasance tsakakninsa da wutar, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa, sai ya yi aikin 'yan Aljanna kuma ya shiga Aljannar.
Fa’idoji
- Bayanin matakan halittar mutum.
- Yin imani da hukuncin (Allah) da kuma ƙaddara.
- Makomar al'amura a karshe zuwa ga abinda hukunci ya rigaya da shi ne, kuma kaddara ta gudana da shi.
- Gargadi akan ruduwa da yanayin ayyuka; kadai ayyuka da karshe ne kawai.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 135) (7454)، (4/ 111) (3208).
صحيح مسلم (4/ 2036) (2643).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (15/ 130).
شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 84).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي العَبَّاسِ، عَبْدِ الله بْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: كُنْت خَلْفَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: «يَا غُلَامِ! إنِّي أُعَلِّمُك كَلِمَاتٍ: احْفَظِ اللَّهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ الله تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاَللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الأُمَّةَ لَوْ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَنْفَعُوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ لَكَ، وَإِنِ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ لَمْ يَضُرُّوكَ إلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللَّهُ عَلَيْكَ؛ رُفِعَتِ الأَقْلَامُ، وَجَفَّتِ الصُّحُفُ».
وَفِي رِوَايَةِ غَيْرِ التِّرْمِذِيِّ: «احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ أَمَامَكَ، تَعَرَّفْ إلَى اللهِ فِي الرَّخَاءِ يَعْرِفْكَ فِي الشِّدَّةِ، وَاعْلَمْ أَنَّ مَا أَخْطَأَكَ لَمْ يَكُنْ لِيُصِيبَكَ، وَمَا أَصَابَك لَمْ يَكُنْ لِيُخْطِئَكَ، وَاعْلَمْ أَنَّ النَّصْرَ مَعَ الصَّبْرِ، وَأَنْ الفَرَجَ مَعَ الكَرْبِ، وَأَنَّ مَعَ العُسْرِ يُسْرًا».
Daga Abul Abbas, Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wata rana, sai ya ce: «Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka same shi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da ace al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru kuma a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka; an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe». A cikin wata riwayar da ba ta Tirmizi ba: «Ka kiyaye Allah zaka same shi a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin wadata zai taimakeka a cikin tsanani, ka sani cewa abin da ya kuskure maka bai zama zai sameka ba, abin da kuma ya sameka bai zama zai kuskure maka ba, ka sani cewa nasara tana tare da haƙuri, kuma yaye baƙin ciki yana tare da farin ciki, kuma sauƙi yana tare da tsanani».
Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai da su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, domin haƙiƙa Shi Allah Shi kaɗai ne wanda Yake amsawa masu roƙo. Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara shi a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka Ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarSa da saninSa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta shi. Kuma cewa wanda ya kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa; to Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana gaban bawa, Yana sanin abin da yake a kansa, kuma zai taimake shi Ya kuma ƙarfafe shi. Kuma lallai mutum idan ya bi Allah a cikin wadata to lallai cewa Allah zai sanya masa yayewa da mafita a lokacin tsanani, kuma kowane bawa ya yarda da abin da Allah Ya ƙaddara masa na alheri da na sharri. Kuma ya lazimci haƙuri a lokacin tsanani da kuma jarrabawa, domin haƙuri mabuɗin yaye baƙin ciki ne, kuma baƙin ciki idan ya yi tsanani sai yayewa tazo daga Allah, kuma cewa tsanani idan ya faru Allah sai Allah Ya biye masa da sauƙi.
Fa’idoji
- Muhimmancin sanar da yara al'amuran addini na tauhidi da ladubba da sauransu.
- Sakamako yana kasancewa daga irin aikin da aka yi.
- Umarni a kan dogaro ga Allah, da tawakkali gare shi ba da waninsa ba, madalla da Shi a matsayin wakili.
- Imani da hukunci da ƙaddara da yarda da shi, kuma Allah Ya ƙaddara kowane abu.
- Wanda ya tozarta umarnin Allah, to, Allah Zai tozarta shi ba kuma zai kiyaye shi ba.
- Bushara mai girma cewa mutum idan tsanani ya same shi to ya saurari sauƙi.
- lallashin bawa a lokacin faruwar musiba, da rasa abin da ake so a cikin faɗinsa: «Ka sani cewa abin da ya sameka bai zama zai kuskureka ba, abin da kuma ya kuskureka to bai zama zai sameka ba» to jumal ta farko bada haƙuri ce a lokacin faruwar wani abin ƙi, ta biyu kuma bada haƙuri a kokacin rasa abin da ake so.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 284) (2516).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص42).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص200).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص69).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com