Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bawa idan ya mutu za'a bijiro masa da masaukinsa da gurinsa na musamman a cikin aljanna ko wuta, a farkon yini da ƙarshensa; wurinsa a aljanna idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna, da kuma wurinsa a wuta idan ya kasance daga cikin 'yan wuta ne, kuma za’a ce masa: Wadannan wuraran ne wadanda za'a tasheka zuwa gare su ranar alƙiyama; a cikin hakan akwai ni'imtarwa ga mumini, da kuma azabtarwa ga kafiri.
- Azabar ƙabari da ni'imarsa gaskiya ne.
- Ibnu Hajar ya ce: Lallai wannan bijirowar ga mumini mai tsoron Allah da kuma kafiri zahiri ne, amma mumini wanda ya cakuɗa ayyukansa sai a ɗauka akan cewa za'a bijiro masa da mazauninsa na aljannar da zai tafi zuwa gareta.
صحيح البخاري (2/ 99-100) (1379). صحيح مسلم (4/ 2199) (2866). عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لبدرالدين العيني (8/ 209). التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد الصنعاني (2/ 209). الإفصاح عن معاني الصحاح، ليحيى بن هبيرة (4/ 131).