Asma'u tana bada labarin cewa Manzon Allah SAW ya yi Wa'azin fitintinu waxanda Mutum zai gamu da su a cikin Qabarinsa,da tsoronsa, kuma ya faxi Fitinar Qabari, kuma abunda ake nufi da ita shi ne tamabayar Mala'iku biyu Munkarun da Nakiri, zasu tambayi bawa game da Ubangijinsa da Annabinsa da Addininsa, kuma ya faxi wannan fitina ce Maigirma, kuma duk wanda ya dace a wannan to ya rabauta, kuma duk wanda ya kasa to ya halaka, yayin da ya faxi haka sai Musulmai sai sukai kuwwa da ta hanani na fahimci abunda manzon Allah SAW yake nufi, yayin da kururuwar ta su ta ragu sai nace da wani Mutum da yake kusa da ni: Mai Manzon Allah yace Allah yayi maka Al-barka a qarshen maganarsa? sai ya ce: Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal, Saboda Fitinar Duja Mai tsanani ce kuma mai wuya haka ma Azabar Qabari.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. المجتبى من السنن (السنن الصغرى)، أحمد بن شعيب النسائي، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، مكتب المطبوعات الإسلامية، حلب، الطبعة: الثانية 1406هـ، 1986م. منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، حمزة محمد قاسم، راجعه: عبد القادر الأرناؤوط، عني بتصحيحه ونشره: بشير محمد عيون، الناشر: مكتبة دار البيان، دمشق، مكتبة المؤيد، الطائف، عام النشر: 1410هـ، 1990م. شرح سنن النسائي المسمى «ذخيرة العقبى في شرح المجتبى»، محمد بن علي الإثيوبي الوَلَّوِي، الناشر: دار المعراج الدولية للنشر، دار آل بروم للنشر والتوزيع، الطبعة الأولى.