Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.
Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.
Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.
Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.
Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 48) (17).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 681).
تطرز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص414).
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (1/ 189).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com