Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

TAFSIRIN AYOYI

Hadisai 10

Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا، فَإِذَا طَلَعَتْ فَرَآهَا النَّاسُ آمَنُوا أَجْمَعُونَ، فَذَلِكَ حِينَ: {لاَ يَنْفَعُ نَفْسًا إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آمَنَتْ مِنْ قَبْلُ، أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْرًا} [الأنعام: 158] وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ نَشَرَ الرَّجُلاَنِ ثَوْبَهُمَا بَيْنَهُمَا فَلاَ يَتَبَايَعَانِهِ، وَلاَ يَطْوِيَانِهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدِ انْصَرَفَ الرَّجُلُ بِلَبَنِ لِقْحَتِهِ فَلاَ يَطْعَمُهُ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَهُوَ يَلِيطُ حَوْضَهُ فَلاَ يَسْقِي فِيهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ رَفَعَ أَحَدُكُمْ أُكْلَتَهُ إِلَى فِيهِ فَلاَ يَطْعَمُهَا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu, wannan yayin da: {Wani rai imanin sa ba zai anfane shi ba, bai yi imani ba kafin nan, ko bai aikata alheri a imanin na sa ba} [Al-An'am: 158] kuma lalli Alkiyama za ta tsaya alhali mutum biyu za su shinfida tufafinsu a tsakaninsu ba za su saida shi ba, ba kuma za su ninkeshi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali hakika mutum ya juya da nonon taguwarsa da ta tatsa ba zai dandane shi ba, lallai Alkiyama za ta tsaya alhali shi yana yabe tafkinsa ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tsaya alhali hakika dayanku ya daga lomarsa zuwa bakinsa ba zai cinyeta ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama manya; shi ne bullowar rana daga yamma maimakon daga gabas, lokacin da mutane suka ganta za su yi imani gaba daya, A wannan lokacin imanin kafiri ba zai anfanar da shi ba, kuma aiki na gari ba zai yi amfani ba haka kuma tuba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama zata zo kwatsam; har cewa ita zata tashi alhali mutane suna cikin harkokin su da kuma sha'aninninkan rayuwarsu; Sai Alkiyama ta tashi alhali mai siyarwa da mai saya sun shimfida tufafinsu a tsakakninsu, amma ba za su saida su ba, ba kuma za su ninke su ba. Kuma Alkiyama zata tashi alhali hakika mutum ya dauki nonon taguwarsa mai yawan nono amma ba zai sha shi ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum yana gyara tafkinsa yana tsaftace shi amma ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum ya daga lomarsa zuwa bakinsa dan ya ci amma ba zai ci ba.

Fa’idoji
  1. Musulunci da tuba ana karbar su matukar rana ba ta bullo ta mafadarta ba.
  2. Kwadaitarwa akan tanadi dan Alkiyama da aiki na gari; domin Alkiyama za ta zo ne kwatsam..
Madogara

صحيح البخاري (8/ 106) (6506)، صحيح مسلم (1/ 137) (157)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (23/ 92).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يُؤْتَى بِالْمَوْتِ كَهَيْئَةِ كَبْشٍ أَمْلَحَ، فَيُنَادِي مُنَادٍ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، ثُمَّ يُنَادِي: يَا أَهْلَ النَّارِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: وهَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، فَيُذْبَحُ ثُمَّ يَقُولُ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، وَيَا أَهْلَ النَّارِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، ثُمَّ قَرَأَ: {وَأَنْذِرْهُمْ يَوْمَ الحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ} [مريم: 39]، وَهَؤُلاَءِ فِي غَفْلَةٍ أَهْلُ الدُّنْيَا {وَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ} [مريم: 39]».
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa Za’a zo da mutuwa ranar Alkiyama, kamar siffar namijin tinkiya a jikinsa akwai fari da baki, Sai a yi kira: Ya ku 'yan Aljanna! sai su dago wuyan su da kawunansu suna dubawa. Sai ya ce da su: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun ganta sun kuma santa, Sannan mai kira ya yi kira: Ya ku 'yan wuta, sai su dago wuyansu su dago kawunansu suna dubawa. Sai ya ce: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun gan ta. Sai a yankata, sannan mai kira ya ce: Ya ku 'yan Aljanna wanzuwa har abada babu mutuwa,m. Ya ku 'yan wuta wanzuwa har abada babu mutuwa. Wannan dan ya zama kari a cikin ni'imar muminai, da masifa a cikin azabar kafirai. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin rafkana, kuma ba su yin imani ba.} Ranar Alkiyama za'a rabe tsakanin 'yan Aljanna da 'yan wuta, kuma kowanne zai shiga inda zai dawwama a cikinsa. Sai mai munanawa ya yi nadama dan bai kyautata ba, mai takaitawa kuma dan bai kara alheri ba.

Fa’idoji
  1. Makomar mutum a lahira ita ce dawwama a cikin Aljanna ko a wuta.
  2. Gargadi mai tsanani daga tsoron Alkiyama kuma cewa ita ce ranar da na sani.
  3. Bayanin dawwamar farin cikin 'yan Aljanna, da kuma dawwamar bakin cikin 'yan wuta.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 93) (4730)، صحيح مسلم (4/ 2188) (2849)، التوضيح شرح الجامع الصحيح (22/595)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (19/ 52)، البحر المحيط الثجاج (43/686).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne

عَنْ ‌عَدِيِّ بْنِ حَاتِمٍ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الْيَهُودُ مَغْضُوبٌ عَلَيْهِمْ، وَالنَّصَارَى ضُلَّالٌ».
Daga Adi Dan Hatim daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne".
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Yahudawa wasu mutanene da aka yi fushi da su; domin cewa su sun san gaskiya amma ba su aiki da ita. Kiristoci kuwa wasu mutanene ne batattu; domin cewa su sun yi aiki ba tare da ilimi ba.

Fa’idoji
  1. Hadawa tsakanin ilimi da aiki da shi, tsira ne daga tafarkin wadanda aka yi fushi da su da kuma batattu.
  2. Tsoratarwa akan tafarkin Yahudawa da Kiristoci, da lazimtar hanya madaidaiciya wacce ita ce Musulunci.
  3. Kowanne daga Yahudawa da Kiristoci batattune an yi fushi da su, saidai mafi kebantar siffofin Yahudawa ita ce fushi, kuma mafi kebantar siffofin Kiristoci ita ce bata.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 71) (2954)، النهاية في غريب الحديث و الأثر ( ص 548)، المنهل العذب المورود (5/250)، البحر المحيط الثجاج (9/248).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu

عَنْ ‌عَائِشَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ: تَلَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَذِهِ الْآيَةَ: {هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ، وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ، وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو الْأَلْبَابِ} [آل عمران: 7]. قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَإِذَا رَأَيْتِ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ فَأُولَئِكَ الَّذِينَ سَمَّى اللهُ، فَاحْذَرُوهُمْ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar:{Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda ya yi kama da juna daga gare shi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda ya san tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne Ba mai tunani sai ma'abota hankalu}. a cikin wannan ayar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -Ya bada labari cewa Shi ne wanda Ya saukar da Alkur’ani ga AnnabinSa, wanda daga cikinsa akwai wasu ayoyi masu bayyananar nuni, hukunce-hukuncensu sanannu ne babu rikici a cikinsu, su ne asalin littafi kuma makomarsa, su ne makoma yayin sabani, daga cikinsa akwai wasu ayoyin daban masu daukar sama da ma'ana, ma'anarsu tana rikitarwa ga wasu daga mutane, ko ya zaci cewa tsakakninsu da wata ayar akwai karo, sannan Allah Ya bayyana mu'amalar mutane tare da wadannan ayoyin. wadanda a cikin zukatansu akwai karkata daga gaskiya sai su bar bayyayanannu, su yi riko da masu kama da juna masu daukar ma'anoni sama da daya, suna neman tayar da rikici ta hakan da batar da mutane, kuma suna neman tawilinsu akan abinda ya dace da son ransu, amma matabbata a cikin ilimi to cewa su suna sanin wadannan masu kama da junan, suna dawo da shi ga bayyananne, kuma suna yin imani da shi kuma cewa shi daga gurin Allah yake - Madaukakin sarki -, ba zai yiwu ya rikitar ba ko ya yi karo da juna, saidai ba mai tunanin hakan sai mai wa'azantuwa ma'abota hankula lafiyayyu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa Uwar Muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa ita idan ta ga wadanda suke neman masu kama da juna to cewa su ne wadanda Allah Ya ambace su a cikin fadinSa; {Amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata} to ku gujesu kada ku karkata zuwa gare su.

Fa’idoji
  1. Bayyanannu daga ayoyin Alkur’ani ; Su ne wadanda nuninsu ya bayyana kuma ma'anarsu ta bayyana. Mai kama da juna kuma: Wanda ya dauki sama da ma'ana daya kuma ya bukatu zuwa duba da fahimta.
  2. Gargadarwa daga cakuduwa da ma'abota karkata da 'yan bidi'a da wanda yake jefa mushkiloli dan batar da mutane da sa su kokwanto.
  3. A karshen ayar da fadinSa - Madaukakin sarki -: {Ba mai tunani sai ma'abota hankula} jirwaye mai kama da wanka ga karkatattu, da yabo ga matabbata a ilimi, yana nufin: Wanda bai yi tinaniba bai wa'azantuba, kuma ya bi son ransa to ba ya daga ma'abota hankula.
  4. Bin masu kamanceceniya da juna sababine ga karkatar zuciya.
  5. Wajabcin dawo da ayoyi masu kamanceceniya da juna wadanda ba'a fahimtar ma'anarsu zuwa ga ayoyi bayyanannu.
  6. Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya sanya sashin Alkur’ani bayyananne, da wani sashinsa kuma mai kama da juna; dan jarraba mutane dan kuma ma'abota imani su ware daga ma'abota bata.
  7. A cikin afkuwar mai kama da juna a cikn Alkur’ani: Bayyanar da falalar malamai akan wasunsu, da sanarwar takaituwar hankula; dan su mika wuya ga Mahaliccinsu su yi ikirari da gajiyawarsu.
  8. Falalar tabbata a cikin ilimi da wajibcin tabbata a cikinsa.
  9. A hukuncin tsayawa akan {Allah} daga fadinSa: {Kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah da matabbata a cikin ilimi} a kwai maganganu biyu na masu tafsiri: Wanda ya tsaya akan {Allah}, sai ya zama abin nufi da tawili shi ne sanin hakikanin abu da yadda yake da abinda babu wata hanya zuwa riskarsa kamar al'amarin rai da Alkiyama wadanda Allah ne Ya kebantu da saninsa, matabbata a cikin ilimi suna imani da shi suna fawwala hakikaninsa zuwa ga Allah, sai su mika wuya su kubuta. Wanda kuma ya zarce (a karatu) bai tsaya a {Allah} ba, sai abin nufi da tawili ya zama fassara da bayyanarwa, sai Allah Ya zama Ya san shi matabbata a cikin ilimi suma sun san shi , sai su yi imani da su kuma su dawo da su ga bayyananne.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 33) (4547)، صحيح مسلم (4/ 2053) (2665)، فتح الباري (8/211)، شرح النووي على مسلم (16/217)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 407، 465)، فتح الودود في شرح سنن أبي داود (4/415)، تحفة الأبرار شرح مصابيح السنّة (1/129)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (41/ 559).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu

عَنْ ‌عَائِشَةَ رضي الله عنها: أَنَّ رَجُلًا قَعَدَ بَيْنَ يَدَيِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ لِي مَمْلُوكِينَ يَكْذِبُونَنِي وَيَخُونُونَنِي وَيَعْصُونَنِي، وَأَشْتُمُهُمْ وَأَضْرِبُهُمْ، فَكَيْفَ أَنَا مِنْهُمْ؟ قَالَ: «يُحْسَبُ مَا خَانُوكَ وَعَصَوْكَ وَكَذَّبُوكَ وَعِقَابُكَ إِيَّاهُمْ، فَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ بِقَدْرِ ذُنُوبِهِمْ كَانَ كَفَافًا، لَا لَكَ وَلَا عَلَيْكَ، وَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ دُونَ ذُنُوبِهِمْ كَانَ فَضْلًا لَكَ، وَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ فَوْقَ ذُنُوبِهِمُ اقْتُصَّ لَهُمْ مِنْكَ الْفَضْلُ»، قَالَ: فَتَنَحَّى الرَّجُلُ فَجَعَلَ يَبْكِي وَيَهْتِفُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَمَا تَقْرَأُ كِتَابَ اللهِ: {وَنَضَعُ الْمَوَازِينَ الْقِسْطَ لِيَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْئًا}، الْآيَةَ»، فَقَالَ الرَّجُلُ: وَاللهِ يَا رَسُولَ اللهِ، مَا أَجِدُ لِي وَلهُمْ شَيْئًا خَيْرًا مِنْ مُفَارَقَتِهِمْ، أُشْهِدُكَ أَنَّهُمْ أَحْرَارٌ كُلُّهُمْ.
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaMai Rauni ne
Sharhi

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana karar halin bayinsa, cewa su suna yi masa karya a labari, suna ha'intarsa a amana, suna yin algus a mu'amala, suna saba masa a al'amari, shi kuma yana zaginsu yana dukansu dan ladabtar da su, sai ya tambaye shi game da halinsa ranar Alkiyama tare da su? sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Za'a lissafa abinda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, kuma za'a lissafta ukubarka garesu, idan gwargwadan ukubar ta yi daidai da laifukansu to ba ka da komai, kuma babu komai a kanka, idan kuma gwargwadan ukubarka garesu kasa da laifukansu ne, ya zama falala da kari gareka a lada, idan ukubarka garesu sama da laifukansu ne za’a yi maka ukuba, za'a karbi gwargwadan karin daga gareka za'a ba su, sai mutumin yadan yi nisa ya fara kuka muryarsa tana sama, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce masa: Shin ba ka karanta littafin Allah ba; {zamu sanya ma'auni na adalci ga ranar Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abuba, idan ya kasance kwatankwacin kwayar komayya ne zamu zo da ita, mun isa zama masu hisabi] [Al-Anbiya;47], ba za’a zalinci wani mutum wani abu ba ranar Alkiyama, kuma ma'aunai za su zama a tsakanin mutane da adalci, sai mutumin ya ce: Wallahi ya manzon Allah, ban ji komai game da ni da su ba sama da na rabu dasu da barinsu, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne sabo da Allah gaba dayansu; dan tsoron hisabi da azaba.

Fa’idoji
  1. Gaskiyar sahabi a 'yan tawarsa ga bayinsa dan tsoron azabar Allah.
  2. Sakayya daga azzalimi in ya kasance daidai da gwargwadan zalinci ko kasa daga gare shi to shi halal ne, amma kari to haramun ne.
  3. Kwadaitarwa akan kyakkyawar mu’amalantar masu hidima da raunana.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 227) (3165)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 804)، مرقاة المفاتيح (8/3533)، تحفة الأحوذي (9/3).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata

عَنِ ‌ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا: أَنَّ نَاسًا مِنْ أَهْلِ الشِّرْكِ، كَانُوا قَدْ قَتَلُوا وَأَكْثَرُوا، وَزَنَوْا وَأَكْثَرُوا، فَأَتَوْا مُحَمَّدًا صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالُوا: إِنَّ الَّذِي تَقُولُ وَتَدْعُو إِلَيْهِ لَحَسَنٌ، لَوْ تُخْبِرُنَا أَنَّ لِمَا عَمِلْنَا كَفَّارَةً، فَنَزَلَ {وَالَّذِينَ لا يَدْعُونَ مَعَ اللهِ إِلَهًا آخَرَ وَلا يَقْتُلُونَ النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللهُ إِلا بِالْحَقِّ وَلا يَزْنُونَ}[الفرقان: 68]، وَنَزَلَت: {قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَى أَنْفُسِهِمْ لا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللهِ} [الزمر: 53].
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo wa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai suka ce: Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata, sai (faɗin Allah) ya sauka: {Waɗanda ba sa kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba sa kashe rai wanda Allah Ya haramta face da haƙƙi, kuma ba sa yin zina} [Al-Furqan: 68], kuma (wannan ayar) ta sauka: {Kace: (Allah Ya ce), "Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukanku! kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah} [Al-Zumar: 53].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu mutane daga mushrikai sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun kasance haƙiƙa sun yawaita kisa da zina, sai suka cewa Annabi: Lallai abin da kake kira zuwa gareshi na musulunci da koyarwarsa abu ne mai kyau, sai dai halimmu da abin da muka afka a cikinsa na shirka da manyan zunubai, shin akwai kaffara a ciki? Sai ayoyi biyu suka sauka: Yayin da Allah Ya karɓi tuba daga mutane tare da yawan zunubansu da girmansu, da ba don haka ba, da sun zarce a kan kafircinsu da shisshiginsu da kuma ba su shiga wannan addinin ba.

Fa’idoji
  1. Falalar musulunci da girmansa kuma cewa shi yana rusa abin da ya gabata na zunubai.
  2. Yalwar rahamar Allah ga bayinSa da gafararSa da rangwaminSa.
  3. Haramcin shirka, da haramcin kashe rai ba tare da wani haƙƙi ba, da haramcin zina, da narko a kan wanda ya aikata waɗannan zunuban.
  4. Tuba na gaskiya abin wanda ya hadu da ikhlasi da aiki na gari yana kankare dukkanin manyan zunubai har ma da kafircewa Allah - Maɗaukakin sarki -.
  5. Haramcin yanke ƙauna daga rahamar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 125) (4810)، صحيح مسلم (1/ 113) (122)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (7/ 319)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 808).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su

عَنِ ‌ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَطَبَ النَّاسَ يَوْمَ فَتْحِ مَكَّةَ، فَقَالَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ اللهَ قَدْ أَذْهَبَ عَنْكُمْ عُبِّيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ وَتَعَاظُمَهَا بِآبَائِهَا، فَالنَّاسُ رَجُلَانِ: بَرٌّ تَقِيٌّ كَرِيمٌ عَلَى اللهِ، وَفَاجِرٌ شَقِيٌّ هَيِّنٌ عَلَى اللهِ، وَالنَّاسُ بَنُو آدَمَ، وَخَلَقَ اللهُ آدَمَ مِنْ تُرَابٍ، قَالَ اللهُ: {يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ} [الحجرات: 13]».
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya ɗauke kuma ya gusar muku da girman kan Jahiliyya, da jiji da kanta, da alfahari da iyaye, kawai dai mutane sun rabu gida biyu: Ko dai mumini mutumin kirki mai tsoron Allah mai biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to, wannan mai girma ne a wajen Allah, ko da bai zama mai wani matsayi ko nasaba a wurin mutane ba. Ko kafiri fajiri taɓaɓɓe, to, wannan wulaƙantacce ne ƙasƙantacce a wurin Allah, kuma bai yi daidai da komai ba, ko da ya zama mai matsayi kuma yana da alfarma da mulki. Mutane dukkaninsu 'ya'yan Adam ne, kuma Allah Ya halicci Adam daga turɓaya, ba ya dacewa ga wanda asalinsa daga turɓaya ne ya yi girman kai ya yi jiji da kai, gasgata hakan shi ne faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Ya ku mutane lallai Mu Mun halicceku daga namiji da mace, kuma mun sanyaku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku ga Allah, lallai Allah Masani ne Mai ba da labari} [Al-Hujurat: 13].

Fa’idoji
  1. Hani daga alfahari da dangantaka da kuma matsayi.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 309) (3270)، صحيح ابن حبان (9/ 137) (3828)، عون المعبود وحاشية ابن القيم (14/ 16)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص587).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}

عَنْ ‌الزُّبَيْرِ بْنِ الْعَوَّامِ قَالَ: لَمَّا نَزَلَتْ: {ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ} [التكاثر: 8]، قَالَ الزُّبَيْرُ: يَا رَسُولَ اللهِ، وَأَيُّ النَّعِيمِ نُسْأَلُ عَنْهُ، وَإِنَّمَا هُمَا الْأَسْوَدَانِ التَّمْرُ وَالْمَاءُ؟ قَالَ: «أَمَا إِنَّهُ سَيَكُونُ».
Daga Zubairu ɗan Awwam ya ce: Yayin da (aya) ta sauka {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Fa’idoji
  1. Ƙarfafawa a kan godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a kan ni'ima.
  2. Ni'ima tana daga abin da za a yi tambaya game da ita a ranar Alƙiyama kaɗan ce ko mai yawa.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 375) (3356)، سنن ابن ماجه (5/ 262) (4158)، شرح سنن ابن ماجه للسيوطي (ص: 307)، تحفة الأحوذي (9/203)، مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (25/ 251).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 10
Hadisai 10
  1. Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu
  2. Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki
  3. Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne
  4. Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu
  5. Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu
  6. Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata
  7. Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su
  8. {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}
  9. a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa
  10. Mabuɗan gaibu biyar ne

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com