Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

{Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima}

عَنْ ‌الزُّبَيْرِ بْنِ الْعَوَّامِ قَالَ: لَمَّا نَزَلَتْ: {ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ} [التكاثر: 8]، قَالَ الزُّبَيْرُ: يَا رَسُولَ اللهِ، وَأَيُّ النَّعِيمِ نُسْأَلُ عَنْهُ، وَإِنَّمَا هُمَا الْأَسْوَدَانِ التَّمْرُ وَالْمَاءُ؟ قَالَ: «أَمَا إِنَّهُ سَيَكُونُ».
Daga Zubairu ɗan Awwam ya ce: Yayin da (aya) ta sauka {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Fa’idoji
  1. Ƙarfafawa a kan godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a kan ni'ima.
  2. Ni'ima tana daga abin da za a yi tambaya game da ita a ranar Alƙiyama kaɗan ce ko mai yawa.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 375) (3356)، سنن ابن ماجه (5/ 262) (4158)، شرح سنن ابن ماجه للسيوطي (ص: 307)، تحفة الأحوذي (9/203)، مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (25/ 251).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
RAYUWAR LAHIRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com