Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu

عَن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا بَالُ أَقْوَامٍ يَرْفَعُونَ أَبْصَارَهُمْ إِلَى السَّمَاءِ فِي صَلاَتِهِمْ»، فَاشْتَدَّ قَوْلُهُ فِي ذَلِكَ، حَتَّى قَالَ: «لَيَنْتَهُنَّ عَنْ ذَلِكَ أَوْ لَتُخْطَفَنَّ أَبْصَارُهُمْ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi waɗanda suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallah a lokacin addu'a ko waninta, sannan tsawatarwarsa ta yi tsanani da narkonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wanda ya aikata haka da cewa shi yana jin tsoro akan idanuwansu kada a fauce musu su a karɓesu da gaggawa ta inda basa ji sai kawai ga shi sun rasa n'imar gani.

Fa’idoji
  1. Kyakkyawan tsarin Da'awar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da bayanin gaskiya; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bayyana wanda ya saɓa ba; domin abin nufi shi ne bayanin gaskiya alhali kuwa ta tabbata; domin kuma a cikinsa akwai suturtawa ga mai saɓawa kuma ya fi sa a karɓa.
  2. Hani mai ƙarfi, da narko mai tsanani akan wanda ya ɗaga ganinsa zuwa sama a cikin sallah.
  3. Ya faɗa a cikin Aunil Ma'abud: Illa a cikin hakan cewa shi idan ya ɗaga ganinsa zuwa sama to ya fita daga saitin alƙibla kuma ya bijire mata dama siffar sallar.
  4. Ɗaga ido zuwa sama yana kore Khushu'i a cikin sallah.
  5. Girman sha'anin sallah, kuma yana wajaba akan mai sallah ya kasance a cikinta akan cikar ladabi tare da Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 150) (750). كشاف القناع عن متن الإقناع، لمنصور بن يونس البهوتي (2/ 404). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 101). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 587). منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة قاسم (2/ 159).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KURAKUREN MASU SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com