عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَدْخُلُ الْخَلَاءَ، فَأَحْمِلُ أَنَا وَغُلَامٌ نَحْوِي إِدَاوَةً مِنْ مَاءٍ وَعَنَزَةً فَيَسْتَنْجِي بِالْمَاءِ.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana shiga bayan gida, sai ni da wani yaro sa'ana mu ɗaukar masa salka ta ruwa da kuma sanda sai ya yi tsarki da ruwa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya kasance da wani mai yin hidima sa'ansa a shekaru suna bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya fita dan biyan buƙatarsa, suna ɗaukar masa sanda mai kai irin kan goron mashi dan ya sanyata kariya da zai rataya wani abu a kanta yana mai suturtawa ko kuma sutura ga sallarsa, kuma suna ɗaukar masa ƙaramar ƙwarya na fata wacce take a cike da ruwa, idan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gama biyan buƙatarsa sai ɗaya daga cikinsu ya ba shi ƙwaryar, sai ya yi tsarki da ruwa.
Fa’idoji
- Musulmi ya yi tanadin ruwan tsarki a lokacin biyan buƙata; dan kada ya buƙatar da shi zuwa tashi sai ya ɓata jikinsa.
- Kiyaye al'aura a lokacin biyan buƙata dan kada wani ya ganta; domin kallon al'aura haramun ne, ya kasance yana kafa sanda a ƙasa kuma yana shinfiɗa tufa mai suturtawa a kanta.
- Koyar da yara ladubban Musulunci da kuma tarbiyantar da su akanta; dan su gaje su (su saba da su).
Madogara
صحيح البخاري (1/ 42) (152).
صحيح مسلم (1/ 227) (271).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص40).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 43).
الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص84).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: «جاء أعرابِيُّ، فبَالَ في طَائِفَة المَسجد، فَزَجَرَه النَّاسُ، فَنَهَاهُمُ النبِيُّ صلى الله عليه وسلم فَلمَّا قَضَى بَولَه أَمر النبي صلى الله عليه وسلم بِذَنُوب من ماء، فَأُهرِيقَ عليه».
Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- an daga hadisin zuwa ga Annabi: Wani balaraben kauye ya zo ya yi fitsari a wani bangare na masallaci,sai mutane suka kyare shi, sai Annabi ya hana su -tsira da aminci su tabbata a gare shi- bayan ya gama fitsarin sai Annabi tsira da amaincin Allah ya yi umarni da a zo da cikakken guga na ruwa, sai aka kwara akai
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Yana daga al'adar larabawan kauye, kausasawa da wauta, saboda nisansu da abin da Allah ya saukar ga Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.Wata rana Annabi tsira da amincin Allah ya kasance tare da sahabbansa a cikin masallacin Annabi, sai wani balaraben kauye ya zo ya yi fitsari a wani bangaren masallacin Annabi, tsammaninsa massallaci kamar fikli ne, sai abin ya ba sahabbai mamaki ba don komai ba sabo da girman alfarmar masallacin, sai suka tsawatar masa lokacin da yake fitsarin. sai dai Annabi maabocin kyawawan dabi'u, wanda aka aiko da bushara da sauki ya hana su, sabio da saninsa da halayen larabawan kauye, kumadon kar ya bata gurare masu yawa a cikin masallacin, kuma don kada ya cutu idan aka yanke masa fitsarin, kuma yin hakan zai sa yafi karbar nasihar da koyarwar Manzo, don haka ya umarce su da su tsarkake gurin ta hanyar kwara ruwa cikin guga a wajen
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه: أَنَّهُ لَقِيَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي طَرِيقٍ مِنْ طُرُقِ الْمَدِينَةِ وَهُوَ جُنُبٌ، فَانْسَلَّ فَذَهَبَ فَاغْتَسَلَ، فَتَفَقَّدَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمَّا جَاءَهُ قَالَ: «أَيْنَ كُنْتَ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ؟» قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، لَقِيتَنِي وَأَنَا جُنُبٌ فَكَرِهْتُ أَنْ أُجَالِسَكَ حَتَّى أَغْتَسِلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سُبْحَانَ اللهِ، إِنَّ الْمُؤْمِنَ لَا يَنْجُسُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - a sashin hanyoyin Madina, Abu Huraira ya kasance yana da janaba, kuma yana daga cikin girmamawarsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ƙyamaci zama da shi da kuma hira da shi alhali shi yana kan wannan halin dan yana zatan cewa shi najasa ne, sai ya tafi a ɓoye ya yi wanka, sannan ya dawo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye shi ina ya tafi? Sai ya sanar da shi halin da yake ciki, kuma cewa shi ya ƙyamaci zama da shi ne alhali shi yana najasa saboda janabar (da ta same shi), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mamaki kuma ya ce masa: Lallai cewa mumini mai tsarki ne ba ya zama najasa akan kowane hali; a raye ko a mace.
Fa’idoji
- Janaba kawai tana hana sallah ne da taɓa Alƙur'ani da kuma zama a cikin masallaci, amma bata hana zama tare da musulmai da kuma fuskantarsu, kuma mai janaba ba ya zama najasa saboda ita.
- Tsarkakar mumini a raye ko a mace.
- Girmama ma'abota falala, da ilimi, da salaha, da kuma zama da su akan yanayi mai kyau.
- Halaccin neman izinin mai bi ga wanda ake bi idan zai tafi, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - inkarin tafiyarsa ba tare da saninsa ba, hakan domin cewa neman izini yana daga cikin kyakkyawan ladabi.
- Faɗin: Subhanal Lahi, a lokacin yin mamaki.
- Halaccin zantar da mutum game da kansa da abinda ake jin kunya daga gare shi dan maslaha.
- Kafiri najasa ne, sai dai najasarsa ta ma'ana ce dan munin aƙidarsa.
- Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin akwai ladubba cewa malami idan ya ga daga wanda yake binsa wani al'amarin da yake jin tsoro a kansa wanda a cikinsa akwai saɓanin daidai to ya tambaye shi, kuma ya faɗa masa daidai, ya kuma bayyana masa hukuncinsa. Allah ne Mafi sani.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 65) (285).
صحيح مسلم (1/ 282) (371).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 46).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص61).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 74).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي أَيُّوبَ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا أَتَيْتُمُ الغَائِطَ فَلاَ تَسْتَقْبِلُوا القِبْلَةَ، وَلاَ تَسْتَدْبِرُوهَا وَلَكِنْ شَرِّقُوا أَوْ غَرِّبُوا» قَالَ أَبُو أَيُّوبَ: فَقَدِمْنَا الشَّأْمَ فَوَجَدْنَا مَرَاحِيضَ بُنِيَتْ قِبَلَ القِبْلَةِ فَنَنْحَرِفُ، وَنَسْتَغْفِرُ اللَّهَ تَعَالَى.
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi nufin biyan buƙatarsa na fitsarine ko bayan gida ya fuskanci alƙibla wajen Ka'aba, kuma kada ya juya mata baya, ya sanyata a bayansa; kai ya wajaba akansa ne ya juya ɓangaren gabas ko yamma idan alƙiblarsa kamar alƙiblar mutanen Madina ce. Sannan Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su lokacin da suka je Sham sun samu banɗakunan da aka tanada dan biyan buƙata a cikinsu an gina su suna fuskantar Ka'aba, sun kasance suna juyawa alƙibla baya da jikkunasu, tare da hakan suna neman gafarar Allah.
Fa’idoji
- Hikima a hakan shi ne girmama Ka'aba maɗaukakiya da ganin alfarmarta.
- Neman gafara bayan fitowa daga gurin biyan buƙata.
- Kyakkyawan koyarwar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi lokacin da ya ambaci wanda aka hana sai ya shiryar zuwa ga wanda ya halatta.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 88) (394).
صحيح مسلم (1/ 224) (264).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص37).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 39).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: إِنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «إِذَا شَرِبَ الْكَلْبُ فِي إِنَاءِ أَحَدِكُمْ فَلْيَغْسِلْهُ سَبْعًا».
ولمسلم: « أولاهُنَّ بالتُراب».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai". A riwayar Muslim: "Na farkonsu da turbaya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da wanke kwarya sau bakwai idan kare ya shigar da harshensa a cikinta, na farko daga cikinsu a haɗa da turbaya sai ruwa ya biyo bayanta, sai cikakkiyar tsafta ta tabbata daga najasarsa da kuma cutarsa.
Fa’idoji
- Yawun kare najasa ne najasa mai kauri.
- Lallagin kare a cikin kwarya yana maida ita mai najasa, kuma yana najasantar da ruwan dake cikinta.
- Tsarkakewa da turbaya da maimaitawa sau bakwai ya kebanci tsarkakewa ne daga lallaginsa banda fitsarinsa da bayan gidansa, da ragowar abinda kare ya bata shi .
- Yadda wanke kwarya da turbaya: A sanya ruwa a cikin kwarya sai a zuba turbaya (kasa) a ciki, sannan a wanke kwarya da wannan cuɗaɗɗen.
- Zahirin Hadisin mai gamewa ne a dukkanin karnuka, har karnukan da shari’a ta bada iznin a dauke su, misalin karnukan farauta da na gadi da na kiwo.
- Sabulu da makilin ba sa tsayawa a matsayin turbaya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nassanta turbaya ne.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 45) (172).
صحيح مسلم (1/ 234) (279).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 14).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص24).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ رَجُلًا مَذَّاءً وَكُنْتُ أَسْتَحْيِي أَنْ أَسْأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمَكَانِ ابْنَتِهِ فَأَمَرْتُ الْمِقْدَادَ بْنَ الْأَسْوَدِ فَسَأَلَهُ فَقَالَ: «يَغْسِلُ ذَكَرَهُ وَيَتَوَضَّأُ».
وَلِلبُخَاريِّ: فَقَالَ: «تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ».
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda matsayin 'yarsa sai na umarci Mikdad Dan Aswad sai ya tambaye shi sai ya ce: "Ya wanke gabansa ya yi alwala". Ga Bukhari: Sai ya ce: "Ka yi alwala ka wanke gabanka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.
Fa’idoji
- Falalar Aliu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, yadda kunya ba ta hana shi barin tambayaba ta hanyar (wani).
- Halaccin wakilci a neman fatawa.
- Halaccin mutum ya baiwa wani labarin abinda yake jin kunyar shi domin wata maslaha.
- Najasar maziyyi, da wajabcin wanke shi daga jiki da tufafi.
- Fitar maziyyi yana daga abubuwa masu bata alwala.
- Wajabcin wanke gaba da maraina dan zuwansa a wani hadisin daban.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 62) (269).
صحيح مسلم (1/ 247) (303).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 39).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص53).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص29).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أُمِّ قَيْسٍ بِنْتِ مِحْصَنٍ رَضيَ اللهُ عنها: أَنَّهَا أَتَتْ بِابْنٍ لَهَا صَغِيرٍ لَمْ يَأْكُلِ الطَّعَامَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَجْلَسَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجْرِهِ، فَبَالَ عَلَى ثَوْبِهِ، فَدَعَا بِمَاءٍ، فَنَضَحَهُ وَلَمْ يَغْسِلْهُ.
Daga Ummu Kais Bint Mihsan -Allah Ya yarda da ita -: Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ummu Kais bintu Mihsan - Allah Ya yarda da shi - ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani ɗanta wanda bai fara cin abinci ba saboda ƙanƙantar shekarunsa, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai yaron ya yi fitsari akan tufafinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan akan tufafinsa bai wanke tufafin ba.
Fa’idoji
- Kyawawan Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabata agare shi - mai girma, da kuma tawali'unsa mai yawa.
- An so kyautata kyakkyawar mu'amala da tawali'u da tausasawa ga ƙananan yara, da gyara zukatan manya ta hanyar girmama ƙananan yaransu da kuma zaunar da su a ƙirji, da makamancin haka.
- Najasar fitsarin yaro ko da bai fara cin abinci daomin sha'awa ba.
- Aikin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ana kiransa yayyafi, kuma ya keɓanci ƙaramin yaro ne wanda bai fara cin abinci ba, amma mace to babu makawa sai an wanke fitsarinta koda ta kasance ƙarama ce.
- Bahayar yaro wanda yake cin abinci ta hanyar tsotson nonon mahaifiyarsa to babu makawa a cikin hakan sai an wanke kamar sauran najasa.
- Babu makawa a wankewar daga wani al'amari na ƙari akan sanya ruwan.
- Abin da ya fi yin gaggawa da tsaftace bigiren najasar; dan gaggawa a tsarkaka daga kabasin, kuma dan kada a manta.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 54) (223).
صحيح مسلم (1/ 238) (287).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 42).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص55).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 68).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: بال أعرابي في المسجد، فقام الناس إليه لِيَقَعُوا فيه، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «دعوه وأريقوا على بوله سَجْلاً من ماء، أو ذَنُوبًا من ماء، فإنما بُعِثْتُمْ مُيَسِّرِينَ، ولم تُبْعَثُوا مُعَسِّرِينَ».
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: wani Balaraben Kauye a Masallaci, sai Muatane sukai ca kansa don su taba shi, sai Annabi -Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Ku rabu da shi ku zuba Bokitin Ruwa, ko Gugan Ruwa, Saboda an turo ku ne Masu saukakakawa ba'a turoku masu tsanantawa ba"
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Bukhari neDarajaIngantacce ne
Madogara
الجامع المسند الصحيح (صحيح البخاري), تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري, تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر, دار طوق النجاة ترقيم محمد فؤاد عبدالباقي, ط 1422.
رياض الصالحين-النووي-تعليق وتحقيق: الدكتور ماهر ياسين الفحل الناشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق - بيروت-الطبعة: الأولى، 1428 هـ - 2007 م.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي.
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري, تأليف: أبو العباس أحمد بن محمد القسطلاني, الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية, ط7 عام 1323.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com