Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda matsayin 'yarsa sai na umarci Mikdad Dan Aswad sai ya tambaye shi sai ya ce: "Ya wanke gabansa ya yi alwala

عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ رَجُلًا مَذَّاءً وَكُنْتُ أَسْتَحْيِي أَنْ أَسْأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمَكَانِ ابْنَتِهِ فَأَمَرْتُ الْمِقْدَادَ بْنَ الْأَسْوَدِ فَسَأَلَهُ فَقَالَ: «يَغْسِلُ ذَكَرَهُ وَيَتَوَضَّأُ». وَلِلبُخَاريِّ: فَقَالَ: «تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ».
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda matsayin 'yarsa sai na umarci Mikdad Dan Aswad sai ya tambaye shi sai ya ce: "Ya wanke gabansa ya yi alwala". Ga Bukhari: Sai ya ce: "Ka yi alwala ka wanke gabanka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.

Fa’idoji
  1. Falalar Aliu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, yadda kunya ba ta hana shi barin tambayaba ta hanyar (wani).
  2. Halaccin wakilci a neman fatawa.
  3. Halaccin mutum ya baiwa wani labarin abinda yake jin kunyar shi domin wata maslaha.
  4. Najasar maziyyi, da wajabcin wanke shi daga jiki da tufafi.
  5. Fitar maziyyi yana daga abubuwa masu bata alwala.
  6. Wajabcin wanke gaba da maraina dan zuwansa a wani hadisin daban.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 62) (269). صحيح مسلم (1/ 247) (303). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 39). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص53). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص29).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
GUSAR DA NAJASA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com