Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma

عَنْ أَبِي أَيُّوبَ الأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا أَتَيْتُمُ الغَائِطَ فَلاَ تَسْتَقْبِلُوا القِبْلَةَ، وَلاَ تَسْتَدْبِرُوهَا وَلَكِنْ شَرِّقُوا أَوْ غَرِّبُوا» قَالَ أَبُو أَيُّوبَ: فَقَدِمْنَا الشَّأْمَ فَوَجَدْنَا مَرَاحِيضَ بُنِيَتْ قِبَلَ القِبْلَةِ فَنَنْحَرِفُ، وَنَسْتَغْفِرُ اللَّهَ تَعَالَى.
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi nufin biyan buƙatarsa na fitsarine ko bayan gida ya fuskanci alƙibla wajen Ka'aba, kuma kada ya juya mata baya, ya sanyata a bayansa; kai ya wajaba akansa ne ya juya ɓangaren gabas ko yamma idan alƙiblarsa kamar alƙiblar mutanen Madina ce. Sannan Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su lokacin da suka je Sham sun samu banɗakunan da aka tanada dan biyan buƙata a cikinsu an gina su suna fuskantar Ka'aba, sun kasance suna juyawa alƙibla baya da jikkunasu, tare da hakan suna neman gafarar Allah.

Fa’idoji
  1. Hikima a hakan shi ne girmama Ka'aba maɗaukakiya da ganin alfarmarta.
  2. Neman gafara bayan fitowa daga gurin biyan buƙata.
  3. Kyakkyawan koyarwar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi lokacin da ya ambaci wanda aka hana sai ya shiryar zuwa ga wanda ya halatta.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 88) (394). صحيح مسلم (1/ 224) (264). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص37). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 39).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
GUSAR DA NAJASA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com