Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa

عَن عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: سُئِلَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْمَاءِ وَمَا يَنُوبُهُ مِنَ الدَّوَابِّ وَالسِّبَاعِ، فَقَالَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا كَانَ الْمَاءُ قُلَّتَيْنِ لَمْ يَحْمِلِ الْخَبَثَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tamnayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hukuncin tsarkin ruwa wanda dabbobi da zakokai suke zuwa domin su sha da makancinsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ruwa idan awonsa yakai manyan tulu biyu, su sun yi daidai da: Lita (210) cewa shi ruwa ne mai yawa ba ya najastuwa; sai dai idan ɗayan siffofinsa uku ya canja da najasa (su ne) launinsa ko ɗanɗanonsa ko warinsa.

Fa’idoji
  1. Ruwa yana zama mai najasa idan ɗayan siffofinsa uku ya canza da najasa, launinsa, ko ɗanɗanonsa, ko warinsa, hadisin ya fita mafitar mafi rinjaye, ba wai akan iyakancewa ba.
  2. Malamai sun yi ijma'ai akan cewa ruwa idan najasa ta canja shi to ya zama mai najasa kai tsaye, daidai ne ya kasance kaɗan ne ko mai yawa.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 46) (63). سنن الترمذي (1/ 109) (67). سنن النسائي (1/ 46) (52). سنن ابن ماجه (1/ 324) (517). مسند أحمد (8/ 211) (4605). توضيح الأحكام، للبسام (1/ 121). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 67). منحة العلام، لعبد الله الفوزان (1/ 35).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com