Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Lallai mu muna hawa jiragen ruwa a cikin kogi dan sū ko kasuwanci da abinda ya yi kama da hakan, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan wanda za'a iya sha, idan muka yi anfani da ruwan shan dan yin alwala da wanka zai ƙare, kuma ba zamu samu wanda zamu sha ba, shin ya halatta garemu mu yi alwala da ruwan kogi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce game da ruwan kogi: Ruwansa mai tsarki ne kuma mai tsarkakewa; alwala tana halatta da shi da kuma wanka da shi, kuma halal ne cin abinda yake fita daga cikinsa na kifaye da wasunsu, koda an samu mushe ya fito a bayansa ba tare da an yi sū dinsa ba.
- Mushen dabbar kogi halal ne, abin nufi da mushensa: Abin da ya mutu a cikinsa na dabbobinsa daga abinda ba ya rayuwa sai a cikinsa.
- Amsawa mai tambaya da mafi yawan abinda ya tambaya dan cika fa'ida.
- Abin nufi idan ɗanɗanonsa ko launinsa ko warinsa ya canja da wani abu mai tsarki, to shi wanzajje ne akan tsarkinsa muddin dai ruwa ne wanzajje akan haƙiƙaninsa, ko da tsartsinsa ko zafinsa ko sanyinsa ko waninsa ya tsananta.
- Ruwan kogi yana ɗauke babban kari da karami, kuma yana gusar da najasa wacce da ta afkawa abu mai tsarki, daga jiki, ko tufa, ko wanin hakan.
سنن أبي داود (1/ 62) (83). سنن الترمذي (1/ 111) (69). سنن النسائي (1/ 50) (59). سنن ابن ماجه (1/ 250) (386). مسند أحمد (12/ 171) (7233). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (1/ 28). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 59). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 116).