Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN RUWA

Hadisai 5

Kada dayanku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi.

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: "لا يَبُولَنَّ أحَدُكم في الماء الدَّائِم الذي لا يجْرِي، ثمَّ يَغتَسِل مِنه". وفي رواية: "لا يغتسل أحدكُم في الماء الدَّائم وهو جُنُب".
An karbo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - an daga shi zuwa g Annabi: 'kar waninku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi" A wata ruwayar: 'kar waninku ya yi wanka da ruwan da ba ya gudan alhali yana da janaba"
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi mai tsira d a aminci ya yi hani ga yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, saboda hakan ka iya janyo cakuduwarsa da najasa da cututtukan da fitsarin ke dauke da su, wanda sa iya cutar da wanda ya yi amfani da su, ta iya yiwuwa mai yin fitsarinma da kanshi zai iya yin wanka da shi. to ta yaya zai yi fitsari cikin abin da zai iya zama abin tsarkinsa. Hakanan kuma ya yi hani ga yin wankan janaba a cikin ruwan da ba ya gudana; saboda yin hakan zai iya bata ruwan da datti da kazantar janaba.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne

عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلَ رَجُلٌ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّا نَرْكَبُ البَحْرَ، وَنَحْمِلُ مَعَنَا القَلِيلَ مِنَ الْمَاءِ، فَإِنْ تَوَضَّأْنَا بِهِ عَطِشْنَا، أَفَنَتَوَضَّأُ مِنَ الْبَحْرِ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «هُوَ الطَّهُورُ مَاؤُهُ، الحِلُّ مَيْتَتُهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, mu muna tafiya a teku, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan tare da mu, idan muka yi alwala da shi zamu ji ƙishirwa, shin zamu yi alwala daga ruwan kogi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Lallai mu muna hawa jiragen ruwa a cikin kogi dan sū ko kasuwanci da abinda ya yi kama da hakan, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan wanda za'a iya sha, idan muka yi anfani da ruwan shan dan yin alwala da wanka zai ƙare, kuma ba zamu samu wanda zamu sha ba, shin ya halatta garemu mu yi alwala da ruwan kogi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce game da ruwan kogi: Ruwansa mai tsarki ne kuma mai tsarkakewa; alwala tana halatta da shi da kuma wanka da shi, kuma halal ne cin abinda yake fita daga cikinsa na kifaye da wasunsu, koda an samu mushe ya fito a bayansa ba tare da an yi sū dinsa ba.

Fa’idoji
  1. Mushen dabbar kogi halal ne, abin nufi da mushensa: Abin da ya mutu a cikinsa na dabbobinsa daga abinda ba ya rayuwa sai a cikinsa.
  2. Amsawa mai tambaya da mafi yawan abinda ya tambaya dan cika fa'ida.
  3. Abin nufi idan ɗanɗanonsa ko launinsa ko warinsa ya canja da wani abu mai tsarki, to shi wanzajje ne akan tsarkinsa muddin dai ruwa ne wanzajje akan haƙiƙaninsa, ko da tsartsinsa ko zafinsa ko sanyinsa ko waninsa ya tsananta.
  4. Ruwan kogi yana ɗauke babban kari da karami, kuma yana gusar da najasa wacce da ta afkawa abu mai tsarki, daga jiki, ko tufa, ko wanin hakan.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 62) (83). سنن الترمذي (1/ 111) (69). سنن النسائي (1/ 50) (59). سنن ابن ماجه (1/ 250) (386). مسند أحمد (12/ 171) (7233). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (1/ 28). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 59). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 116).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa

عَن عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: سُئِلَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْمَاءِ وَمَا يَنُوبُهُ مِنَ الدَّوَابِّ وَالسِّبَاعِ، فَقَالَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا كَانَ الْمَاءُ قُلَّتَيْنِ لَمْ يَحْمِلِ الْخَبَثَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tamnayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hukuncin tsarkin ruwa wanda dabbobi da zakokai suke zuwa domin su sha da makancinsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ruwa idan awonsa yakai manyan tulu biyu, su sun yi daidai da: Lita (210) cewa shi ruwa ne mai yawa ba ya najastuwa; sai dai idan ɗayan siffofinsa uku ya canja da najasa (su ne) launinsa ko ɗanɗanonsa ko warinsa.

Fa’idoji
  1. Ruwa yana zama mai najasa idan ɗayan siffofinsa uku ya canza da najasa, launinsa, ko ɗanɗanonsa, ko warinsa, hadisin ya fita mafitar mafi rinjaye, ba wai akan iyakancewa ba.
  2. Malamai sun yi ijma'ai akan cewa ruwa idan najasa ta canja shi to ya zama mai najasa kai tsaye, daidai ne ya kasance kaɗan ne ko mai yawa.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 46) (63). سنن الترمذي (1/ 109) (67). سنن النسائي (1/ 46) (52). سنن ابن ماجه (1/ 324) (517). مسند أحمد (8/ 211) (4605). توضيح الأحكام، للبسام (1/ 121). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 67). منحة العلام، لعبد الله الفوزان (1/ 35).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Annabi SAW ya kasance yana wanka da ragowar ruwan Maimuna -Allah ya yarda da ita

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم كان يغتسل بفضل ميمونة رضي الله عنها .
Daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- Cewa Annabi SAW ya kasance yana wanka da ragowar ruwan Maimuna -Allah ya yarda da ita
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah SAW ya Kasance yana wanka da ragowar ruwan Wankan Matarsa Maimuna -Allah ya yarda da ita.

Madogara

- منحة العلام في شرح بلوغ المرام: تأليف عبد الله الفوزان - طبعة دار ابن الجوزي - الطبعة الأولى 1428. - تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام: تأليف الشيخ صالح الفوزان- مؤسسة الرسالة. - توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام: تأليف عبد الله البسام - مكتبة الأسدي – مكة المكرمة – الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ruwa baya yin Najasa

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: اغتسل بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم في جَفْنَةٍ، فجاء النبي صلى الله عليه وسلم ليتوضأ منها أو يغتسل، فقالت: له يا رسول الله، إني كنت جُنُبًا؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إن الماء لا يَجْنُبُ».
An karvo daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: wasu daga cikin Matan Annabi SAW sunyi Wanka a cikin Daro, sai Manzon Allah ya zo zai yi Al-wala daga ciki ko zai yi wanka, sai ta ce da shi: Ya manzon Allah nifa na kasance ina da janaba? sai Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai ruwa baya yin Najasa"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Xaya daga cikin Matan Manzon Allah SAW tayi Wankan Janaba, sai Manzon Allah SAW yazo zaiyi Al-wala ko wanka; sai yaso yayi amfani da ruwan da ya ragu na ruwan Wankan Matarsa -Allah ya yarda da ita- sai ta gaya masa cewa ita ta kasance tana da Janaba, sai ya nusar da ita cewa hakan ba zaiyi tasiri a ruwan ba, kasancewar sa mai tsarki kuma abun tsarkakewa

Madogara

توضيح الأحكام للشيخ البسام، ط5، مكتبة الأسدي، مكة المكرمة، 1423ه. سُبل السلام، للصنعاني، دار الحديث. تسهيل الإلمام للشيخ صالح الفوزان، بعناية: عبدالسلام السليمان، ط1، 1427ه. شرح الشيخ ابن عثيمين، تحقيق صبحي رمضان وآخر، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه. منحة العلَّام للشيخ عبد الله بن صالح الفوزان، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1427ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com