Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ƘISSOSHI DA YANAYI NA AL'UMATAI DA SUKA GABATA

Hadisai 5

Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi

عَنْ صُهَيْبٍ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "كَانَ مَلِكٌ فِيمَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ، وَكَانَ لَهُ سَاحِرٌ، فَلَمَّا كَبِرَ، قَالَ لِلْمَلِكِ: إِنِّي قَدْ كَبِرْتُ، فَابْعَثْ إِلَيَّ غُلَامًا أُعَلِّمْهُ السِّحْرَ، فَبَعَثَ إِلَيْهِ غُلَامًا يُعَلِّمُهُ، فَكَانَ فِي طَرِيقِهِ إِذَا سَلَكَ رَاهِبٌ فَقَعَدَ إِلَيْهِ وَسَمِعَ كَلَامَهُ، فَأَعْجَبَهُ، فَكَانَ إِذَا أَتَى السَّاحِرَ مَرَّ بِالرَّاهِبِ وَقَعَدَ إِلَيْهِ، فَإِذَا أَتَى السَّاحِرَ ضَرَبَهُ، فَشَكَا ذَلِكَ إِلَى الرَّاهِبِ، فَقَالَ: إِذَا خَشِيتَ السَّاحِرَ، فَقُلْ: حَبَسَنِي أَهْلِي، وَإِذَا خَشِيتَ أَهْلَكَ فَقُلْ: حَبَسَنِي السَّاحِرُ، فَبَيْنَمَا هُوَ كَذَلِكَ إِذْ أَتَى عَلَى دَابَّةٍ عَظِيمَةٍ قَدْ حَبَسَتِ النَّاسَ، فَقَالَ: الْيَوْمَ أَعْلَمُ آلسَّاحِرُ أَفْضَلُ أَمِ الرَّاهِبُ أَفْضَلُ؟ فَأَخَذَ حَجَرًا، فَقَالَ: اللهُمَّ إِنْ كَانَ أَمْرُ الرَّاهِبِ أَحَبَّ إِلَيْكَ مِنْ أَمْرِ السَّاحِرِ فَاقْتُلْ هَذِهِ الدَّابَّةَ، حَتَّى يَمْضِيَ النَّاسُ، فَرَمَاهَا فَقَتَلَهَا، وَمَضَى النَّاسُ، فَأَتَى الرَّاهِبَ فَأَخْبَرَهُ، فَقَالَ لَهُ الرَّاهِبُ: أَيْ بُنَيَّ أَنْتَ الْيَوْمَ أَفْضَلُ مِنِّي، قَدْ بَلَغَ مِنْ أَمْرِكَ مَا أَرَى، وَإِنَّكَ سَتُبْتَلَى، فَإِنِ ابْتُلِيتَ فَلَا تَدُلَّ عَلَيَّ، وَكَانَ الْغُلَامُ يُبْرِئُ الْأَكْمَهَ وَالْأَبْرَصَ، وَيُدَاوِي النَّاسَ مِنْ سَائِرِ الْأَدْوَاءِ، فَسَمِعَ جَلِيسٌ لِلْمَلِكِ كَانَ قَدْ عَمِيَ، فَأَتَاهُ بِهَدَايَا كَثِيرَةٍ، فَقَالَ: مَا هَاهُنَا لَكَ أَجْمَعُ، إِنْ أَنْتَ شَفَيْتَنِي، فَقَالَ: إِنِّي لَا أَشْفِي أَحَدًا إِنَّمَا يَشْفِي اللهُ، فَإِنْ أَنْتَ آمَنْتَ بِاللهِ دَعَوْتُ اللهَ فَشَفَاكَ، فَآمَنَ بِاللهِ فَشَفَاهُ اللهُ، فَأَتَى الْمَلِكَ فَجَلَسَ إِلَيْهِ كَمَا كَانَ يَجْلِسُ، فَقَالَ لَهُ الْمَلِكُ: مَنْ رَدَّ عَلَيْكَ بَصَرَكَ؟ قَالَ: رَبِّي، قَالَ: وَلَكَ رَبٌّ غَيْرِي؟ قَالَ: رَبِّي وَرَبُّكَ اللهُ، فَأَخَذَهُ فَلَمْ يَزَلْ يُعَذِّبُهُ حَتَّى دَلَّ عَلَى الْغُلَامِ، فَجِيءَ بِالْغُلَامِ، فَقَالَ لَهُ الْمَلِكُ: أَيْ بُنَيَّ قَدْ بَلَغَ مِنْ سِحْرِكَ مَا تُبْرِئُ الْأَكْمَهَ وَالْأَبْرَصَ، وَتَفْعَلُ وَتَفْعَلُ، فَقَالَ: إِنِّي لَا أَشْفِي أَحَدًا، إِنَّمَا يَشْفِي اللهُ، فَأَخَذَهُ فَلَمْ يَزَلْ يُعَذِّبُهُ حَتَّى دَلَّ عَلَى الرَّاهِبِ، فَجِيءَ بِالرَّاهِبِ، فَقِيلَ لَهُ: ارْجِعْ عَنْ دِينِكَ، فَأَبَى، فَدَعَا بِالْمِئْشَارِ، فَوَضَعَ الْمِئْشَارَ فِي مَفْرِقِ رَأْسِهِ، فَشَقَّهُ حَتَّى وَقَعَ شِقَّاهُ، ثُمَّ جِيءَ بِجَلِيسِ الْمَلِكِ فَقِيلَ لَهُ: ارْجِعْ عَنْ دِينِكَ، فَأَبَى فَوَضَعَ الْمِئْشَارَ فِي مَفْرِقِ رَأْسِهِ، فَشَقَّهُ بِهِ حَتَّى وَقَعَ شِقَّاهُ، ثُمَّ جِيءَ بِالْغُلَامِ فَقِيلَ لَهُ ارْجِعْ عَنْ دِينِكَ، فَأَبَى فَدَفَعَهُ إِلَى نَفَرٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: اذْهَبُوا بِهِ إِلَى جَبَلِ كَذَا وَكَذَا، فَاصْعَدُوا بِهِ الْجَبَلَ، فَإِذَا بَلَغْتُمْ ذُرْوَتَهُ، فَإِنْ رَجَعَ عَنْ دِينِهِ، وَإِلَّا فَاطْرَحُوهُ، فَذَهَبُوا بِهِ فَصَعِدُوا بِهِ الْجَبَلَ، فَقَالَ: اللهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ، فَرَجَفَ بِهِمِ الْجَبَلُ فَسَقَطُوا، وَجَاءَ يَمْشِي إِلَى الْمَلِكِ، فَقَالَ لَهُ الْمَلِكُ: مَا فَعَلَ أَصْحَابُكَ؟ قَالَ: كَفَانِيهِمُ اللهُ، فَدَفَعَهُ إِلَى نَفَرٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: اذْهَبُوا بِهِ فَاحْمِلُوهُ فِي قُرْقُورٍ، فَتَوَسَّطُوا بِهِ الْبَحْرَ، فَإِنْ رَجَعَ عَنْ دِينِهِ وَإِلَّا فَاقْذِفُوهُ، فَذَهَبُوا بِهِ، فَقَالَ: اللهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ، فَانْكَفَأَتْ بِهِمِ السَّفِينَةُ فَغَرِقُوا، وَجَاءَ يَمْشِي إِلَى الْمَلِكِ، فَقَالَ لَهُ الْمَلِكُ: مَا فَعَلَ أَصْحَابُكَ؟ قَالَ: كَفَانِيهِمُ اللهُ، فَقَالَ لِلْمَلِكِ: إِنَّكَ لَسْتَ بِقَاتِلِي حَتَّى تَفْعَلَ مَا آمُرُكَ بِهِ، قَالَ: وَمَا هُوَ؟ قَالَ: تَجْمَعُ النَّاسَ فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ، وَتَصْلُبُنِي عَلَى جِذْعٍ، ثُمَّ خُذْ سَهْمًا مِنْ كِنَانَتِي، ثُمَّ ضَعِ السَّهْمَ فِي كَبِدِ الْقَوْسِ، ثُمَّ قُلْ: بِاسْمِ اللهِ رَبِّ الْغُلَامِ، ثُمَّ ارْمِنِي، فَإِنَّكَ إِذَا فَعَلْتَ ذَلِكَ قَتَلْتَنِي، فَجَمَعَ النَّاسَ فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ، وَصَلَبَهُ عَلَى جِذْعٍ، ثُمَّ أَخَذَ سَهْمًا مِنْ كِنَانَتِهِ، ثُمَّ وَضَعَ السَّهْمَ فِي كَبْدِ الْقَوْسِ، ثُمَّ قَالَ: بِاسْمِ اللهِ، رَبِّ الْغُلَامِ، ثُمَّ رَمَاهُ فَوَقَعَ السَّهْمُ فِي صُدْغِهِ، فَوَضَعَ يَدَهُ فِي صُدْغِهِ فِي مَوْضِعِ السَّهْمِ فَمَاتَ، فَقَالَ النَّاسُ: آمَنَّا بِرَبِّ الْغُلَامِ، آمَنَّا بِرَبِّ الْغُلَامِ، آمَنَّا بِرَبِّ الْغُلَامِ، فَأُتِيَ الْمَلِكُ فَقِيلَ لَهُ: أَرَأَيْتَ مَا كُنْتَ تَحْذَرُ؟ قَدْ وَاللهِ نَزَلَ بِكَ حَذَرُكَ، قَدْ آمَنَ النَّاسُ، فَأَمَرَ بِالْأُخْدُودِ فِي أَفْوَاهِ السِّكَكِ، فَخُدَّتْ وَأَضْرَمَ النِّيرَانَ، وَقَالَ: مَنْ لَمْ يَرْجِعْ عَنْ دِينِهِ فَأَحْمُوهُ فِيهَا، أَوْ قِيلَ لَهُ: اقْتَحِمْ، فَفَعَلُوا حَتَّى جَاءَتِ امْرَأَةٌ وَمَعَهَا صَبِيٌّ لَهَا فَتَقَاعَسَتْ أَنْ تَقَعَ فِيهَا، فَقَالَ لَهَا الْغُلَامُ: يَا أُمَّهْ اصْبِرِي فَإِنَّكِ عَلَى الْحَقِّ".
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da ya girma, sai ya cewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zai zo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan ya zo wajen matsafin sai ya dake shi, sai ya kai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce : Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce: Matsafi ne ya tsareni. Yana cikin haka sai ga shi ya zo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko mai ibada ne ya fi ? sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shi ne mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance ya ji, sai ya zo masa da kyaututtuka masu yawa, sai ya ce: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka yi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yana zama, sai sarkin ya ce da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? ya ce: Ubangijina kuma Ubangijinka Shi ne Allah, sai ya kama shi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har saida ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka ya kai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai aka zo da mai ibadar sai aka ce masa: Ka bar Addinika, sai ya ƙi, sai ya sa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi har saida ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da ɗan majalisar sarki sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai aka ɗora zarton akan tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da yaron sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai ya miƙa shi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan ya bar Addininsa to (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗauke shi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa to inba haka ba fa to ku jefa shi, sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiye, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya cewa sarkin: Kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, ya ce: Menene shi? ya ce: Ka tara mutane wuri ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, sai ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, sai aka zo wa sarkin sai aka ce da shi: Shin kana ganin abinda tsoro, haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sun yi imani, sai ya yi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko a ce masa: Ka faɗa sai suka aikata, har sai da wata mace ta zo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani sarki cikin waɗanda suka gabacemu daga cikin al’ummu, ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da matsafin ya girma (ya tsufa), sai ya cewa sarkin: Lallai ni na girma, to ka aiko wani saurayi zuwa wurina in koya masa tsafi. Sai sarkin ya aika masa da wani saurayin da zai koya masa, a kan hanyar saurayin idan zai tafi gurin matsafin akwai wani mai ibada, sai ya zauna a wurinsa sau ɗaya ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi. Ya kasance idan ya zo wurin matsafin sai ya wuce wurin mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan kuma ya je wurin matsafin sai ya dake shi, saboda jinkirin da ya yi, sai ya kai ƙarar hakan wurin mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce: Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce : Matsafi ne ya tsareni. Sun kasance a haka lokacin da ya zo wa wata babbar dabba ta hana mutane wucewa, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko kuma mai ibada ne yafi? Sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin wannan mai ibadar ne mafi soyuwa gareKa daga al'amarin matsafin nan to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su wuce, sai ya jefeta sai ya kasheta, kuma mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana ! Kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda kake gani, kuma lallai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, yana bawa mutane maganin sauran cututtuka da izinin Allah, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya rasa idonsa ya ji, sai ya zo masa da kyautuka masu yawa, sai ya cewa yaron: Dukkan abinda ke nan na kyautuka naka ne idan ka warkar da ni. Sai ya ce: Lallai ni bana warkar da wani kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka ni imani da Allah zan roƙi Allah Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yake zama, sai sarkin ya ce masa: Waye ya mayar maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? Ya ce: Ubangijina da Ubangijinka shi ne Allah. Sai ya kama shi bai gushe ba yana azabtar da shi har sai da ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Ya kai ɗana ! haƙiƙa tsafinka yakai har kana warkar da makaho da kuturu, kana aikata kaza da kaza. Sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gushe ba yana azabtar da shi har saida ya nuna mai ibadar. Sai aka zo da mai ibadar, sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai yaƙi, sai ya ce akawo masa zarto, sai ya ɗora shi akan tsakiyar kansa, sai ya raba shi gida biyu. Sannan aka zo da ɗan majalisar sarkin sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi sai ya sanya zarto akan tsakiyar kansa, sai ya raba shi gida biyu. Sannan aka zo da yaron sai aka ce masa ka bar Addinika, sai ya ƙi sai ya miƙashi wurin wasu mazaje daga mutanensa tsakanin uku da goma. Sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa, idan ya bar Addininsa to, inba haka bafa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi sai suka hau dutsen da shi. Sai yaron ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su ya yi motsi motsi mai tsanani sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin. Sai sarkin ya ce masa: Me mutanenka suka yi? Ya ce: Allah Ya isar mini su. Sai ya miƙashi zuwa wasu mutane daga cikin mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗaukeshi a cikin ƙaramin jirgin ruwa, sai ku tafi tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jefa shi a cikin kogin. Sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah Ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiya, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin. Sai sarkin ya ce masa: Me mutanenka suka yi? Sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai yaron ya cewa sarkin: Lallai cewa kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi. Ya ce: Menene shi? Ya ce: Ka tara mutane a babban fili, ka tsireni akan kututturen bishiya, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai cewa kai idan ka aikata haka to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa, sannan ya sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan ya ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai mashin ya faɗa a kayakayinsa tsakanin idanuwansa da kunnansa, sai ya ɗora hannunsa a kayakayinsa a wurin da mashin (ya faɗa) sai ya mutu. Sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, mun yi imani da Ubangijin yaro, Mun yi imani da Ubangijin yaro. Sai aka zo wa sarkin aka ce masa: Shin kaga abinda ka kasance kana jin tsoro? Haƙiƙa wallahi abinda ka ji tsoro ya kasance, shi ne mutane suna bin yaron da yin imani da Ubangijin yaron bakiɗayansu, sai ya yi umarni a tsaga ƙasa a yi manyan ramuka masu tsawo a ƙofofin hanyoyi, aka kunna wuta a cikinsu, kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku jefa shi a cikinta, sai suka aikata abinda sarkin ya umarcesu da shi, har wata mace ta zo atare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya ta lazimci inda take, taƙi shiga cikin wutar, sai ɗanta ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri, lallai ke akan gaskiya kike.

Fa’idoji
  1. Tabbatar da karamomin waliyyai, daga cikin hakan akwai kashe babbar dabba ta hanyar jifan yaron, da kuma amsa addu'ar yaron sau biyu, da kuma maganar ƙaramin yaron da ake shayar da shi.
  2. Taimakon wanda ya dogara ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
  3. Bayanin matsayin haƙuri da kuma tabbata akan Addini.
  4. Hikima a cikin neman ilimi a farkon rayuwa; domin cewa saurayi a galibi ya fi saurin hadda akan babba.
  5. Ƙarfin imanin wannan yaron, kuma cewa bai yi nisa da imaninsa ba bai kuma juya baya ba.
  6. Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana amsa kiran wanda ke cikin tsananin buƙata idan ya kiraShi.
  7. Mutum yana halatta ya ruɗar da kansa a cikin maslahar dukkanin musulmai, domin wannan yaron ya nunawa sarki abinda zai kashe shi da shi ya kuma halakar da kansa da shi, shi ne ya ɗauki mashi daga cikin kibiyoyinsa ya sanya shi a tsakiyar kwari sai ya ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro.
  8. Halaccin yin ƙarya a cikin yaƙi da makamancinsa, da kuma tsamo rai daga halaka.
  9. Mumini ana jarrabarsa a cikin gaskiyar imaninsa da kuma tabbata akan faɗin gaskiya, ko da al'amarin zai kaishi ga rasa ransa.
  10. Bada rai ta hanyar kira zuwa ga Allah da kuma bayyanar da gaskiya.
  11. Zukatan bayi suna hannun Allah Yana shiryar da wanda Yake so kuma Yana ɓatar da wanda Ya ga dama, haƙiƙa yaron ya shiriya alhali shi yana karkashin renon matsafi da kuma kulawar sarki mai laifi.
  12. Halaccin roƙon Allah - Maɗaukakin sarki - Ya nunawa bawa alamar da zai san daidai, da ita kuma yaƙini ya tabbata gare shi .
  13. Masu imani suna bada dukkan abinda Allah Ya basu kuma Ya yi musu falala da shi dan yi wa Addininsa hidima da kuma kira zuwa ga tarkinSa.
  14. Sabubban halaka suna hannun Allah, idan Ya so sai Ya zartar da su idan kuma ya so sai ya yanke su.
  15. Kafirai hujjoji da dalilai basa tauyesu dan yin imani, kawai sababin kafircinsu shi ne shisshigi da kuma girman kai.
  16. Ɗagutai da azzalumai akwai suna da tanadi dan kashe mutane bakiɗaya dan su wanzu akan abinda suke a cikinsa na ni'imar duniya.
  17. Allah Yana yi wa azzalumai uƙuba ta inda basa zato, haƙiƙa mutane sun yi imani da Ubangijin yaro lokacin da suka ga tabbatarsa da gaskiyar da'awarsa da kuma rashin tsoronsa ga zargin mai zargi saboda Allah.
  18. Akwai waɗanda suka yi magana suna tsumman goyo banda (Annabi) Isa - aminci ya tabbata agare shi -, wannan hadisin yana bayanin faɗin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Babu waɗanda suka yi magana a cikin shinfiɗar goyo sai mutum uku...", sai ya ambacesu, ya kuma taƙaitasu a cikin Banu Isra'il banda wasunsu.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2299) (3005). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 86). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص39). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 412). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 210). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 62).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu.

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «ما نهيتكم عنه فاجتنبوه، وما أمرتكم به فأْتُوا منه ما استطعتم، فإنما أَهلَكَ الذين من قبلكم كثرةُ مسائلهم واختلافهم على أنبيائهم».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana nuna mana cewa shi idan ya hanamu wani abu ya wajaba akanmu mu nisance shi ba tare da wata togaciya ba, kuma idan ya Umarcemu da wani abu kan mu yi shi to muyi gwargwadon iko sannan ya tsawatar mana don kada mu zamanto irin wasu Al'ummai da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawansu kuma suka saba musu sai Allah yayi musu Ukuba da Nau'o'in Hallaka da rusawa to ya dace kada mu kasance irin su don kada mu hallaka kamar yada suka hallaka.

Madogara

-التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، مطبعة دار نشر الثقافة، الإسكندرية، الطبعة: الأولى، 1380 هـ. -شرح الأربعين النووية، للشيخ ابن عثيمين، دار الثريا للنشر. -فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، دار ابن القيم، الدمام المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1424هـ/2003م. -الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك، دار التوحيد للنشر، الرياض. -شرح الأربعين النووية، للشيخ صالح آل الشيخ، دار الحجاز، الطبعة: الثانية، 1433هـ. -الأربعون النووية وتتمتها رواية ودراية، للشيخ خالد الدبيخي، ط. مدار الوطن. -الجامع في شروح الأربعين النووية، للشيخ محمد يسري، ط. دار اليسر. -صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita

عَنْ أَبِي حَازِمٍ قَالَ: قَاعَدْتُ أَبَا هُرَيْرَةَ رضي الله عنه خَمْسَ سِنِينَ، فَسَمِعْتُهُ يُحَدِّثُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «كَانَتْ بَنُو إِسْرَائِيلَ تَسُوسُهُمُ الأَنْبِيَاءُ، كُلَّمَا هَلَكَ نَبِيٌّ خَلَفَهُ نَبِيٌّ، وَإِنَّهُ لاَ نَبِيَّ بَعْدِي، وَسَيَكُونُ خُلَفَاءُ فَيَكْثُرُونَ» قَالُوا: فَمَا تَأْمُرُنَا؟ قَالَ: «فُوا بِبَيْعَةِ الأَوَّلِ فَالأَوَّلِ، أَعْطُوهُمْ حَقَّهُمْ، فَإِنَّ اللَّهَ سَائِلُهُمْ عَمَّا اسْتَرْعَاهُمْ».
Daga Abu Hazim ya ce: Na zauna da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - shekara biyar, sai na ji shi yana zantarwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce; "Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita" Suka ce: Da me zaka umarce mu? ya ce: "Ku cika caffar na farko sai na farko, ku basu haƙƙinsu, domin cewa Allah Mai tambayarsu ne daga abinda Ya basu kiwo".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.

Fa’idoji
  1. Babu makawa ga talakawa daga wani Annabi ko halifa da zai tsayu da al'amarinsu, kuma zai ɗorasu akan hanya madaidaiciya.
  2. Cewa babu wani Annabi bayan Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Gargaɗarwa daga fito na fito akan wanda shugabancinsa ya tabbata ta hanya ta shari'a.
  4. Ba ya halatta a yi caffa ga halifofi biyu a lokaci ɗaya.
  5. Girman nauyin shugaba, domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa hisabi game da talakawansa.
  6. Ibnu Hajar ya ce: Gabatar da al'amarin Addini akan al'amarin duniya; domin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da cika haƙƙin shugaba dan abinda ke cikinsa na ɗaukaka kalmar Addini da kame fitina da sharri; da jinkirta al'amarin nema da haƙƙinsa ba zai sarayar da shi ba, haƙiƙa Allah Ya yi masa alƙawari cewa Shi Zai tseratar da shi kuma zai cika masa koda a gidan lahira ne.
  7. Alama ce daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haƙiƙa halifofi sun yawaita a bayansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma masu gyarawa da masu munanawa sun jerantu ga al'umma.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 169) (3455). صحيح مسلم (3/ 1471) (1842). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 707). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 544).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ba'a tava samun wanda yayi magana ba yana zanin goyo sai Mutane Uku

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لم يتكلَّم في المهد إلا ثلاثة: عيسى ابن مريم، وصاحب جرَيج، وكان جُريج رجلًا عابِدا، فاتخذ صَوْمَعَة فكان فيها، فأتته أمه وهو يصلي، فقالت: يا جريج، فقال: يا رَبِّ أُمِّي وصلاتي فأقبل على صلاته فانْصَرفت. فلمَّا كان من الغَدِ أتَتْهُ وهو يصلي، فقالت: يا جُريج، فقال: أي رَبِّ أمِّي وصلاتي، فأقبل على صلاته، فلمَّا كان من الغَدِ أتَتْهُ وهو يصلي، فقالت: يا جُريج، فقال: أي رَبِّ أمِّي وصلاتي، فأقبل على صلاته، فقالت: اللَّهُمَّ لاَ تُمِتْهُ حتى يَنظر إلى وجوه المُومِسَاتِ. فتذاكر بَنُو إسرائيل جُريجا وعبادته، وكانت امرأة بَغِيٌّ يُتَمَثَّلُ بحُسنها، فقالت: إن شِئتم لأَفْتِنَنَّهُ، فتَعرَّضت له، فلم يَلتَفت إليها، فأتت راعِيا كان يَأوِي إلى صَوْمَعَتِهِ، فَأَمْكَنَتْه من نَفسِها فوقع عليها، فحملت، فلمَّا ولدت، قالت: هو من جُريج، فَأتَوْهُ فَاسْتَنْزَلُوهُ وهدَمُوا صَومَعتَه، وجَعَلوا يَضربونه، فقال: ما شَأنُكم؟ قالوا: زَنَيْتَ بهذه البَغِيِّ فولَدَت منك. قال: أين الصَّبي؟ فجاؤَوا به فقال: دَعوني حتى أُصلَّي، فصلَّى فلمَّا انْصرف أتى الصَّبي فَطَعن في بَطنه، وقال: يا غُلام مَنْ أبوك؟ قال: فلانٌ الراعي، فأقبلوا على جُريج يقبلونه ويَتمسَّحون به، وقالوا: نَبْنِي لك صَوْمَعَتَكَ من ذهب. قال: لا، أعِيدُوها من طين كما كانت، ففعلوا. وبينا صبي يَرضع من أُمِّهِ فمرَّ رجل راكب على دابة فَارِهة وَشَارَةٍ حسَنَة، فقالت أمه: اللهم اجعل ابْني مثل هذا، فَترك الثَّدْي وأقْبَلَ إليه فنَظَر إليه، فقال: اللَّهم لا تجعلني مثْلَه، ثم أقْبَلَ على ثَدْيه فجعل يَرتضع»، فكأني أنظر إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم وهو يَحكي ارتْضَاعه بِأصْبَعِهِ السَّبَّابَة في فِيه، فجعل يَمُصُّهَا، قال: «ومَرُّوا بجارية وهم يَضْرِبُونها، ويقولون: زَنَيْتِ سَرقت، وهي تقول: حَسبي الله ونعم الوكيل. فقالت أمه: اللَّهم لا تجعل ابني مِثلها، فترك الرَّضاع ونظر إليها، فقال: اللَّهم اجعلني مِثْلَها، فَهُنَالك تَرَاجَعَا الحديث، فقالت: مرَّ رجلٌ حَسَنُ الهَيْئَةِ ، فقلت: اللَّهم اجعل ابْنِي مِثْلَه، فقلت: اللَّهم لا تَجْعَلْنِي مِثْله، ومَرُّوا بهذه الأَمَة وهم يَضربونها ويقولون: زَنَيْتِ سَرقت، فقلت: اللَّهم لا تجعل ابني مِثلها، فقلت: اللَّهم اجعلني مِثلها؟! قال: إن ذلك الرَّجُل كان جبَّارا، فقلت: اللَّهم لا تجعلني مِثْله، وإن هذه يقولون: زَنَيْتِ، ولم تَزْنِ وسَرقْتِ، ولم تَسْرِقْ، فقلت: اللَّهم اجْعَلْنِي مِثْلَهَا».
A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: “Uku ne kawai suka yi magana a cikin shimfiɗar jariri: Yesu, ɗan Maryama, da mamallakin Jarij, kuma Greg ya kasance mutum ne mai yawan ibada, ya Haga Greg, sannan ya ce: Ya Ubangiji, mahaifiyata da addu'ata, don haka na karvi addu'arsa, sai ta tafi. Kuma a lokacin da ya kasance gobe, sai ta je masa yayin da yake salla, sai ta ce: Ya Greg, sai ya ce: Wanne ne Ubangijin mahaifiyata da addu'ata, don haka ya karvi sallarsa, kuma idan ta kasance gobe ta zo gare shi yayin da yake sallah, sai ta ce: Ya Greg, sai ya ce: Mene ne Ubangijin mahaifiyata da addu'ata, sai ta ce: Ya Allah, kada ka mutu har sai ya kalli fuskokin karuwai. Don haka ya tuna da Bani Isra’ila Grija da bautarsa, kuma wata karuwa tana kwaikwayon kyawunta, sai ta ce: Idan kuna so, da ni za a jarabce ni da shi, sai ta bayyana gare shi, kuma bai kula ba. zuwa gare ta.Saboda haka suka sauko da shi suka lalata dakin da yake ciki, suka sanya shi suka doke shi, don haka ya ce: Mece ce sana'ar ku? Sai suka ce: Ka yi zina da wannan karuwa, kuma ita ce ta haife ka. Ya ce: Ina yaron yake? Sannan suka kawo shi suka ce: Bari in yi Sallah har sai na yi Sallah.Ya yi Sallah.Lokacin da ya tafi, sai yaron ya zo ya daba masa wuka a ciki, ya ce: Haba yaro, wane ne babanka? Ya ce: Haka-da-haka Makiyayin, don haka suka zo wurin Greg, suka sumbace shi kuma suka shafe shi, suka ce: Mun gina maka sila ta zinariya. Ya ce: A'a, dauke shi daga laka yadda yake, haka kuwa suka yi. A cikinmu akwai wani yaro mai shayarwa daga mahaifiyarsa, sai wani mutum da yake hawa kan wata dabba mai ni'ima da wata alama mai kyau ya wuce, sai mahaifiyarsa ta ce: Ya Allah ka sanya dana kamar haka, sai ya bar nono ya zo gare shi, don haka sai ya dube shi, ya ce: Ya Allah, kada ka sanya ni kamar shi, sai ya sumbace ni, sai ya sumbace ni - - Allah Ya yi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake ba da labarin shayarwarsa da yatsa a ciki, sai ya fara tsotsa. Ya ce: “Sun wuce kusa da wata baiwa yayin da suke mata duka, sai suka ce: Na sata, sai ta ce: Allah Mai rahama ne, kuma Ee, wakilin. Mahaifiyarsa ta ce: Ya Allah, kada ka sanya dana ya zama kamar ta, sai ya bar nono ya dube ta, sai ya ce: Ya Allah, ka sanya ni kamar ta, don a can ne muka sake yin hadisin. Kuma suka ce: Ni sace sace na, sai na ce: Ya Allah, kada ka sanya dana kamar ta, sai na ce: Ya Allah, ka sanya ni kamar ta?! Ya ce: Wannan mutumin babban mutum ne, sai na ce: Ya Allah, kada ka sanya ni kamar shi, kuma wadannan suna cewa: Na yi zina, kuma ban yi zina ba, kuma na yi sata, kuma ban yi sata ba, sai na ce: Ya Allah , sanya ni kamar ta.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ. بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م. نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ، الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ. شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ. رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ. دليل الفالحين، تأليف: محمد بن علان، الناشر: دار الكتاب العربي، نسخة الإلكترونية ، لا يوجد بها بيانات نشر. صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. دروس وعبر من صحيح القصص النبوي، تأليف: شحاتة محمد صقر، الناشر: مكتبة دار العلوم، البحيرة، مصر.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wasu Mutane Uku sun futo suna tafiya sai Ruwan sama ya sauko, sai suka shiga cikin Kogo. sai Dutse ya rufe su

عن ابن عمر رضي الله عنهما ، عن النبي صلى الله عليه وسلم ، قال: «خرج ثلاثةُ نَفَرٍ يمشون فأصابهم المَطَر، فدَخَلوا في غارٍ في جبَل، فانْحَطَّت عليهم صَخْرةٌ، قال: فقال بعضُهم لبعض: ادعوا اللهَ بأفضلِ عَمَلٍ عَمِلتموه، فقال أحدُهم: اللهمَّ إني كان لي أبَوَانِ شَيْخانِ كبيران، فكنتُ أخرج فَأَرْعى، ثم أَجيء فأحْلِب فأجيء بالحِلاب، فآتي به أبويَّ فيَشْربان، ثم أسِقِيَ الصِّبْيَة وأهلي وامرأتي، فاحتَبَستُ ليلة، فجئتُ فإذا هما نائمان، قال: فكرهتُ أن أُوقِظَهما، والصِّبية يَتَضَاغَوْن عند رِجْلي، فلم يزل ذلك دَأْبي ودَأْبَهما، حتى طلَع الفجر، اللهم إن كنتَ تَعْلَمُ أنِّي فعلتُ ذلك ابْتغاء وجهِك، فافرُجْ عنا فُرْجة نرى منها السماء، قال: فَفُرِج عنهم، وقال الآخر: اللهم إن كنتَ تعلم أني كنتُ أُحبُّ امرأةً مِن بنات عمي كأشَدِّ ما يُحبُّ الرجلُ النساء، فقالت: لا تَنال ذلك منها حتى تعطيها مائة دينار، فسَعيْتُ فيها حتى جَمَعتُها، فلما قَعَدتُ بيْن رِجليْها قالت: اتقِ الله ولا تَفُضَّ الخاتَمَ إلا بحقِّه، فقمتُ وتركتُها، فإن كنتَ تعْلَم أنِّي فعلتُ ذلك ابتغاء وجهِك، فافرُجْ عنا فُرْجَة، قال: ففُرِج عنهم الثُّلُثيْنِ، وقال الآخر: اللهم إن كنتَ تعْلَم أني اسْتَأجَرْتُ أجيرًا بفَرَق من ذُرَة فأعْطيتُه، وأَبَى ذاك أنْ يأخُذَ، فعَمَدتُ إلى ذلك الفَرَق فزرعتُه، حتى اشتريتُ منه بقرًا وراعِيها، ثم جاء فقال: يا عبد الله أعْطِني حَقِّي، فقلتُ: انطلقْ إلى تلك البقر وراعِيها فإنها لك، فقال: أتستهْزِئ بي؟ قال: فقلت: ما أستهزئ بك ولكنها لك، اللهم إن كنتَ تعلم أنِّي فعلتُ ذلك ابتغاء وجهك، فافْرُجْ عنا فكُشِف عنهم».
Daga Ibn Umar - Allah ya yarda da shi - a kan annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: “Mutane uku sun fita suna tafiya sai ruwan sama ya same su, sai suka shiga wani kogo a cikin wani dutse, sai dutse ya fado musu. .ayansu ya ce: Ya Allah, Ina da tsofaffi shehunnai biyu. Don haka, wannan har yanzu aikina ne, har zuwa wayewar gari, idan ka san na yi haka da sha'awar fuskarka , to sai ka bude wani rami daga gare mu wanda muke gani daga sama. Namijin, matan, suka ce: Kada ku samo hakan a wurinta har sai kun ba ta dinari dari. Kashi biyu bisa uku a madadinsu, dayan kuma ya ce: Ya Allah, idan ka san cewa na dauki hayar ma’aikaci haya da bambancin masara, to, sai na ba shi, kuma ya ki karba, sai na tafi waccan kungiyar, don haka na dasa shi, har sai da na saye shi daga gare shi, ya bawa, sannan ya zo wurina, sai na sayo mata baiwa, sannan na dasa shi.Siyar da makiyayinta, domin naka ne. Ya ce: Shin ka yi min izgili? Ya ce: Don haka na ce: Ba na izgili da kai, amma naka ne. Ya Allah, idan ka san cewa na yi hakan a fuskarka, to ka bar mu, don haka na bayyana su. ”
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uku daga cikin mutanen sun fita suna tafiya sai aka yi ruwan sama a kansu a sama, don haka suka shiga wani kogo don fakewa da shi daga tsananin ruwan sama, sai wani dutse ya fadi ya rube kofar kogon, sai wasu daga cikinsu suka ce juna: Ku roƙi Allah don mafi kyawun aikin da kuka yi. Wataƙila Allah zai sake ku ya cire wannan dutsen, don haka ɗayan ukun ya ce: Ya Allah, Ina da tsoho uba da mahaifiya, kuma na kasance ina fita zuwa makiyaya ina kiwon raƙumana, sannan na fito daga makiyayar, kuma Ina shayar da rakumi na, don haka zan kawo madara don mahaifina da mahaifiyata su basu kuma su sha, sannan na shayar da littleana childrenana andana children da matata da sauran iyalina daga brotheran uwa da sisterar uwa, don haka wani dare ya makara saboda wani abu da ke damuna, don haka mahaifina da mahaifiyata suna barci, kuma na yi madara kamar yadda nake madara, don haka na tashi a kawunansu, na ƙi in tashe su, kuma na ƙi jinin shayar da childrena beforeana da iyalina a da su, da yarana suna ta kuka suna kururuwa saboda yunwa lokacin da Kafa na, kuma hakan ya kasance kasuwancin su har gari ya waye kuma suka farka suka shayar da su sannan suka shayar da yarana, don haka Allah, idan ka san cewa nayi hakan ne don farin cikin ka, to cire dutsen nan daga garemu kadan har sai mun ga sama, sai Allah ya sake su don haka suka ga sama daga gare ta. Na biyun ya ce: Ya Allah, na ƙaunaci mace daga cikin 'ya'yan kawuna mata sosai, don haka sai ta tafi daga kanta, don haka ta ƙi ni sai dai in ba ta dinari ɗari. An cire budurcina ban da na halal, don haka na tashi daga tsakanin ƙafafuwanta kuma na bar ta, kuma ban yi komai da ita ba, don haka Allah, idan ka san cewa na yi hakan don jin daɗinka, to, ka cire mu daga wannan dutsen, sai Allah ya sake su kashi biyu bisa uku na wurin da dutsen yake shine. Na ukun ya ce: Ya Allah, na yi hayar wani ma'aikaci don ya yi min aiki in ba shi masara fam goma sha shida.Lokacin da ya gama aikinsa, sai na ba shi ladansa ya ƙi karɓa. Ya Abdullah, ka ba ni damana Don haka na ce: Je zuwa ga shanun nan ka yi kiwon su, domin naku ne, don haka ku dauke su duka. Sai ma'aikacin ya ce: Shin kuna izgili da ni? Na ce: Ba na muku izgili, amma naku ne, don haka Allah, idan da kun san cewa na yi hakan ne don farin cikin ku, to sai ku sake wannan dutsen daga gare mu, sai Allah ya sake su daga abin da ya rage daga kofar kogon, don haka suka barshi.

Madogara

- صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. - صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. - عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. - النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير، نشر: المكتبة العلمية - بيروت، 1399هـ - 1979م، تحقيق: طاهر أحمد الزاوى - محمود محمد الطناحي. - شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ. - الشرح الممتع على زاد المستقنع, محمد بن صالح بن محمد العثيمين, دار ابن الجوزي, الطبعة: الأولى، 1422 - 1428 هـ. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين, محمد علي بن محمد البكري, اعتنى بها: خليل مأمون شيحا, الناشر: دار المعرفة, بيروت – لبنان, الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com