Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.
- Babu makawa ga talakawa daga wani Annabi ko halifa da zai tsayu da al'amarinsu, kuma zai ɗorasu akan hanya madaidaiciya.
- Cewa babu wani Annabi bayan Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Gargaɗarwa daga fito na fito akan wanda shugabancinsa ya tabbata ta hanya ta shari'a.
- Ba ya halatta a yi caffa ga halifofi biyu a lokaci ɗaya.
- Girman nauyin shugaba, domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa hisabi game da talakawansa.
- Ibnu Hajar ya ce: Gabatar da al'amarin Addini akan al'amarin duniya; domin cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da cika haƙƙin shugaba dan abinda ke cikinsa na ɗaukaka kalmar Addini da kame fitina da sharri; da jinkirta al'amarin nema da haƙƙinsa ba zai sarayar da shi ba, haƙiƙa Allah Ya yi masa alƙawari cewa Shi Zai tseratar da shi kuma zai cika masa koda a gidan lahira ne.
- Alama ce daga alamomin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haƙiƙa halifofi sun yawaita a bayansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma masu gyarawa da masu munanawa sun jerantu ga al'umma.
صحيح البخاري (4/ 169) (3455). صحيح مسلم (3/ 1471) (1842). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 707). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 544).