Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HIJIRA

Hadisai 3

‌Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu

عَنْ أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: نَظَرْتُ إِلَى أَقْدَامِ الْمُشْرِكِينَ عَلَى رُءُوسِنَا وَنَحْنُ فِي الْغَارِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ لَوْ أَنَّ أَحَدَهُمْ نَظَرَ إِلَى قَدَمَيْهِ أَبْصَرَنَا تَحْتَ قَدَمَيْهِ، فَقَالَ: «يَا أَبَا بَكْرٍ، مَا ظَنُّكَ بِاثْنَيْنِ اللهُ ثَالِثُهُمَا».
Daga Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kalli digadigan mushrikai akan kawunanmu alhali mu muna cikin kogo, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai kalii digadigansa zai ganmu a ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce: «‌Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sarkin muminai Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a lokacin hijira: Na kalli digadigan mushrikai alhali su suna tsaye akan kawunanmu a saman kogon Hira alhali mu muna cikinsa, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai yi duba zuwa ga digadigansa zai ganmu ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce : Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyu Allah ne na ukunsu da nasara da kuma taimako, da kiyayewa da kuma daidaita?!

Fa’idoji
  1. Darajar Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a abokantakarsa da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a hijirarsa da ya yi daga Makkah zuwa Madina, da kuma rabuwa da ya yi da iyalansa da kuma dukiyarsa.
  2. Tausayin Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi -, da kuma fagen soyayyarsa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda ya jiye masa tsoro daga maƙiya.
  3. Wajabcin amincewa Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da nutsuwa ga kiyayewarSa, da kuma kulawarSa bayan yin ƙoƙari a riƙar kiyayewa.
  4. Kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga AnnabawanSa da masoyanSa, da kuma kiyayewarSa garesu da nasara, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: (Lallai ne Mu zamu taimaki Manzanninmu da waɗanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da masu shaida zasu tsaya).
  5. Faɗakarwa akan cewa duk wanda ya dogara ga Allah to Ya isar masa, zai taimake shi, kuma zai kiyaye shi.
  6. Cikar tawakkalin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, kuma cewa shi ne wanda ake dogaro gareShi, kuma ake fawwala al'amari gareShi.
  7. Gwarzantakar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda yake sa zukata da rayuka nutsuwa.
  8. Guduwa da Addini dan jin tsoron maƙiyi, da kuma yin riƙo da sabubba.
Madogara

صحيح البخاري (5/ 4) (3653). صحيح مسلم (4/ 1854) (2381). شرح صحيح مسلم (149/15). فتح الباري (11/7). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (276/2) شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (563/1).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yayin da Annabi SAW ya Iso daga Yakin Tabuka Mutane sun tare shi, sai na tare shi ni da Yara a Saniyyatil Wada'a

عن السَّائب بن يزيد رضي الله عنه قال: لما قَدِم النبي صلى الله عليه وسلم من غَزْوة تَبُوك تَلَقَّاهُ الناس، فَتَلَقَّيتُه مع الصِّبْيَان على ثَنيَّةِ الوَدَاع. ورواية البخاري قال: ذَهَبْنا نَتَلَقَّى رسول الله صلى الله عليه وسلم مع الصِّبْيَان إلى ثَنيَّةِ الوَدَاع.
An rawaito daga Al-Sa'ib Bn Yazid -Allah ya yarda da shi- yace: "Yayin da Annabi SAW ya iso Madina- daga yakin Tabuka Mutane sun tare sai na tare shi tare da Yara, kuma a cikin wata Riwayar ya ce:"Mun tafi mu taro Annabi SAW tare da Yara a Thaniyat Al-Wadaa"
Buhari ne ya rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ma'anar hadisin: - Al-Saib bin Yazid - Allah ya yarda da shi - ya ce Annabi - SAW- lokacin da ya zo daga yaqin Tabuka, mutane - waxanda suka bari daga yaqin neman gafara da wasunsu - suka tafi gidan bankwana don karvar sa - tsira da aminci su tabbata a gare shi - lokacin da Dawowarsa. Al-Saib bin Yazid ya fita tare da yaran Madina don ganawa da Annabi - SAW

Madogara

- سنن أبي داود - سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد: المكتبة العصرية. - صحيح البخاري -للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين/تأليف مصطفى سعيد الخن-مصطفى البغا-محي الدين مستو-علي الشربجي-محمد أمين لطفي-مؤسسة الرسالة-بيروت –لبنان-الطبعة الرابعة عشرة. - منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري تأليف- حمزة محمد قاسم مكتبة دار البيان، دمشق - الجمهورية العربية السورية، مكتبة المؤيد، الطائف - المملكة العربية السعودية- 1410 هـ - 1990 م. - إرواء الغليل في تخريج أحاديث منار السبيل/ محمد ناصر الدين الألباني - إشراف: زهير الشاويش-المكتب الإسلامي – بيروت-الطبعة: الثانية 1405 هـ - 1985م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa Manzon Allah SAW ya zauna a Makkah Shekara goma Al-qur'ani ya na Sauka a gare shi, a Madina kuma Shekara goma

عن عائشة وابن عباس رضي الله عنهم : «أنَّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم لَبِثَ بمكَّة عشرَ سِنِين، يَنْزلُ عليه القرآنَ، وبالمدينة عشرًا».
Daga Aisha da Ibn Abbas -Allah ya yarda da su-: "Lallai cewa Manzon Allah SAW ya zauna a Makkah Shekara goma Al-qur'ani ya na Sauka a gare shi, a Madina kuma Shekara goma"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. - كشف المشكل من حديث الصحيحين، لجمال الدين أبي الفرج عبد الرحمن بن علي بن محمد الجوزي، المحقق: علي حسين البواب، الناشر: دار الوطن - الرياض. - لسان العرب, محمد بن مكرم بن على ابن منظور الأنصاري, دار صادر – بيروت, الطبعة: الثالثة - 1414 هـ. - التوضيح لشرح الجامع الصحيح, عمر بن علي بن أحمد ابن الملقن, ت: دار الفلاح للبحث العلمي وتحقيق التراث, دار النوادر، دمشق – سوريا, الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com