An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da shugabannin da suke neman haƙƙinsu daga mutane na ji da biyayya, kuma suna hana haƙƙin da ke kansu; na yin adalci da bada ganima da dawo da abubuwan da aka zalinta da daidaito, to me zaka umarcemu mu aikata tare da su? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kau da kai; kamar ya ƙyamaci waɗannan tambayoyin, sai dai mai tambayar ya sake maimaita masa karo na biyu da na uku, sai al-Ash'as ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya fizgo mai tambayar dan ya sa shi ya yi shiru. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa, ya ce: Ku ji abinda suke faɗa, kuma Ku bi umarninsu; kaɗai abinda aka ɗora musu na adalci da bawa talakawa hakkinsu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku na biyayya da bada haƙƙoƙi da haƙuri akan masifu yana kanku.
- Umarni da ji ga shugabanni a kowane hali a cikin abinda zai yardar da Allah - Mai girma da ɗaukaka -, koda basu tsaya da haƙƙin talakawa ba.
- Gazawar shugababnni a sauke wajibinsu ba ya halatta mutane su gaza ta fuskar kin cika musu wajibinsu; kowa abin tambaya ne game da aikinsa, kuma za'a kama shi game da gazawarsa.
- Addini ba abin ginawa ba ne akan muƙayadah (yi min, in yi maka) ba , kaɗai akan lazimta ne da abinda ya wajaba koda ɗayan ya gaza a abinda ya wajaba akansa ta wurinsa, kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisin.
صحيح مسلم (3/ 1474) (1846). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 719). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 664). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص432). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 553).