عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: مَرَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِقَبْرَيْنِ، فَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ، وَمَا يُعَذَّبَانِ فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ لاَ يَسْتَتِرُ مِنَ البَوْلِ، وَأَمَّا الآخَرُ فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ» ثُمَّ أَخَذَ جَرِيدَةً رَطْبَةً، فَشَقَّهَا نِصْفَيْنِ، فَغَرَزَ فِي كُلِّ قَبْرٍ وَاحِدَةً، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، لِمَ فَعَلْتَ هَذَا؟ قَالَ: «لَعَلَّهُ يُخَفِّفُ عَنْهُمَا مَا لَمْ يَيْبَسَا».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.
Fa’idoji
- annamimanci da barin tsarkaka daga fitsari yana daga manyan zunubai kuma daga sabubban azabar kabari.
- Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ya yaye wasu sashin gaibu - kamar azabar kabari - dan bayyanar da alamar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Wannan aikin na tsaga itacan dabino da sanya shi akan kabari ya kebanci Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ; domin Allah Ya tsinkayar da shi akan halin masu kabarin su biyun, ba za’a kiyasta waninsa da shi ba domin babu wani da yasan halayen ma'abota kaburbura.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 53) (218).
صحيح مسلم (1/ 240) (292).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص43).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص22).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 29).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن هَانِئ مَوْلَى عُثْمَانَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: كَانَ عُثْمَانُ إِذَا وَقَفَ عَلَى قَبْرٍ بَكَى حَتَّى يَبُلَّ لِحْيَتَهُ، فَقِيلَ لَهُ: تُذْكَرُ الْجَنَّةُ وَالنَّارُ فَلَا تَبْكِي، وَتَبْكِي مِنْ هَذَا؟ فَقَالَ: إِنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «إِنَّ الْقَبْرَ أَوَّلُ مَنْزِلٍ مِنْ مَنَازِلِ الْآخِرَةِ، فَإِنْ نَجَا مِنْهُ فَمَا بَعْدَهُ أَيْسَرُ مِنْهُ، وَإِنْ لَمْ يَنْجُ مِنْهُ فَمَا بَعْدَهُ أَشَدُّ مِنْهُ».
Daga Hani baran Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Usman ya kasance idan ya tsaya akan ƙabari sai ya yi kuka har sai gemunsa ya yi dan shi, sai aka ce masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka, kuma kana yin kuka saboda wannan? sai ya ce: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan Lahira, idan mutum ya tsira a cikinsa to abinda ke bayansa ya fishi sauƙi, idan kuma bai tsira a cikinsa ba to abinda ke bayansa ya fi shi tsanani».
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Sarkin muminai Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya kasance idan ya tsaya akan wani ƙabari sai ya yi kuka har sai hawaye ya sa gemunsa ya yi dan shi, sai akace masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka dan shauƙi zuwa aljanna ko tsoron wuta! amma kana kuka saboda ƙabari? Sai ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan lahira, idan ya tsira ya kuɓuta daga cikinsa to abinda ke bayansa na masaukai su ne mafi sauƙi daga gare shi , idan bai tsira daga azabarsa ba; to abinda ke bayansa na uƙuba ya fi tsanani daga abinda ke cikinsa.
Fa’idoji
- Bayanin abinda Usman - Allah Ya yarda da shi - yake a kansa na tsoron Allah - Maɗaukakin sarki - tare da cewa shi yana daga cikin waɗanda aka yi wa albishir da aljanna.
- Halaccin kuka a lokacin tina tshin hankali na ƙabari da kuma alƙiyama.
- Tabbatar da ni'imar ƙabari da kuma azabarsa.
- Tsoratarwa daga azabar ƙabari.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 142) (2308).
سنن ابن ماجه (5/ 333) (4267).
مشكاة المصابيح، للتبريزي (1/ 48).
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، المباركفوري (6/ 490).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (1/ 215).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com