عن أبي هريرة رضي الله عنه أن أبا بكر الصديق رضي الله عنه قال: يا رسول الله مُرني بكلمات أقُولُهُنَّ إذا أصبَحتُ وإذا أمسَيتُ، قال: «قل: اللهم فاطِرَ السماوات والأرض عالم الغيبِ والشهادة، ربَّ كُلِّ شَيءٍ ومَلِيكَه، أَشْهد أن لا إله إلا أنت، أعوذ بك من شرِّ نفسي وشرِّ الشيطان وشِرْكِهِ وأن أقترف على نفسي سوءًا أو أجرُّه إلى مسلم» قال: «قلها إذا أصبحت، وإذا أمسيت، وإذا أخذْتَ مَضْجَعَك».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - cewa Abu Bakr Al-Siddiq, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Manzon Allah, don Allah ka fada min kalmomin da nake fada lokacin da na zama, kuma idan na kasance, sai ya ce: "Ka ce: Ya Allah, kai ne Mahaliccin sama da ƙasa, da abunda ke fake da na fili, Ubangijin komai da Mallakarsa, na shaida hakan Babu wani abin bauta sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin raina da sharrin Shaidan da shirkarsa, da cewa na aikata sharri ko jawo shi ga Musulmi.Ya ce: "kakatanta idan ka wayi gari ko kayi yammaci ko idan ka tafi kwanciya."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
سنن أبي داود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، المكتبة العصرية، صيدا – بيروت.
سلسلة الأحاديث الصحيحة، للألباني، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، ط، الأولى، لمكتبة المعارف.
رياض الصالحين، للنووي، تحقيق ماهر الفحل، ط، الأولى 1428هـ، دار ابن كثير، دمشق -بيروت.
نزهة المتقين، لمجموعة من المؤلفين، مؤسسة الرسالة، ط: الرابعة عشر، 1407هـ.
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي، دار ابن الجوزي، السعودية، ط: الثالثة 1418هـ.
جامع الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر، وآخرون، ط2، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي ، مصر، 1395هـ.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد وآخرون، إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، 1425هـ.
سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، للألباني، ط1، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، 1422هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بنِ عمر رضي الله عنهما أن عمرَ بْن الخطاب رضي الله عنه قال: ((يا رسول الله، أّيَرقُدُ أَحَدُنا وهو جُنُب؟ قال: نعم، إِذَا تَوَضَّأ أَحَدُكُم فَليَرقُد)).
Daga Abdullahi Dan Umar Allah ya yarda dasu Umar Dan Khaddab Allah ya yarda da shi yace: [Ya Manzon Allah, waninmu zai iya kwanciya da janaba? sai yace: E, zai iya, amma in yayi alwala
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya tambayi Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi: Idan janaba ta sami wani tun farkon dare ta hanyar saduwa da iyali ko mafarki, shi zai iya kwanciya bacci a haka? sai Mai tsira da amincin Allah ya basu damar yin haka amma idan anyi alwalla irin ta salla.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ.
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا تَوَضَّأَ أَحَدُكُمْ فَلْيَجْعَلْ فِي أَنْفِهِ ثُمَّ لِيَنْثُرْ، وَمَنِ اسْتَجْمَرَ فَلْيُوتِرْ، وَإِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ نَوْمِهِ فَلْيَغْسِلْ يَدَهُ قَبْلَ أَنْ يُدْخِلَهَا فِي وَضُوئِهِ، فَإِنَّ أَحَدَكُمْ لاَ يَدْرِي أَيْنَ بَاتَتْ يَدُهُ».
ولفظ مسلم: «إِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ نَوْمِهِ فَلَا يَغْمِسْ يَدَهُ فِي الْإِنَاءِ حَتَّى يَغْسِلَهَا ثَلَاثًا، فَإِنَّهُ لَا يَدْرِي أَيْنَ بَاتَتْ يَدُهُ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin huklunce-hukuncen tsarki, daga cikinsu: Na farko: Cewa wanda zai yi alwala to ya wajaba akansa ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da numfashi, sannan ya fitar da shi ta numfashi kuma. Na biyu: Cewa wanda ya yi nufin tsarkake kazanta mai fita daga gareshi da gusar da ita ba tare da ruwa ba kamar duwatsu da makancinsu to tsarkakewarsa ta zama akan adadin mara mafi karancinsa uku, mafi yawa wanda zai kawar da abinda ya fita zai kuma tsarkake wurin. Na uku: Cewa wanda ya farka daga baccin dare kada ya shigar da tafinsa a cikin kwarya dan ya yi alwala har sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, domin cewa shi bai san a'ina hannunsa ya kasance ba, ba zai iya amintar da najasa akan su ba, zai iya yiwuwa Shaidan ya yi wasa da su kuma ya dora abubuwa masu cutarwa garesu ga mutum ko mai bata ruwan.
Fa’idoji
- Shaka ruwa yana wajaba a cikin alwala, shi ne: Shigar da ruwa a cikin hanci ta hanyar numfashi, hakan nan facewa yana wajaba, shi ne: Fitar da ruwa daga hanci ta hanyar numfashi.
- Anso mara a tsarkin hoge.
- Halaccin wanke hannaye bayan baccin dare sau uku.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 43) (162).
صحيح مسلم (1/ 233) (278).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص19).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 11).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: احْتَرَقَ بَيْتٌ بالمَدِينَةِ عَلَى أهْلِهِ مِنَ اللَّيْلِ، فَلَمَّا حُدِّثَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم بِشَأنِهِم، قالَ: «إنَّ هذه النارَ عَدُوٌّ لَكُمْ، فَإِذَا نِمْتُم، فَأَطْفِئُوهَا عَنْكُمْ».
Daga Abu Musa al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - yana cewa: "Wani gida a cikin gari an kona shi daga mutanensa daga dare, don haka lokacin da Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi magana game da su, sai ya ce:" Wannan wutar makiyi ne a gare ku, don haka idan kun yi bacci, to ku kawar da ita daga gare ku.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An kona wani gida a Madina da daddare, kuma Annabi -SAW- ya ruwaito cewa ya gaya musu cewa wannan wuta makiyin mutanenta ne idan ba su kiyaye sharrin harshenta da konewarsa ba, to sai ya umurce su - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - su kashe ta kafin bacci don kiyaye sharrinta daga wuta da wuta da makamantansu
Madogara
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ - 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى 1418هـ.
صحيح البخاري، للإمام أبي عبدالله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبدالباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
المعجم الوسيط، مكتبة الشروق الدولية، الطبعة الرابعة، 1425هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ حُذَيْفَةَ بْنِ اليَمَانِ رَضيَ اللهُ عنه: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا أَرَادَ أَنْ يَنَامَ وَضَعَ يَدَهُ تَحْتَ رَأْسِهِ، ثُمَّ قَالَ: «اللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَجْمَعُ أَوْ تَبْعَثُ عِبَادَكَ».
Huzaifa Ibnul Yaman -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin yin bacci yana sanya hannunsa ƙarƙashin kansa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka kareni azabarKa ranar da zaKa tara ko zaka tashi bayinKa».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya kwanta dan yayi barci, sai ya shimfiɗa hannunsa na dama kuma ya sanya kundukukinsa (kumatunsa)na dama akansa, sai ya ce: «Ya Allah» Ubangijina «Ka kareni» Ka kiyayeni daga «azabarKa» da uƙubarKa «ranar da zaKa tara ko zaKa tashi bayinKa» a ranar hisabi, ranar alƙiyama.
Fa’idoji
- Falalar wannan addu'ar mai albarka, kuma an so kiyayewa a kanta dan yin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- An so kwanciya akan ɓarin jiki na dama.
- Sindi ya ce: Faɗinsa (Ya Allah Ka kareni azabarKa), a cikinsa cewa yana kamata ga mai hankali ya maida baccinsa tsani dan tina mutuwa da kuma tashi a bayanta.
- Kariya daga azabar Allah a ranar alƙiyama tana kasancewa ne da falalar Allah da kuma rahamarSa, ta hanyar dacewar bawa ga aiki na gari da kuma gafarar Allah ga bayinSa.
- Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa kuma Majiɓincin al'amuransa - Allah Maɗaukakin sarki -.
- Tabbatar da taruwa da kuma makoma, kuma cewa mutane masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu dan ya yi musu hisabi akan ayyukansu, wanda ya samu alheri to ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki -, wanda ya samu koma bayan haka to kada ya zargi kowa sai kansa, kawai su ne ayyukan bayi Allah Yana kiyaye musu su.
- Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan bayanin halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agagre shi - a baccinsa.
- Faɗinsa: "Sai ya sanya hannunsa na dama ƙarƙashin kundukukinsa" ya kasance daga al'adunsa - tsra da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne damantawa a cikin kowane abu, sai dai abinda dalili ya zo akan saɓaninsa.
- Bacci akan ɓarin jiki na dama ya fi saurin farkawa saboda rashin tabbatar zuciya a cikin wannan halin, kuma ya fi sauƙi ga zuciya; domin ita zuciya a ɓangaren hagu take, da a ce bawa ya yi bacci akan ɓarin hagu zai cutar da zuciya dan nauyin gaɓɓai a kanta.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 404) (3398).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 533).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 335).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1001).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عمر رضي الله عنهما مرفوعاً: «لا تَتْرُكُوا النار في بيوتكم حين تنامون».
Daga Ibn Umar -Allah ya yarda da su- zuwa ga Manzon Allah SAW: "Kada ku bar wuta kunne a gidajenku lokacin da kuke bacci"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ma'anar Hadisin cewa Manzon Allah SAW ya hana Al-ummarsa yin bacci kafin su kashe Wutar da suka kunna
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
رياض الصالحين، تأليف : محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ
شرح سنن أبي داود، تأليف: عبد المحسن بن حمد بن عبد المحسن العباد، نسخة الإلكترونية.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا أَوَى إِلَى فِرَاشِهِ كُلَّ لَيْلَةٍ جَمَعَ كَفَّيْهِ، ثُمَّ نَفَثَ فِيهِمَا فَقَرَأَ فِيهِمَا: {قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ}، وَ{قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ}، وَ{قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ}، ثُمَّ يَمْسَحُ بِهِمَا مَا اسْتَطَاعَ مِنْ جَسَدِهِ، يَبْدَأُ بِهِمَا عَلَى رَأْسِهِ وَوَجْهِهِ وَمَا أَقْبَلَ مِنْ جَسَدِهِ، يَفْعَلُ ذَلِكَ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ.
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya daga su - kamar yadda mai addu'a yake yi - sai ya yi tofi a cikinsu daga bakinsa sassaukan tofi tare da yawu sassauka sai ya karanta surori uku: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane}, sannan ya shafi abinda zai yi wu daga jikinsa; yana mai farawa da kansa da fuskarsa da bangare na gaba daga jikinsa, yana maimaita wannan aikin sau uku.
Fa’idoji
- An so karanta suratul Ikhlas da Mu'awwizataini kafin bacci da tofi da su, da shafar abinda zai yi wu daga jikinsa.
Madogara
صحيح البخاري (6/ 190) (5017)، (7/ 133) (5748)، الكاشف عن حقائق السُّنن (5/1651)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (20/ 35)، التوضيح لشرح الجامع الصحيح ( 24/ 91)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 929)، شرح سنن أبي داود لابن رسلان (19/268).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com