عَنْ المُغِيرَةِ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَأَهْوَيْتُ لِأَنْزِعَ خُفَّيْهِ، فَقَالَ: «دَعْهُمَا، فَإِنِّي أَدْخَلْتُهُمَا طَاهِرَتَيْنِ» فَمَسَحَ عَلَيْهِمَا.
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a daya daga tafiye-tafiyensa sai ya yi alwala, lokacin da ya isa wanke kafafuwa sai Mugira dan Shu'uba - Allah Ya yarda dashi - ya mika hannayensa dan ya cire abinda ke saman kafar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na kuffi dan wanke kafafuwansa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka barsu kada ka cire su, ni na shigar da kafafuwamna a cikin kuffin alhali ni ina da tsarki (Alwala). Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shafa akan kuffinsa, maimakon wanke kafafuwa kenan.
Fa’idoji
- Halaccin shafa akan kuffi yana kasancewa ne a lokacin alwala na karamin kari, amma wanka dan babban kari (janaba, al’ada) babu makawa daga wanke kafafuwa.
- shafa yana kasancewa ne sau daya da shudar da hannu mai danshi akan saman kuffin banda kasansa.
- An shardanta shafa akan kuffi ya zama ya sanyasu bayan ya yi cikakkiyar alwala ya wanke kafafuwansa da ruwa, kuma kuffin ya zama mai tsarki, mai suturta bigiren farillar na kafa, kuma shafarsu ya zama a karamin kari ne ba a janaba ba ko abinda yake wajabta wanka ba, kuma shafar ta zama a kayyadajjen lokaci a shari'ance shi ne yini da dare ga mazaunin gari, matafiyi kuma kwana uku da dararensu.
- Ana kiyasta dukkanin abinda yake suturta kafafuwa akan kuffi na jaurabi da wasunsu, to shafa akansu yana halatta.
- Kyakkyawan dabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da koyarwarsa, inda ya hana Mugira ciresu, ya kuma bayyana masa dalili: Cewa shi ya shigar da su suna tsarki; dan ransa ya natsu, ya kuma san hukuncin.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 52) (206).
صحيح مسلم (1/ 230) (274).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص50).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 36).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص27).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يُسَبِّحُ على ظَهرِ رَاحِلَتِه حَيثُ كان وَجهُهُ، يُومِئُ بِرَأسِهِ، وكَان ابنُ عُمرَ يَفعَلُهُ».
وفي رواية: «كان يُوتِرُ على بَعِيرِه».
ولمسلم: «غَيرَ أنَّه لا يُصَلِّي عَليهَا المَكتُوبَة».
وللبخاري: «إلا الفَرَائِض».
Daga Abudullahi Dan Umar "Cewa Lallai Annabi ya Kasance yana Tasbihi akan abin hawansa, kuma ko ina ya sanya fuskarsa, yana nuni da kansa, kuma haka ma Dan Umar yake yi" a wata Riwar kuma "Ya kasance yana yin wutiri a kan rakuminsa a kuma Hadisin Muslim: "Sai dai cewa shi baya sallar Farilla a kanta a kanta" a riwayar bukari kuma" "Sai Sallar Farillai"
Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi ya kasance yana Sallar Nafila kawai ne akan abin hawansa kuma duk inda ya dosa da shi, kuma koda bata fuskantar Alkibla, kuma yana nuni da kansa idan yazo yin ruku'u da Sujada kuma baya dorawa kansa sai ya Sauko kasa don yayi sujada ko Ruku'u ko Sujada ko kuma ya kalli Alkibla, kuma babu banbanci da ya kasance Nafila ce kawai ko kuma Nafila ta dole ko kuma salloli Ma'abota Sababi, kuma haka ya kasance yana yin Wuturi akan Rakuminsa
Madogara
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ.
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ، 2006م.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: الأولى 1426هـ.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ، 1988م.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا يَحِلُّ لِامْرَأَةٍ مُسْلِمَةٍ تُسَافِرُ مَسِيرَةَ لَيْلَةٍ إِلَّا وَمَعَهَا رَجُلٌ ذُو حُرْمَةٍ مِنْهَا».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana haramta akan mace musilma ta yi tafiyar dare (daya) sai idan akwai namji muharraminta tare da ita.
Fa’idoji
- Ibn Hajar ya ce: Rashin tafiya ga mace ba tare da muharrami ba, shi ijam'i ne a wanin Hajji da Umarh, da fita daga kasar shirka, daga cikinsu (malamai akwai) wanda ya sanya hakan daga sharuɗɗan Hajji.
- Cikar shari'ar musulunci, da kwaɗayinta akan kiyaye mace da kuma tsareta.
- Imani da Allah da ranar lahira suna lazimtar da ƙanƙar da kai ga shari'ar Allah, da kuma tsayuwa a iyakokinta.
- Muharramin mace shi ne mijinta ko wanda yake haramta a gareta (ta aure shi) har abada saboda 'yan uwantaka, ko shayarwa, ko sukurtaka, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce; domin cewa abin nufi daga muharrami (shi ne) tsare mace da kareta da tsayuwa da sha'aninta.
- AlBaihaƙi ya ce game da riwayoyin da suka zo a tsawon tafiyar da mace ba za ta yi tafiya ba sai tare da muharrami: Abin tabbatarwa cewa dukkan abinda ake ambatansa tafiya to an hana mace daga gare shi ba tare da miji ko muharrami ba, daidai ne ya kasance kwana uku ne ko kwana biyu ko kwana ɗaya ko tafiyar wasu awanni ko wanin haka; saboda riwayar Ibnu Abbas abar wawaitawa (Mutlaka ce), ita ce kuma ƙarshen riwayoyin Muslim wacce ta gabata: (Kada mace ta yi tafiya sai tare da muharraminta) wannan yana haɗa dukkan abinda ake ambatansa tafiya. Ya tiƙe. Wannan hadisin ya kasance gwargwadan mai tambaya ne da kuma ƙasarsa.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 43) (1088).
صحيح مسلم (2/ 977) (1339).
تيسير العلام، لعبد الله البسام (ص374).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام، لابن عثيمين (3/ 501).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص178).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «السفر قطعة من العذاب، يمنع أحدكم طعامه وشرابه ونومه، فإذا قضى أحدكم نَهْمَتَهُ من سفره، فليُعَجِّلْ إلى أهله».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - da isnadi:: Tafiya azaba ce, dayanku ya hana abincinsa, da shansa, da bacci.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
1- فتح الباري لابن حجر (623/3).
2- شرح صحيح مسلم(70/13).
3-كنوز رياض الصالحين(580/12).
4-شرح رياض الصالحين لابن عثيمين(621/4).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما مرفوعاً: نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم أن يُسَافَرَ بالقرآن إلى أرض العدو.
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : "Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- Annabi ya hana tafiya da Qur'ani zuwa garin Abokan Gaba
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ya hana daukar Al-Qur'ani da kuma tafiya da shi zuwa garin Kafirai wadan da basa Addinin Musulunci kada ya zamanto abun Wulakantawa a can, kuma idan mafi yawan rinjaye tunani rashin samun hakan to ya halatta.
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ.
- صحيح البخاري -للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين/محمد علي بن محمد بن علان البكري -اعتنى بها: خليل مأمون شيحا- دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت – لبنان- الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م.
- فتاوى اللجنة الدائمة: اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء- جمع وترتيب: أحمد بن عبد الرزاق الدويش.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن سَرْجِس رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا سافر يَتَعَوَّذ مِن وَعْثاء السَّفَر، وكآبة الـمُنْقَلَب، والحَوْر بعد الكَوْن، ودعوة المظلوم، وسُوء الـمَنْظَر في الأهل والمال.
An rawaito daga Abdullahi Bn Sarjis -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
كنوز رياض الصالحين, بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426هـ.
معالم السنن، للخطابي، نشر: المطبعة العلمية - حلب، الطبعة: الأولى 1351 هـ - 1932م.
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري، نشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء - الجامعة السلفية - بنارس الهند، الطبعة: الثالثة ، 1404 هـ - 1984م.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما مرفوعًا: «الراكب شيطان، والراكبان شيطانان، والثلاثة رَكْب».
An rawaito daga Abdullahi Bn Amr bn Al-ass -Allah ya yarda da su daga Annabi: ""Mahayi shi Kadai Shaidan ne, Mahaya Biyu kuma Shadanu biyu ne, Guda uku kuma Karafka"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Malik Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Madogara
- سنن الترمذي - محمد بن عيسى ، الترمذي، تحقيق وتعليق:أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض -شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م.
- مسند الإمام أحمد بن حنبل المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي مؤسسة الرسالة الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م.
- سنن أبي داود - سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد: المكتبة العصرية. صيدا – بيروت.
- صحيح أبي داود – الأم -محمد ناصر الدين، الألباني - مؤسسة غراس للنشر والتوزيع، الكويت الطبعة: الأولى، 1423 هـ - 2002 م.
- موطأ الإمام مالك- المؤلف: مالك بن أنس بن مالك الأصبحي-صححه ورقمه وخرج أحاديثه وعلق عليه: محمد فؤاد عبد الباقي-دار إحياء التراث العربي، بيروت – لبنان-1406 هـ - 1985 م.
- نيل الأوطار- محمد بن علي الشوكاني -تحقيق: عصام الدين الصبابطي- دار الحديث، مصر- الطبعة: الأولى 1413هـ - 1993م
عون المعبود شرح سنن أبي داود، ومعه حاشية ابن القيم: تهذيب سنن أبي داود وإيضاح علله ومشكلاته / محمد أشرف بن أمير بن علي بن حيدر، ، العظيم آبادي: دار الكتب العلمية -بيروت
الطبعة: الثانية، 1415 هـ.
- الاستذكار: أبو عمر بن عبد البر بن عاصم النمري القرطبي -تحقيق: سالم محمد عطا، محمد علي معوض-دار الكتب العلمية – بيروت-الطبعة: الأولى، 1421 - 2000م.
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين/محمد علي بن محمد بن علان بن إبراهيم البكري الصديقي الشافعي -اعتنى بها: خليل مأمون شيحا- دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت – لبنان- الطبعة: الرابعة، 1425 هـ - 2004 م.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «إذا سافرتم في الخِصْب، فأَعْطُوا الإبل حظَّها من الأرض، وإذا سافرتم في الجَدْب، فأَسْرِعوا عليها السَّيْر، وبادروا بها نِقْيَها، وإذا عَرَّسْتُم، فاجتنبوا الطريق؛ فإنها طُرُق الدَّوَابِّ، ومَأْوَى الهَوَامِّ بالليل»
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Idan kukai tafiya a cikin Yalwa, to ku bawa Rakuma hakkinsu na Kasa, kuma idan kukai Tafiya cikin Fari kuyi Saurin Tafiya, kuyi gaggawar wanketa"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى 1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- مرقاة المفاتيح، علي بن سلطان محمد، أبو الحسن نور الدين الملا الهروي القاري، دار الفكر.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى 1430ه.
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com